|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani D English Alhaji a Shafinsa na facebook ya saka wani bidiyo dake nuna yadda aka kashe wasu mahara hudu kuma aka banka wa gawan su wuta a kauyen Aboki dake karamar hukumar Jega a jihar Kebbi.

Hukunci: Karya ce! Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa hakan ya faru ne a kauyen Aboki dake karamar hukumar Kaiama dake jihar Kwara ba a jihar Kebbi ba sannan rahotanni basu tabbatar cewa an babbake gawanwakin wadannan mahara ba.
Cikakken bayani
A shafinsa na Facebook D English Alhaji ya wallafa wani bidiyo a (nan) da ya nuna cewa an kashe wasu mahara hudu kuma an banka wa gawanwakin su wuta a kauyen Aboki dake karamar hukumar Jega a jihar Kebbi.
Da’awar bidiyon ya ce ‘Jiya, 21 ga Yuli 2026 da karfe 10:15 na yamma dai-dai mahara sun kai wa kauyen Aboki dake karamar hukumar Jega a jihar Kebbi hari. Maharan sun yi kokarin yin garkuwa da wani dan kasuwa a kauyuen Alhaji Tukur amma sai dai kafin hakan ya faru kungiyar ‘yan bijilante sun samu labarin harin inda bayan maharani sun shigo kauyen suka yi batakashi da su na tsawon awa daya.
A dalilin haka ‘yan bijilante din suka samu nasarar kama mahara biyu, sun kashe hudu tare da banka wa ganwanwakin su wuta.
A ranar 23 ga Yuli 2026 wannan da’awar ya samun mutum 39,000 da suke son bayanin, 4,000 sun mayar da martani, 1,000 sun sake wallafawa. Mutane da dama a Facebook sun amince da wannan bayani sai dai kuma wasu sun nuna cewa kauyen Aboki a jihar Kwara yake ba a jihar Kebbi ba.
Njoku Ugochukwu a shafinsa na Facebook ya ce ‘Barka ga ‘yan bijilante din Aboki masu hankali’.
Ayuba Sunday ya rubuta ‘Barka ga ‘yan bijilante masu jarunta. English Alhaji zai bayyana duk wani abin dake boye’.
Sai dai kuma wasu sun nuna rashin amincewarsu da kauyen da aka dauki bidiyon.
Emmanuel Nworie ya ce ‘Amma ran kashi dade Aboki na karamar hukumar Kaiama ne dake jihar Kwara a Najeriya’.
Shima Mohammed Sani Salihu ya ce ‘ Aboki a karamar hukumar Kaiama dake jihar Kwara ne yake’.
anin rashin tabbatar da inda aka dauki bidiyon ne ya sa DUBAWA gudanar da binciken.
Tantancewa
DUBAWA ta yi amfani da ‘Google Keyword’ domin gano ko wasu kafafen yada labarai sun wallafa labaran da ke da alaka da kisan mahara da banka musu wuta a kauyen Aboki da ke karamar hukumar Jega a jihar Kebbi.
Sakamakon binciken ya nuna cewa kauyen Aboki na karamar hukumar Kaiama ne dake jihar Kwara lamarin ya faru.
Gidajen jaridu da suka hada da ‘Nigerian Tribune, Leadership NEWSPAPERS, Daily Post Nigeria, TVC NEWSda Western Post duk sun buga labari game da aukuwar wannan lamari. Rahotanin da suka bada ya nuna cewa lamarin ya faru ranar Talata 21 ga Yuli 2026 inda wasu mahara su biyar suka kai waw ani kauyen hari inda daga shigan su suka bud awa mutane wuta da misalign karfe 10:15 na yamma. Harin ya yi ajalin wani mazaunin kauyen Musa.
Maharan sun yi garkuwa da wani dan kasuwa a kauyrn Alhaji Tukur amma sai hadaddiyar kungiyar jami’an tsaro da suka hada da sojoji da bijilante suka ceto mutumin. Gaggawan daukin da jami’an tsaron suka bada ya sa suka samu nasarar kashe hudu daga cikin maharani inda daya ya gudu da ranin harsashi a jikinsa.
Kafaffen yada labarai duk sun tabbatar cewa lamarin ya faru ne a kauyen Aboki dake karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara ba a jihar Kebbi ba.
DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano bayanan da hukumomin jihar suka fitar game da aukuwar lamarin inda ta gano wani takarda da Gwamnatin Jihar Kwara ta fitar wanda ya kara tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kaiama jihar Kwara.
DUBAWA ta kara duba Shafin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara na yanar gizo inda ta ga cewa rundunar ba ta saka sanarwa ba tun ranar 17 ga Yuli 2026. Binciken da gidan jaridar ta kara gudanarwa ya sa ta gano labarin da ‘PUNCH’ ya buga inda yake nuna cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara Adekimi Ojo ya tabbatar da awkuwar lamarin.
DUBAWA ta gudanar da wani binciken domin tabbatar da ko an bank awa maharani wuta inda rahotanin da gidajen jaridu masu tushe suka fitar ya tabbatar cewa an kashe maharani amma ba a kona gawan su ba.
DUBAWA ta yi amfani da ‘Google Reverse Image’domin gano ko akwai rahotanin da za su tabbatar an babbake gawan maharani amma sai bata samu ba.
A duk binciken da DUBAWA ta gudanar babu rahotani, bayanai daga wajen gwamnati, rundunar ‘yan sandan da yavtabbatar cewa wannan lamari ya faru a jihar Kebbi ba kuma ba a kona gawanwakin maharani da aka kashe ba.
A halin da ake ciki Gwamnatin jihar Kebbi da Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ba su fitar da wani takarda ba domin tabbatar da aukuwar lamarin a jihar ba.
A Karshe
Da’awar cewa an kashe mahara hudu kuma an kona gawawwakinsu a kauyen Aboki dake karamar hukumar Jega jihar Kebbi karya ne.
Sakamakon binciken da DUBAWA ta gudanar ya tabbatar cewa kauyen Aboki a karamar hukumar Kaiama yake a jihar Kwara amma ba a jihar Kebbi ba sannan maharani da aka kashe ba a kona gawan su ba.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
