|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Mai amfani da shafin Instagram ya wallafa wani bidiyon da ke ikirari cewa an Kama Kiristoci a yankin arewacin Najeriya an daure su ana saida su dan su je su yi bauta.

Hukunci: Yaudara ce! Bidiyon tsoho ne kuma ba shi da wata alaka da Najeriya. Rahotannin da muka samu daga kafofi masu sahihanci sun danganta shi da kasar Kwango.
Cikakken bayani
Wani mai amfani da shafin Instagram, @Apostleamosngosha, ya wallafa wani bidiyo (archived here) ya na da’awar wai ana kashe kiristoci wasu ma sayar da su ake yi su je su yi bauta a wasu wuraren.
“Abin da ke faruwa a Najeriya ke nan. Ana kashe kiristoi kuma yawancinsu ma saida su ake yi a sa su bauta. Kun san cewa a Islama ce ta fara bauta sadda suka mamaye yankin Arewacin Afirka?” ya rubuta cikin taken da aka yi wa bidiyon.
A cikin wannan bidiyon dai ana iya ganin mata da maza cikin rukunansu suna tafe cikin layi da hannayensu daure a bayan su, jikinsu na rawa dan zafi. Sa’annan ana iya ganin wasu maza cikin kayyayakin da ba’a iya tantancewa ba suna rike da bindigogi suna biye da sy yayin da suke tafe cikin cabi.
Daga 28 ga watan Yunin 2026, labarin na da alamar like 59 da tosakace-tsokace 22. Haka nan kuma labarin ya dauki hankali sosai a shafin X da Facebook, da nan.
Wani mai amfani da shafin X, @globalrevival91, ya goyi bayan da’awar da tsokaci kamar haka, “Abin da ke faruwa a Najeriya ke nan: Ana hallaka kiristoci, kuma yawanci ana sayar da su cikin bauta. Ko kun san cewa bauta na da asali daga addinin Islama ne sadda suka mamaye yanikin arewacin Afirka?”
Wani shi ma mai amfani da shafin Prince Robinson, ya yi tababa dangane da sahihancin da’awar, inda ya ce: “Yanzu ‘yan sanda su ma sun zama masu yin garkuwa da mutane ne, domin na ga wani dan sanda rike da wata doguwar bindiga a gaban wadannan mutanen wadanda ba su ji ba su gani ba?”
DUBAWA ta yanke shawarar tantance wannan batun saboda irin sarkakiyar da ya ke da shi ganin yadda batu ne da ya shafi tsaro kuma akwai ra’ayoyin da suka sabawa juna.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da tantance mahimman kalmomin da ke da alaka da da’awar amma babu abin da ya bulla a sunan rahoto ko labari dangane da wannan batun.
Bayan nan mun yi amfani da manhajar tantance hotuna ta yin amfani da wasu bangarorin bidiyon masu mahimmanci. Daga nan ne bincikenmu ya kai mu ga ainihin bidiyon da aka fara wallafawa a watan Mayun 2026, watanni da dama kafin aka danganta wannan da’awar da bidiyon a Najeriya.
Mun gano wani labarin da aka wallafa a shafin Kivumorningpost.cd (@KivuMorningPost) da wannan bidiyon ana da’awar wai ya na kwatanta daruruwan fararen hula daga yankin Kudancin Kivu wadanda aka kama a yankin Kunda da ke lardin Ituri can a Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kwango, wato DRC.
Mun yi amfani da wadannan bayanan wajen sake fadada binciken inda muka sake ganin wani rahoton da aka wallafa a shafin Radio Okapi ranar 14 ga watan Mayun 2026 a Kwango
Mun yi amfani da manhajara fasarar Google dan yin bitan rahoton tunda cikin harshen Faransanci aka wallafa. Wannan rahoton na Radio Okapi ya ce majiyoyin tsaro sun ce yawancin fararen hulan da abin ya shafa matasa ne daga yankin kudancin Kivu. Kasancewarsu a wurin ya ja hankalin ‘yan sanda ya sa su zargin sahihancin dalilin da ya kai su wurin.
Ko da shi ke, wasu majiyoyin sun ce matsan da kan su suka je Kunda dan yin aikin gona da hakan zinarin da ake samu sosai a yankin.
However, sources claimed that the individuals had gradually arrived in Kunda to work in agricultural and gold mining activities.
A Karshe
Bidiyon da aka wallafa a soshiyal mediya ba Najeriya ba ne. Ainihin lamarin ya faru ne a kasar Kwango cikin watan Mayaun 2026 kuma ba shi da wata alaka da Najeriya bare ma kiristocin Najeriya.
