Senate President Godswill Akpabio. Photo source: Vanguard
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X Morris Monye yayi da’awar cewa Akpabio na yin sallah a cikin babban masallacin Abuja.

Hukunci: Yaudara ce! Bincike ya tabbatar da cewa Akpabio ya shiga masallacin Abuja ne don halartar daurin auren ‘yar Sanata Danjuma Goje.
Cikakken Sako
Akwai dai tarin tambayoyi shin Musulmi zai iya shiga Coci ko Kirista zai iya shiga Masallaci. Ga irin wadannan tambayoyi kamar yadda za a gani a wadannan wurare (here, here, here).
Ana tsaka da wannan sai ga wani mai amfani da shafin X @Morris_Monye, ya wallafa wani labari cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya Godwills Akpabio, yana sallah a cikin Babban Masallacin Abuja, mai da’awar na cewa wani salo ne irin na ‘yansiyasa.
“Siyasa!!!! Kalli Akpabio na gudanar da sallah a cikin Masallaci,” kamar yadda ya wallafa.
Ya zuwa ranar 26, ga Oktoba, 2024, wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu 2,800 (likes) da masu sake wallafawa 688 (reposts) da masu tsokaci 406 (comments).
Hety Erabhahiemen, da take mayar da martani kan wannan wallafa (commented) ta ce, “Abin dariya idan takwarorinsa ne Musulmi ba za su je Coci ba don shugabanninsu kawai su yaba.”
“Wadannan mutane ba sa nuna kulawa a wannan lokaci” Lucy Nkem ta ce (reacted.)
Emmy Steven shima yayi nasa sharhin (commented), “Wadannan mutane basa mika wuya ga addini. Cikinsu ne kawai a gabansu.”
DUBAWA ta fahimci yadda labaran karya ke haddasa rikici na addini don haka ya zama wajibi a gudanar da bincike don gano hakikanin gaskiya.
Tantancewa
DUBAWA ta yi amfani da dabarun gano asalin hoto ta hanyar amfani da Google Lens, a nan sai ta ga labarai da kafafan yada labarai suka yi kan wannan hoto dai.
A cewar rahoton (report), Shugaban majalisar dattawan Najeriya Godwills Akpabio na daga cikin manyan baki da suka halarci daurin auren diyar Sanata Danjuma Goje a ranar Juma’a 25 ga Oktoba,2024.
Mista Goje ya kasance dan majalisa mai wakiltar Gombe ta Tsakiya kuma tsohon gwamnan Gombe.
Rahoton ya nunar da cewa (shows) an yi daurin auren Fauziyya Danjuma Goje da Aliyu Ahmed Abubakar a Babban Masallacin Juma’a na Abuja bayan gudanar da Raka’a biyu ta sallar Juma’a.
Wannan ya nunar da cewa Akpabio ya shiga Masallacin ne don halartar daurin aure bayan an gudanar da sallah.
Hoton da ya nunar da mutanen da suka halarci sallah babu Sanata Godswill Akpabio.
A ci gaba da gudanar da bincike, mun dauko hoton bidiyo da Premium Times’ ta dauko a lokacin, mun zurfafa bincike a kan bidiyon sai muka gano cewa baki daya babu inda Godswill Akpabio yake lokacin da ake gudanar da Sallar Juma’a. Ya bayyana ne kawai lokacin da ake daurin aure.
A Karshe
Da’awar cewa Sanata Godswill Akpabio na gudanar da sallah a Babban Masallacin Abuja yaudara ce! Rahotannin kafafan yada labarai sun nunar da cewa shugaban majalisar dattawan ya je wajen ne don halartar daurin aure ba yin sallah ba.
