|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani hoto image mutum dauke da kai ya daga sama da ya bazu a shafukan sada zumunta an yi zargin cewa ya fito ne daga “gasar hako kan mutane.”

Hukunci: A bincikenmu mun gano hoton na wani mutum ne da aka kama da laifin cire kan wani a jihar Binuwai a watan Yuli, 2015. Labarin da aka makalawa wannan hoto yaudara ce.
Cikakken Sakon
Wani hoto (image) mutum ya daga kan mutum da aka cire a baya-bayan nan ya bazu a shafin X da Facebook. Mutumin an bayyana shi da suna “Adekunle,” ana taya shi murna ta yin nasara a wata “zazzafar gasa” ta hako kan mutane a wani yanki da ba a sani ba a Kudu maso Yammacin Najeriya.
Hoton an rika baza shi da wannan rubutu guda daya:
“Ku kalli Adekunle, wanda yayi nasara a gasar samun kawuna ta 2023/2024.” Gasa ce mai zafi da aka fafata , muna tayaka murna da fatan samun kawuna da dama Adekunle.”
Hoton da ake tantama a kansa. Asalin hoto : Facebook.
Wasu daga masu amfani da shafukan sun yarda da labarin, wasu kuwa sun nuna shakku kan yiwuwr hakan, wasu kuwa sun sanya kabilanci kan batun , DUBAWA ta gudanar da bincike kan batun don warware komai.
Tantancewa
DUBAWA ta gaza gano inda ake gudanar da gasar hako kan mutane a koina a fadin Najeriya. Wannan ana ganinsa babban laifi kamar yadda aka tanada a sashi na 329A na dokar miyagun laifuka wacce ta bayyana cewa, “Duk mutumin da aka samu da kai ko kwarangal na kan mutum cikin watanni shida da aka yanko kan nan daga jikin mutum ko kwarangal na jikin dan Adam da niyar cewa a ajiye da wannan kai a matsayin wata shedar nasara ko tsafi ko Juju ko ya mika abun zuwa ga wani ko aka bashi a matsayin alamar nasara ko tsafi ko juju to an same shi da laifin cin amanar kasa kuma za a tsare shi a gidan gyara hali tsawon shekaru biyar.”
Da muka gudanar da bincike don gano asalin hoton sai muka lura cewa hoton an dauko shine daga wani rahoto na laifi da aka bayar ranar 13 ga Yuli,2015 a Utonkon, karamar hukumar Ado a jihar Benue. Hoton mutumin da ke a hoton sunansa Raphael Agazi wanda aka kama shi bisa zargin yanke kan mokocinsa Ajah Asim saboda rikici a kan gona.
A cewar labaran da jaridun The Nation da Vanguard, Mista Agazi ya bayyana cewa ya so yayi amfani da jikin makocinsa ne don tsafi. Dukkaninsu manoma ne.
A Karshe
Da’awar cewa wannan hoto an dauko shine daga wata “gasar hako kan mutane” yaudara ce kuma ya kawar da hakikanin abin da ya faru na cewa asalin hoton na wani ne da ya aikata babban laifi.
