African LanguagesHausa

Yarjejeniyar Samoa : Shin Najeriya ta karbi al’adar ‘yan luwadi da madigo na LGBTQ ke nan da ta sanya hannu? 

Getting your Trinity Audio player ready...

Yarjejeniyar Samoa na nufin wata yarjejeniyar kasa da kasa ce da Kungiyar Tarayyar Turai EU, da Kungiyar kasashen Afirka, na Yankin Karibiyan da Kasashen Yankin Facific na OACPS suka rattabawa hannu . Wannan hadakar na zaman wani tsari na yadda kasashen Turai 15 da na Afirka, Karibiyan da Facific 79 za su rika hadaka a wajen iyakokinsu.

Wannan yarjejeniyar ta yi mafari ne tun daga 1959 da yarjejeniyar Yawunde, wadda aka kwaskware ta ta koma yarjejeniyar Kwatano bayan nan. To sai dai shekaru 20 bayan haka, tanade-tanaden na bayan sun gaza cimma bukatun kasashe mambobi, dan haka ne aka kirkiro yarjejeniyar Samoa aka fara amfani da shi a watan Nuwamban 2023.

Mahimman manufofin yarjejeniyar 

Ainihin burin wannan yarjejeniyar ta kasa da kasa mai manufofi daban-daban shi ne a iya cimma wadannan abubuwan a kasashen da ke zaman mambobi:

  1. Tabbatar da kariyar hakkoki, wanzar da dimokiradiyya da gwamnati mai rikon amana.
  2. Tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da tsaro
  3. Inganta rayuwar al’umma da bunkasa yanayin zamantakewa
  4. Samar da muhalli mai dorewa da sauye-sauyen da za su taimaka da sautin yanayi.  
  5. La’akari da kowane bangare na al’umma ba tare da nuna banbanci ba da samar da tattalin arziki mai dorewa.  
  6. Saukake shige da fice da walwalar tafiya tsakanin yankunan

Alfanun da Najeriya za ta samu daga yarjejeniyar ta Samoa

Tanade-tanaden yarjejeniyar na neman shawo kan irin matsalolin da Najeriya ke fuskanta ne a matsayinta na kasa, kuma wannan ne ainihin dalilin da ya sa Najeriya ta sa hannu.

Yarjejeniyar ta yi alkawarin bayar da bashi, tallafi na mutane da na fasaha da kuma abubuwan da za su taimaka wajen habbaka kasa. Ta na kuma da burin inganta wasu daga cikin fannonin kasashen wadanda suka hada da ilimi, lafiya, da ababen more rayuwa.

Haka nan kuma, wannan yarjejeniyar za ta samar da dammamaki wa Najeriya ta shiga a dama da ita a kasuwannin kasa da kasa, ta rika samun riba daga yankunan da ke waje.

A dalilin wannan hadakar, Najeriya za ta sami wakilci a fagen tattalin arziki da sauran batutuwan da ke cigaba da kasancewa kalubale a matakin kasa da kasa wadanda suka hada da sauyin yanayi da tsaro. Sakamakon harkokin da ta ke yi da Turai, da wasu mambobin na OCAPS, za ta sami tallafi, da martanonin da za su taimaka wajen shawo kan matsalolin da aka bayyana daga farko.  Bacin haka, tun da ba Najeriya ce kadai ta ke fama da wadannan matsalolin ba, za ta kasance abin koyi wa sauran kasashen da ke cikin yankinta sakamakon kasancewarta a cikin wannan hadakar.

Daga karshe, tunda tanadin yarjejeniyar ya yi la’akari da bukatun Najeriya ne, ba zai yi wahala wa Najeriya ba idan ta so aiwatar da alhakin da ya rataya a wuyarta , saboda dangantakar da shi a matakin kasa da kasa a dalilin wannan yarjejeniyar.

Yarjejeniyar Samoa, tanadinta da dokokin cikin gida da rashin amincewar da wasu ke nunawa 

Yayin da yarjejeniyar Samoa ke alkawarin samar da kyakyawar makoma wa ‘yan Najeriya, wasu daga cikin manufofin za su gurbata al’adu da ka’idojin kasar. Daya daga cikin wadannan abubuwan wanda ya zama kan gaba a mahawarorin da suka biyo bayan sa hannu kan yarjejeniyar shi ne sakin layin da aka sa kan masu luwadi da madigo da sauran nau’o’in su, wadanda a dunkule ake kira LGBTQ.

A baya DUBAWA ta bayyana cewa dalilin da ya sa Najeriya ta rika jan kafa wajen shiga wannan yarjejeniyar shi ne batun auren jinsi daya, da masu kyamar auren jinsi da wadanda ke sauya jinsin su, wadanda abubuwa ne da duka suka sabawa al’adu da yanayin zamantakewar ‘yan Najeriya.

Sashe na 2.5 na yarjejeniyar ya ce kasashe mambobi za su inganta manufofin da ke la’akari da jinsi su kuma tabbatar da daidaito tsakanin jinsi a duka manufofin da za’a yi amfani da su.  A waje guda kuma, sashe na 29 ya bukaci mambobi da su goyi bayan samar da lafiya a fannin da ya shafi jima’i da haihuwa. Wannan ya hada da tazarar haihuwa, bayanai da ilimi da kuma amfani da matakai daban-daban na samar da lafiya a kasa baki daya.  

A watan Janairun 2014, Mr Goodluck Jonathan, shugaban kasar Najeriya ya aiwatar da dokar da ta haramta dangantaka tsakanin jinsi daya, wanda ya sabawa manufofin kasashen yamma ya kuma nuna kaskanci ga al’ummar ta LGBTQ. Dokar – wadda ta hana auren jinsi, ko dangantaka tsakanin wadanda ke jinsi daya da kasancewa mamba a kungiyoyin kare hakkin masu auren jinsi — na dauke da hukuncin dari na tsawon shekaru 14.

Wannan tanadin ya janyo rashin gamsuwa da Allah wadai daga ‘yan Najeriya inda da yawa suka fara kira ga gwamnati da ta janye daga wannan yarjejeniyar kamar yadda aka gani a wannan shafinda wannan  and da wannan

Abin da kwararru ke cewa

DUBAWA cta tuntubi Busola Ajibola, mataimakiyar darekta a shirin aikin jarida na Cibiyar Aikin Jarida, Sabbin Dabaru da Cigaba dan jin ra’ayinta dangane da wannan sahsen da ke bayani kan masu auren jinsi na LGBTQ.  A cewarta yarjejeniyar ba ta ce komai a kan LGBTQ ba amma “ ta jaddada mahimmancin mutunta dokokin kasa da kasa kan cin zarafin jama’a saboda jinsinsu ko wanda su ke so idan har kasashen da ke zaman mambobi suna so su ci gajiyar tanadi da aka yi a ciki.”

Haka nan kuma, Ms Ajibola ta cigaba da cewa duk da cewa bai tilastawa mambobi halatta auren tsakanin jinsi daya, “ya bayar da damar kara yawan hakkokin kungiyoyin tsiraru wadanda ke da nau’o’in LGBTQ”

“Kamar dai yadda mu ke gwagwarmayar kare hakkokin mata, za mu sami al’ummomin LGBTQ wadanda za su rika bayyana bukatunsu su ma na a mutunta hakkokinsu. Abun da ya sauya kuma shi ne tilas ne gwamnati ta saurari wadannan bukatun idan har su na so su cigaba da samun alfanun da yarjejeniyar zai bayar. Sai dai kuma ba dole ba ne su mutunta,” ta bayyana.

A wata hirar da ta yi da DUBAWA, Badejoko Selimot, wata lauya a jihar Legas ta ce sa hannun da Najeriya ta yi kan yarjejeniyar Samoa ya dora ma ta alhakin aiwatar da tanade-tanade da manufofinta, dan haka yanzu ta na da alhakin kare hakkokin al’ummar LGBTQ.

“To sai dai ya na da mahimmanci a yi la’akari da sashi na 1(3) na 1999 CFRN (wannan ne tushen ko wane doka a kundin tsarin mulkin Najeriya) wanda ya tanadi cewa duk dokar da ta sabawa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya ba ta da hurumi a kasar.

“Dan haka, Najeriya na iya kare kanta da wannan tanadin ta ce yarjejeniyar ta sabawa kundin tsarin mulkinta.

“Abin da na ke cewa shi ne, idan har muka kwatanta kundin tsarin mulkin Najeriya da tanadin yarjejeniyar Samoa za mu ga cewa suna karo da juna. Kuma a duk lokacin da akwai sabanin tsakanin kundin tsarin mulkin Najeriya da ko ma wace irin doka ce, Kundin tsarin mulkin Najeriya za ta fi karfin shi,” ta bayyana.

Olumide Alabi, wani lauya shi ma, ya amince da madam Selimot, ya na matsayar dokokin Najeriya kan dokokin da suka sabawa na kasar a bayyane ta ke. “Idan har tanadin yarjejeniya ta yi karo da dokokin Najeriya, to dokar Najeriya ce za ta fi tasiri, kuma majalisar dokoki ba za ta amince da duk wata dokar da ke karo da dokokinmu na cikin gida ba,” ya bayyanawa DUBAWA.

Da ya ke mayar da na sa martanin, Inibehe Effiong, wani masanin shari’a shi ma, ya yi bayyanin cewa tamkar “rainin hankali” ne a ce wai yarjejeniyar Samoa ba ta da alaka da LGBTQ.

“Tambayar da ya kamata a yi shi ne, shin sanya hannu kan wannan yarjejeniyar zai yi tasiri kan dokokin kasar da suka haramta auren jinsi?” ya tambaya.

Martanin gwamnati

Da ya ke mayar da martani kan wannan cece-kucen da aka shiga yi, Ministan Yada Labarai Mohammed Idris cewa ya yi yarjejeniyar Samoa Agreement, wadda Najeriya ta sanya wa hannu a watan Yuni, “ba wani abu ba ne illa tsari dokar da ta tabbatar da hadin kai tsakanin OACPS da Kungiyar Tarayyar Turai, dan ingantawa da kuma tabbatar da dorewar cigaba, yaki da sauyin yanayi da kuma samar da hadaka mai amfani tsakanin kasashen OACPS a fagen kasa da kasa.” 

Mr Idris ta ce Najeriya da ma ta na da “dokar da ta haramta auren jinsi kuma sabanin rahotannin da ake samu, babu yadda za’a yi tanadin yarjejeniyar ta fi karfin dokokin Najeriya.”

Bolaji Adebiyi, mataimakin yada labarai na Ministan Kasafin Kudi, shi ma ya jaddada cewa wannan yarjejeniyar da aka sanyawa hannu an yi shi ne saboda cigaban tattalin arzikin kasa, ba hakkokin LGBTQ ba.

“Takardun da gwamnatin tarayya ta sanyawa hannu, musamman saboda bunkasar tattalin arzikin Najeriya ne, babu inda aka ce takardun na LGBT ne ko auren jinsi, ko kadan ma ba’a yi wannan bayanin ba, kuma ba zai yi kyau a ce wai Najeriya ta amince da haka ba. Abin da Bagudu ya sanya wa hannu na da nasaba da dalar Amurka biliyan 150 na kasuwanci ne,” ya ce.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »