|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai mafani da shafin Facebook na da’awar wasu ‘yan ta’addar da ake zargi Fulani ne sun cire kan shugaban kungiyar kiristocin Najeriya na CAN a jihar Adamawa.

Hukunci: Yaudara ce. Rahotannin da mu ka samu sun nuna cewa bidiyon da aka yo amfani da shi wajen da’awar tsoho ne tunda tun a shekarar 2020 aka yi amfani da shi. Bacin haka ma, kafofin yada labarai masu nagarta sun rawaito cewa shugaban kungiyar CAN din ya na raye a cikin koshin lafiya.
Cikakken bayani
A ‘yan kawanakin da suka gabata al’umma ta yi ta koke-koke kan abin da aka kira “kisan kare dangin da ake wa kiristoci,” tare da zargin cewa da hannun gwamnatin tarayya ma wajen a ciki. Wani ya ja hankalin kasa da kasa har ma shugaban kasar Amurka Donalad Trumo ya ayyana Najeriya a matsayin “Kasar da ake dauka mai matukar damuwa.”
Bisa la’akari da haka ne, wani mai amfani da shafin Facebook, Ochoms TV, ya wallafa wani bidiyo wnada ya yi mafari daga gidan talibijin Television Continental (TVC) wanda ke nuna cewa wai wasu ‘yan ta’adda sun fille kan shugaban kungiyar CAN na jihar Adamawa.
“Labari da dumi-dumi!” ‘Yan ta’adda sun fille kan shugaban kungiyar kiristoci na Kan a jihar Adamawan Najeriya,” Mawallafin Bya rubuta.
Wasu da’awowin su ma masu kama da wannan sun bulla a shafin na Facebook a nan da nan, da kuma wannan a shafin X.
Ranar Lahadi tara ga watan Nuwamban 2025, mutane 19 su ka latsa alamar like da tsokaci uku sa’annan an raba sau 28.
Duk da cewa wani shi ma mai amfani da shafin ya bayyana cewa ‘yan sandan jihar Adamawa sun karyata labarain, wasu sun cigaba da nuna takaicinsu.
Bisa la’akari da sarkakiyar da irin wannan batun ke da shi musamman yayin da ake wannan mahawara ta kisan kare dangin kiristoci a Najeriya, DUBAWA ta ga cewa ya dace ta tantance sahihancin labarin dan kada ya kai ga wata matsala.
Tantancewa
DUBAWA ta fara binciken ne da yin amfani da mahimman kalmomi dangane da sare kan shugaban kungiyar CAN na jihar Adamawa da kuma labarin da tsahar TVC ta wallafa a kan batun. Muna da wani bidiyon TVC mai kama da wanda mai da’awar ya wallafa.
A shekarar 2020 aka wallafa wannan bidiyon a shafin YouTube, inda a lokacin shugaban kungiyar CAN reshen Adamawa, Steven Manza, ya sanar cewa kungiyar Boko Haram ta cire kan Lawan Andimi, shugaban kungiyar CAN a karamar hukumar Michika da ke jihar ta Adamawan.
“Bishop Steven Dami Manza ya yi bayanin cewa, ‘yan ta’addar wadanda daga farko suka bukaci fam miliyan biyu, sun ki karbar tayin naira miliyan 50 din da aka yi tayin ba su sa’annan suka kashe shi, kamar yadda hoton ya yi karin bayani.
A waje guda kuma sakamakon wannan da’awar da ke cewa an cire kan shugaban kungiyar CAN resehn Adamawa, jaridar The Guardian ta yi labarin cewa reshen matasa na kungiyar CAN wadda aka fi sani da YOWICAN ta karyata wannan zargin.
Shugaban kungiyar, Gabriel Shall, ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya sanywa hannu inda ya ce da’awar “baki dayanta karya ce.” Ya ce babu wani abu makamancin haka da ya faru a ‘yan kwanakin nan, duk da cewa a can baya, a shekarar 2020, ‘yan ta’adda sun kama sun kuma kashe shugaban kungiyar CAN a karamar hukumar Michika, Lawan Andimi.
Haka nan ita ma jaridar, The Nation ta yi rahoton cewa rundunar ‘yan sandan Adama da ita kanta Kungiyar ta CAN ta karyata labarin wanda ya shuhura a yanar gizo dangane da zargin kisar shugaban na CAN. Kafar yada labaran ta ce ‘yan sanda da CAN duk sun ce shugaban kungiyar a Adamawa, Joel Manzo ya na raye kuma a cikin koshin lafiya.
A Karshe
Wannan da’awar yaudara ce kawar. Rahotanni sun nuna cewa a shekarar 2020 ne aka fara dora wannan bidiyon a shafin yanar gizo. Shugaban kungiyar na CAN a jihar Adamawa yanzu yana raye, ba abin da ya same shi.




