African LanguagesHausa

Yadda masu amfani da WhatsApp su yi zamba ke damfarar ‘yan Najeriya

Getting your Trinity Audio player ready...

Frank, wanda aka sakaya sunarsa, tun daga watan satumba zuwa Oktoba (2023) ya ke aiki tukuru. An ba shi aiki, kuma yunkurinsa na tabbatar da cewa ya yi komai yadda ya kamata a kai shi ga gajiya. Amma sai aka yi sa’a wani abokin shi wanda ya yi imani da yoga – wanda wani salon atisaye ne da ya fito daga India – ya shawarce shi da ya rika yin yogar.

“Zai amfane ka sosai,” abokin ya ba shi shawara. 

Ba tare da son sa ba, haka nan Frank ya fara bincike kan yanar gizo-gizo ko zai sami aji. A wannan lokacin ne, ya sami waya daga wata lambar da bai sani ba tana masa tayin azuzuwar yoga. Frank ya yi mamakin kwarewar fasaha.

“Wadannan abubuwan yanzu tamkar suna karanta zukatar mutane ne,” ya rika fadawa kansa!

Matakan sun kasance kai tsaye: Ka katsa wannan adireshin sai ka bayar da lambobi shiddan da za’a tura maka bayan nan – natsatsiyar muryar da ke cikin wayar ta umurce shi. Sai dai sa’o’i kadan bayan nan, Frank ya sami wata wayar inda ake fada masa cewa ana amfani da lambar WhatsApp din sa wajen gudanar da wasu laifukan kudi. Nan da nan cikin firgici ya garzaya zuwa lambar tasa ya ga abun da ke faruwa, sai dai bai iya shiga ba domin an rufe.

“An yi mun waya ana gayyata in shiga wani ajin da na yi tunanin na yoga ne. Daga nan sai aka tura mun adireshi aka ce in latsa. Da na latsa, sai na sami umurnin cewa in tura wasu lambobi na musamman guda shida wadanda aka tura mun, wadanda ake kira OTP code. Abun da ni ban sani ba shi ne, OTP code din lambobi ne da ke tantance sahihancin lambar waya ta ta WhatsApp Frank ya bayyana.

Makircin na kama da gaskiya da kyar ake ganewa 

Olu (shi ma an sakaya sunarsa ta gaskiya bisa dalilai na tsaro) mutun ne mai matukar kaunar darar chess kuma mamban wata kungiyar masu wasar golf. Bayan da aka kira shi a waya ana zargin daga kungiyar ‘yan wasan golf din ne ake gayyatarssa zuwa wani taron kungiyar ta mambobin kasa da kasa, ko daya bai yi tunani ba kafin ya dauki lambobin guda shida ya tura. Muryar wadda ta kira kamar ta magidanciya ce (watakila mai shekaru 50 ko fiye haka), abun da ya kara ba ni karfin gwiwar cewa gaskiya ce. Ba’a yi mintoci masu yawa ba aka fara amfani da lambar WhatsApp din na sa ana tambayar wadanda ya ke da lambobinsu a wayar kudi.

Hanya ce mai sauki amma kuma dabarar da ke aiki sosai. Mr Olu ya yi bayanin cewa, “Ina cikin ofishi na da misalin karfe hudu da rabi sadda aka kira ni a waya ta whatsapp, kuma wadda ta yi magana bayarabiya ce wadda na kyautata zaton duk yadda aka yi ta dara shekaru 50 na haihuwa. Ta yi zargin wai tana kira na daga kungiyar ACC ne. Na tambaye ta me hakan ke nufi, sai ta ce mun kungiyar Abeokuta. Sai na yarda kawai domin kungiyar darar Chess ta Abeokuta na da lambar Whatsapp di na. Daga nan sai ta ce mun suna da taro ne na mambobin kasa da kasa da yamma da misalin karfe bakwai da rabi kuma tana so ta san ko zan halarci taron. Ta kuma kara da zargin cewa sun tura mun wasu lambobi na musamman zuwa waya ta, wadanda ya kamata in karanto mata dan ta tantance cewa zan halarci taron.”

Lambobin asusun banki da sunaye na zahiri

Ba wadannan ne kadai misalan da muke da su ba. Mutane da dama sun sami sakonnin da ba su yarda da su ba wadanda yawanci ake zargin sun fito daga ‘yan uwa da abokan arziki ne suna tambayar bashin kudi da alkawarin cewa za su biya, sai daga baya mutun ya fahimci cewa ‘yan damfara ne.

A lamuran Olu da Frank, sunan da ke kan asusun bankin da aka bayar aka ce a sanya kudin na wani mai suna “Bruno Sewa” ne a bankin Guaranty Trust Bank mai lamba 0868143335.

Mr Frank ya ce da wannan sunan ne ma aka taba tura masa sako a shafin Facebook amma aiki bai bar shi ya amsa sakon ba.

Wadansu masu amfani da shafin WhatsApp su ma sun bayyana cewa sun sami irin wadannan sakonnin daga wani asusun wanda shi ma ake neman kudin da shi. Sunan da ke kan wannan asusun shi ne: Rebecca Olotu,  lambobin kuma su ne 9029468406 a Palmpay.

WhatsApp na alfaharin cewa tana da matakan tsaron da ta dauka, har da wanda ke kare sakonnin mutun daga wayarsa zuwa duk wayar da ya yi niyya, ta yadda duk sakonninka za su kasance cikin sirri. Sai dai duk da wadannan matakan tsaron, akwai yadda masu zambar ke iya kai wa jama’a hari a kan manhajar su yi kutse a sakonnin jama’a su kuma yi ma’amala da mutanen da ke da lambobinsu a kan wayar.

Da fasaha ake shawo kan fasaha 

Rahul Sasi, shugaban kamfanin CloudSEk, daya daga cikin manyan kamfanonin tsaron yanar gizo-gizo ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da kan biyo bayan irin wannan damfarar da ake yi a cikin wadannan labaran wadanda ya wallafa a shafinsa na LinkedIn. 

Mr Sasi ya ce masu satar bayanai sukan tura lambobin da kan yi kama da suna bukatar a kira su ne. Yawanci sukan tura lambobin ne sadda mai wayar ke amfani da ita wajen amsa kira. Daga nan sai su tura duk wayoyin da ke neman shiga wayar zuwa ta su wayar. Sadda mutumin ke amfani da ita sai su fara rajistar wayar saboda su sa a tura mu su lambobin na OTP. Da zarar aka tura mu su sai su nemi hanyar tantancewa tunda za’a tura lambar zuwa wayar mai ita. Da zarar suka yaudari mutun suka sami lambobin, sai su cigaba da harkarsu da wayar suna neman kudi wurin jama’a.

Ana iya amfani da wannan dabarar wajen shiga shafin Whatsapp din jama’a idan har ma sun iya sun dauki wayar mutun da kansu.

“Kowace kasa da kamfanonin waya na da lambobi kusan iri daya dan haka ana iya amfani da wannan salon makircin a kowace kasa,” ya bayyana

Mafita!

Hanyar da ta fi tabbatar da kare jama’a daga irin wannan zambar ita ce ka da ma mutun ya fara ya amsa wayarsu, ko kuma ma ya mayar da wayar lambobin da bai sani ba. Haka nan kuma, ku yi taka tsan-tsan wajen amfani da lambobin zamba, kuma ma abun da ya fi mahimmanci shi ne kada kur ika barin wayarku haka nan a wuaren da wani zai iya dauka ya yi amfani da shi ba tare da saninku ba.

Yayin da wasu ke zargin bankuna ne ke barin mutane su yi amfani da lambobin banki na bogi su damfari jama’a, akwai ma bukatar sake inganta tsaro a soshiyal mediya.

Ga Mr Olu idan da ya na da lambar da ya yi amfani da ita a kan whatsapp har yanzu, da hakan bai faru da shi ba. “Da zan iya sake shiga shafin in rufe su, sa’annan in fita in sake shiga in sami lambar ta OTP a akna waya ta, amma sai aka sami akasi da yake na daina amfani da lambar baki daya,” ya bayyana.

Har yanzu ya na tunanin yadda masu damfarar suka gano ire-iren abubuwan da ya ke sha’awa har suka yi amfani da su wajen yaudararsa. “Har yanzu ina sosa kai na dangane da yadda suka san cewa za su iya samu na idan har suka yi amfani da wasan golf … ko kuma ma a ina suka sami irin wannan bayanin…?”

Har yanzu shafin Bruno Sewa  Facebook na aiki, ko bayan da Frank ya fito fili ya fallasa su. Yawancin wadanda ke amfani da whatsapp sun yi korafi kan yadda lambobin da ba su sani ba suke kiransu. Daya daga cikin lambobin iri daya ne da wanda shafin Bruno Sewa ya turawa Frank sako da shi:  “+62 838-7488-37661.”

Kafin a sami mafita ta dindindin ga wannan matsalar, wasu kwararru sun ce masu amfani da shafukan soshiyal mediya su rika amfani da disclaimer – wato takaitaccen bayanin da ke dauke da gargadi wanda zai yi rigakafin da zai kare zambar daga faruwa – misali mutane su ce ba za su taba neman kudi wajen jama’a ta hanyar sakonni ko kuma ma waya ba. Abun da Olu da Frank suke nadamar rashin yi tun farko.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button