African LanguagesHausa

Yadda batun COVID-19 ya mutu murus a Najeriya

Kwayar cutar corona mai haddasa cutar COVID-19, cutar da ke yaduwa ta numfashi wadda ake kyautata zaton ta yi mafari ne daga Wuhan, China a shekarar 2019 ya dakatar da tattalin arzikin duniya baki daya inda aka rika daukan matakan kariya iri-iri hatta da matakin da kasashe suka dauka na takaita tafiye-tafiye.

A Najeriya matakai kamar hana fita zuwa ayyukan da ba dole ba ne, da rufe makarantu da kuma haramta tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na daga cikin ire-iren matakan da aka dauka na rage yaduwar kwayar cutar.

Shekaru biyu bayan nan, a watan Disemban 2022, shugaba Muhammadu Buhari ya umurci da a rage matakan kariyar da aka dauka bisa tanadi da shawarwarin kwamitin da gwamnatinsa ta girka na sanya ido kan lamuran da suka shafi VOVID-19 wato PSC.

Bisa bayanan da aka samu daga gwaje-gwajen da aka yi, akwai hujjojin da ke nuna cewa an sami raguwa a yanayin yaduwa da ma kamuwa da COVID-19 a kasar. Wannan ne ya sa mutane da yawa suka yi tunanin cewo cutar ta mutu murus.

To amma COVID-19 ta tafi da gaske? A wani hali cutar ta ke a yanzu haka da kusan kowa a Najeriya ke tunanin ba za’a sake jin labarinta ba.

Daga ranar Talata 26 ga watan Afrilu, akwai mutane 764,474,387 wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar COVID-19 inda alkaluman ke nuna cewa wasu mutane 6,915,286 kuma sun riga mu gidan gaskiya. A Najeriya, mutane 266,675 aka tabbatar suna dauke da cutar, yayin da wasu 3,567 ke dauke da cutar yanzu, wasu, 3,115 sun mutu, sa’annan mutane 259,953 sun sami sauki sun koma gida.

A watan Janairun 2023, Cibiyar Kula da Cututtuka ta kasa (NCDC) ta ce ta sami mutane 29 da ke dauke da cutar  COVID-19 a cikin mako guda (wato daga 7 zuwa 13, ga watan Janairun 2023) da wasu biyar kuma tsakanin 25 ga watan Maris zuwa 31, 2023. 

Har yanzu NCDC tana amfani da matakin hadin gwiwa na bai daya, wanda ke mataki na biyu wanda kuma ke cigaba da jagorantar shirin kawo dauki na gaggawa ga wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya sai dai yana cigaba da kasancewa sanadin damuwa ga yawancin cibiyoyin lafiya.

Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO), a rahotonta na 27 ga watan Afrilu ta ce kusan mutane miliyan 2.8 suka kamu da cutar yayin da wasu mutane 16,000 su kuma suka hallaka cikin kwanaki 28 (27 ga watan Maris zuwa 23 ga watan Afrilu 2023). Wadannan sabbin alkaluman sun nuna cewa an samu raguwa na mutanen da ke kamuwa da cutar da mutuwa daga ita da kashi 23 da 36 cikin 100 bi da bi, idan har aka kwatanta da alakaluman da aka samu a kwanakin 28 na farko (27 ga watan Fabrairu zuwa 26 ga watan Maris 2023). 

Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa sabanin raguwar da ake tunani ya na faruwa, an sami akwai yankunan da karuwar cutar ne ke tashe, har ma an sam rahotannin mace-mace a yankin kudu maso gabashin Asiya da yankunan da ke kudancin tekun Bahar Rum da ma dai wadansu kasashen duniya.

Baya ga wannan Hukumar Lafiyar a wata sanarwar da ta fitar ranar 5 ga watan Mayun 2023 ta ce yanzu an tabbatar cewa COVID-19 ta zama daya daga cikin cututtukan da za’a cigaba da fama da su, dan haka yanzu ita ba cutar da ke bukatar agajin gaggawa a matakin kasa da kasa ba ce kuma. Sai dai ta ce ya kamata a bi wadannan shawarwarin da masu ruwa da tsaki suka bayar.

  • A tabbatar da dorewar tsare-tsaren da aka sa a kasa sakamakon cutar sa’annan a cigaba da zama da shirin afkuwar matsaloli irin wannan nan gaba. 
  • A sa allurar rigakafin COVID-19 cikin jerin alluran da ya kamata a rika karba a kai – a kai a cikin yanayin zamantakewar rayuwa.
  • A kawo duk bayyanan da aka samu daga binciken kwayoyin cututtukan da ke da alaka da hanyar numfashi a tara su wahe daya saboda a sami irin cikakken bayanin da ake bukata.
  • A zauna cikin shiri dan aiwatar da matakan da zasu yaki cututtuka wadanda mahukunta za su bayar da umurnin aikata su bida tanadin dokokin kasa domin a tabbatar da samun su yadda ake bukata.
  • A cigaba da ayyuka a al’ummomi a kuma cigaba da yin kira ga shugabanni da su cimma matakin sadarwa mai kwari kuma mai jurewa wanda zai hada da sadarwa dangane da hadari, da kuma hada hannu da al’ummomi.
  • A cigaba da dage matakan dokokin COVID -19 din da ke takaita tafiya bisa la’akari da irin hadarin da ake gani.
  • A cigaba da tallafawa bincike

Bayan wannan sanarwar ta WHO, NCDC ta fitar da wata sanarwar da ke cewa har yanzu akwai hadarin samun wadansu sabbin nau’o’in cutar yayin da ake cigaba da samun yaduwarta a wadansu al’ummomin. Dan haka cibiyar ta ce allurar COVID-19 wajibi ne kuma tana bayar da shawarar amfani da takunkumin rufe fuska da dai sauran matakan kariyar da masana kiwon lafiya ke bayar da shawarar amfani da su.

“Bayanin cewa yanzu COVID-19 ba ta da hatsari sosai ba dan wani abu ba ne illa dan kasashe su iya juyawa daga matakin agajin gaggawa zuwa matsalar kiwon lafiyar da ke bukatar kulawa a cikin gida. Barazanar kwayar cutar na cigaba da kasancewa a kasashe da ma duniya baki daya musamman ga mutanen da ba su da garkuwar jiki mai karfi. Yayin da ake cigaba da samun yaduwa tsakanin al’ummomi, hadarin samun sabbin nau’o’in cutar na cigaba da karuwa ke nan wanda kuma shi ne ke kara yawan mutanen da ke amuda da cutar da ma mutuwa.”

Bacin wannan labarin wanda da yawa ka iya amfani da shi a matsayin hujjar jaddada cewa COVID-19 ta tafi, dole mu yi taka tsan-tsan domin kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasa ta bayyana, COVID-19 da Malaria na da alamu kusan iri daya amma kuma ba abu daya ne ke janyo su ba. Banbancin da ke tsakanin cututtukan biyu shi ne yayin da ake iya raba COVID-19 da mutun zuwa mutun, ba za’a iya yada malaria ba saboda haka, wanke hannu, tsabtace kai  da karbar allurar rigakafi duk suna da mahimmanci.

Akwai allurai na rigakafin COVID-19 da yawa wadanda WHO ta amince da amfani da su, kuma a Najeriya ma har yanzu ana wa jama’a allurar. 

Bisa bayanan NPHDCA hukumar da ke kula da kiwon lafiya na farko, daga 30 ga watan Afrilun 2023, a jihohi 36 har da babban birnin tarayya, mutane miliyan 73 daga cikin mutanen da suka cancanci karbar allurar rigakafin sun yi allurar yayin da wadansu miliyan 11 su kuma suka fara allurar amma ba su gama ba. 

A karshe

Duk da cewa hukuma lafiya ta duniya WHO ta ce COVID-19 ba ta da hatsari sosai ga al’umma daukan matakan kariya na da mahimmanci sosai . Yana da mahimmanci a dauki wadannan matakan domin a yi amfani da ka’idojin da cibiyoyin kiwon lafiya suka bayar, tare da wadanda WHO ita ma ta bayar.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button