African LanguagesHausa

Yaudara! Ba Amurka ce ta kai hare-hare ta sama a Kaduna ba

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: wani mai amfani da shafin Facebook da wasu a X na  da’awar cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare ta sama a Kaduna  

Yaudara! Ba Amurka ce ta kai hare-hare ta sama a Kaduna ba

Verdict: Misleading! While an airstrike was recently launched against terrorists in Kaduna, this operation was initiated by the Nigerian Air Force, not the US.

Cikakken bayani

Na tsawon kwanaki da dama yanzu, ake mahawara tsakanin ‘yan Najeriya wadanda ke fargabar cewa Amurka na iya kaddamar da hare-hare a duk sadda ta ga dama. Yayin da ake fama da hakan ne kuma, wasu sabbin  da’awowi suka bulla a kafofin sada zumunta irin su Facebook cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare ta sama a Kaduna.

Wannan labarin wanda ya yi asali daga wani mai amfani da shafin Facebook din da aka tantance  Dili Classic, nan da nan ya shiga ko’ina inda ya sami alamar like sama da 1,700 aka kuma raba sau 28 cikin sa’o’i 17 kacal. Yayin da da yawa suka amince hakan ya faru a zahiri, akwai kadan daga cikin masu tsokacin da suka bayyana shakkunsu.

Yaudara! Ba Amurka ce ta kai hare-hare ta sama a Kaduna ba

Hoton bayanin da ya bi ko’ina a Facebook yanzu.

.Ban da Facebook, wasu masu amfani da shafin X ma su na yada wannan  labarin, da ke cewa Amurka ta fara kai hari a Najeriya. Ganin yadda wannan bayanin ke da sarkakiya DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar batun.

Tantancewa

Rahotannin da aka wallafa a jaridun Premium Times da The Guardian ranar 10 ga watan Nuwamban 2025 sun tabbatar da afkuwar hare-haren da aka kai kwanan nan  a sansanonin wasu ‘yan ta’adda a jihar Kaduna. Sabanin abin da da’awar ke cewa, ba Amurka ce ta kaddamar da hare-haren ba. A maimakon haka, rundunar sojojin yakin saman Najeriya ne (NAF) suka kaddamar da hare-haren a yankuna da dama wadanda suka hada har da wasu yankunan da ke cikin jihohin Kaduna, Borno, Kwara, Katsina da Zamfara.

Bisa bayanan Ehimen Ejodame, daraktan hulda da jama’a da yada bayanai na NAF, ranar 9 ga watan Nuwamba aka kaddamar da shirin a karkashin wata hadakar shirye-shirye biyu wadanda aka yi wa taken   “Operation HADIN KAI da Operation FANSAN YAMMA.”

Ehimen ya kwatanta shi a matsayin wani yunkuri na NAF na yaki da ta’addanci da ‘yan fashin daji dan shawo kan ayyukan kungiyar ISWAP.

“An kaddamar da shirye-shirye masu kama da wannan a jihohin Zamfara da Kaduna, inda aka hallaka ‘yan ta’adda yayin da suke kan babura suna yunkurin tserewa. Sun yi nasarar hallaka su ne tsakanin hanyar Birnin Gwari da Funtuwa,” ya bayyana.

Jaridun The Punch da Daily Post su ma sun dauki wannan labarin kamar yadda za ku iya gani a nan da nan.

A Karshe

Dakarun Najeriya ne suka kaddamar da wannan hare-haren a kan ‘yan ta’adda a Kaduna ba Amurka ba dan haka wannan labarin yaudara ce kawai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »