African LanguagesHausa

Yaudara! Sukari kadai ba zai iya haddasa hawan jini a jikin dan adam ba, dole sai ya hadu da wasu sinadaran

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Sukari ya fi janyo hawan jini a dan adam fiye da gishiri

Yaudara! Sukari kadai ba zai iya haddasa hawan jini a jikin dan adam ba, dole sai ya hadu da wasu sinadaran

Sakamakon bincike: Yaudara. Ma’aikatan kiwon lafiyda da kwararru duk sun ce sukari da gishiri duk suna iya yin sanadin hawan jini a jikin dan adama.

Cikakken bayani

Hawan jini ko kuma tansion a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, shi ne idan bayan an gwada mutun aka ga ma’aunin ya nuna cewa jinin mutun ya hau sosai wato akalla 140/90 mmHg ko fiye na ma’aunin duba hawan jinin

Wata mai amfani da shafin X, Callipigous Kemi (@AdekemiSaliu), na da’awar cewa kamata ya yi a danganta hawan jinin da kan dami dan adam da sukari ba gishiri kadai ba kamar yadda ake yi yanzu.

“Hawan jini matsala ce ta sukari ba gishiri ba. Gishiri ba shi da laifi. Sukari ne,” ta bayyana.

Wannan rubutun na ta martani ga wani batun da wani ya wallafa wani influencer a shafin X mai sunaChinonso Egemba wanda aka fi sani(@aproko_doctor), inda ya ke kira ga masu amfani da soshiyal mediya da su rage amfani da gishiri saboda ya kan janyo hawan jini.

Wannan bayanin ya janyo tsokaci 348 kuma mutane 994 sun yayata yayin da wasu 1,100 kuma suka latsa alamar like. Har ila yau mutane sama da miliyan daya sun yi ma’amala da bayanin. Wasu ma sun kebe sun ajiye sau 306 tun ranar Litinin 22 ga watan Janairun 2024.

Sai dai akwai wadanda suka bayyana ra’ayoyin da suka banbanta da wannan suna tababar sahihancin shi

Dr G The Frontliner (@iamSwaga22) ya ce, wannan ba gaskiya ba ne kai tsaye. “Kemi kin san wannan ba gaskiya ba ne ko?” ya tambaya. 

Edible Euphoria (@VickeysBatter), a waje guda kuma ta amince ne da tsokacin inda ta ce, “Kwarai haka ne na yadda.”

Domin wadannan ra’ayoyi mabanbantan da tsokacin ya janyo, DUBAWA ta yanke shawarar tantance gaskiyar lamarin.

Tantancewa

Kasidar lafiya ta Healthline ta ce mutun ya fi samun hawan jini saboda tsufa, kwayoyin halitta, ko kuma ma dai abubuwan da ke nasaba da kiwon lafiya. Sauran abubuwan da kan janyo hawan jini kuma sun hada da cututtukan da kan shafi koda, rashin baci da kyau saboda matsalar numfashi da kuma cututtukan da kan shafi zuciya.

Haka nan kuma kasidun Medical News Today da Cleveland Clinic su ma sun amince da bayanan Healthline. 

Shin sukari na iya janyo hawan jini (hypertension)?

A cewar Healthline, sukari na daya daga cikin abubuwan da ke kara hawan jini. Mujallar likitoci ta ce sukarin da ke cikin irin lemun kwalban da aka kara wa zaki, yawanci ya kan sa kiba a manya da kananan yara. Bacin haka, ita kanta kiba na iya janyo hawan jini.

Arefa Cassoobhoy, wata likita, a tattaunawar da ta yi a shafin likitoci na WebMD dangane da batun, ta ce sukari, a maimakon gishiri, zai iya kasancewa “babban makasudin” hawan jini.

To sai dai ta kwantar da hankulan masu bin jawabin na ta da cewa sukarin da take magana a kai ba wanda ake samu daga ‘ya’yan itace ko kayan lambu ba ne. A’a irin sukarin da akan kara a cikin abinci ne kamar irin wanda ake samu da raken da aka sarrafa aka yi sukari da ma dai sauran abubuwan da ake amfani da su wajen sarrafa sukarin da ake karawa a abinci.

A cewar Dr Cassoobhoy, shan kofi uku na lemun kwalba zai iya janzo hawan jini a mutun. Ta kuma kara da cewa idan har kashi 25 cikin 100 na yawan abincin da mutun kan ci kullun sukari ne yiwuwar kamuwa da hawan jininsa zai karu fiye da na wanda alal misali ke cin abincin da yawan sukarin shi bai kai kashi 10 cikin 100 ba.

Wata kwararriya kuma likitar abinci, Kate Patten ta yi magana da Cleveland Clinic inda ta bayyana wasu daga cikin matalalin da sukari ke da shi a zuciyar mutun. Ta ce cin abinci masu yawan sukari na iya janyo “kiba mai lahani” wanda aka fi sani da obesity da turanci. A cewar ta, irin wannan kiban na kara yiwuwar kamuwa da cutar sukari da hawan jini da yawan sinadarin cholesterol (sinadari ne wanda ake samu a jinin dan adam, ana bukatar shi dan gina kwayoyin jini masu lafiya, amma idan har ya yi yawa yana iya yin lahani ga zuciya).

Likitar abincin wadda ta lakanci irin abincin da ke kare zuciya ta jaddada cewa dama can kiba na da “alaka” da abincin da ke cike da sukari, wanda zai iya sanadin hawan jini.

To gishiri fa?

A cewar kungiyar kula da hawan jini na Burtaniya Blood Pressure UK, gishiri kan iya sa jikin mutun ya rike ruwa. Wannan na nufin idan mutun ya ci gishiri da yawa (yawanci a abinci) zai iya sa ruwa tsayawa a cikin jini wanda kuma zai matsawa bangon inda jinin ke bi lamba. Wannan kuma zai iya kaiwa ga hawan jini.

Blood Pressure UK ta kuma kara da cewa koda kan taimaka wajen cire ruwan da ke cikin jikin mutun da sauran sinadaran da ba ya bukata dan daidaita hawan jini. Kodar ta kan dauki duk ruwan da ya yi yawa a jinin mutun ta fitar da shi ta mafitsara. Ta kan yi haka ne ta yin amfani da wani salon da ake kira osmosis da turanci, inda ruwa kan fita daga jinin mutun sadda sinadarin sodium ya yi kasa zuwa sauran gabobin jikin da ke da sodium da yawa (sodium sinadari ne da ake yawan samu a cikin gishiri) 

Ko da shi ke, gishiri ne ke bai wa jiki sodium, kuma duk sadda aka ci gishiri da yawa, yakan lalata daidaitawar da ke tsakanin gishirin da ruwa. Wannan ne kuma yawanci ya kan kara matsawa kananan hanyoyin jinin da ke cikin koda lamba.

Wata mujallar Harvard T.H. Chan School of Public Health ta bayyana cewa koda kan taimaka wajen daidaita yawan sodium a jiki. Da zarar sodium ta yi yawa a jiki, dan kansa jikin mutun ya kan yi kokarin surkawa dan ya rage karfin. To sai dai wannan ya kan kara yawan ruwan da ke kewaye da kwayoyin jikin , da ma yawan jinin da ke cikin jikin mutun.

Bacin haka, idan har jini ya yi yawa a jikin mutun, aikin zuciyar mutun zai karu ke nan wanda kuma zai sake matsawa hanyoyin jinin lamba. A cewar wannan mujallar, wannan yawan aikin ne zai iya “sankarar” da hanyoyin hjinin wanda zai kara kaiwa ga hawan jini.

Gishiri ko sukari, wanne ne ya fi haddasa hawan jini?

Healthline ta ce yayin da abinci masu gishiri ne ke janyo hawan jini, su ma abincin da ke dauke da sukari da wadanda aka sarrafaffen mai na iya sanya mutun cikin hadarin kamuwa da hawan jinin.

Bisa bayanan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, abincin da ke dauke da gishiri mai yawan gaske, da kiba (saboda cin abincin da ke da maiko da gishiri da sukari) ne ke da alhakin kawo hawan jini.

Abin da kwararru ke cewa

Cikin wata tattaunawa da likitar abinci da bayar da shawarwari kan yanayin rayuwa, Temiloluwa Omotoso, ta yi bayanin cewa jikin mutun na da wani tsari na yadda ya ke daidaita yawan ruwa da gishiri. Idan har aka samu karuwa a sinadarin sodium, yawan ruwan da ke jikin mutun zai karu. Wannan ne kan sa jikin mutun ya rike ruwa sosai.

“Idan har jikin mutun ya rike ruwa, zai kara yawan hjini, kuma wannan karuwar a yawan jinin zai kara matsin lamba a abin da masana ke kira bangon magudanar jini, ko kuma inda jinin ke bi ya je sauran gabobin jikin,” ta bayyana.

Ms Omotoso ta kuma kara da cewa, sakamakon wannan matsin lambar da ake gani a magudadan jinin, sai su tsuke ta yadda jinin ba zai iya wucewa cikin sauki ba.

Da take danganta sukari da cutar sukarin na diabetes kuma, ta ce cin abinci mai sukari ko sukarin kanta, na rage kaifin aikin sinadarin insulin a jiki. A cewarta yayin da sinadarin insulin ke da mahimmanci wajen kai abincin da ya zama glucose a cikin jiki, wato sukari ke nan, zuwa ga kwayoyin jikin da ke bukata, rashin shi ya kan sa sinadarin na glucose ya yi yawa a jikin mutun. Kuma idan haka ya faru sai sukari ya yi yawa fiye da kima a cikin jikin mutun.

A waje guda kuma, yayin da ta ke mayar da martani dangane da wannan batun, Bunmi Ojo, likitar abincin da ke aiki a asibitin koyarwa na Ibadan, ta ce duk sadda aka ci abinci, wadanda ke zaman carbohydrate, wato kamar shinkafa, hatsi, doya da sauransu, jikin kam mai da su sukari, wadanda ke shiga jinin mutun kai tsaye. Kuma da zarar suka shiga cikin jini, sai su makale, suna jiran sinadarin insulin ya dauke su daga jinin ya kai su zuwa sauran gabobin jikin da ke dauke da kwayoyin da ke bukatar su.

Idan har sukarin ya gaza barin jikin mutun (sakamakon karancin sinadarin insulin) bangon magudanar jinin sai su kara kauri saboda yawan sikarin da ke cikin jikin. Mrs Ojo ta kara da cewa, idan har sukarin da ke cikin jinin na da yawa, za’a sami jinkiri wajen tafiyar jinin zuwa sauran gabobin da ake bukata kuma dan haka, mahimman gabobin jikin da suke bukatar jinin za su fara kokarin tura sako dangane da abubuwan da ke faruwa zuwa ga zuciyar. Wadannan sakonnin sai su sa zuciyar ta kara matsawa magunar jinin lamba. Da zarar zuciyar ta fara matsawa jinin lamba, sai hawan jinin ya karu.

Likitar abincin ta ce ba sukari ne kadai ke jawo hawan jini ba, domin ya na aiki da sauran abubuwan da ke haddasa hawan jinin a jiki ne kamar sodium (wanda gishiri ne) da kuma abubuwa masu maiko.

Shugaban kungiyar likitocin abincin Najeriya Mr Wasiu Afolabi, sadda ya ke hira da jaridar Punch dangane da wani batun da ke da alaka da wannan, yayi bayanin cewa  amfani da sukari sosai na iya sanadin hawan jini.

A cewarsa, “saboda sukari kan hadu da gishiri a matsayin abubuwan da jiki ke amfani da su musamman glucose, idan har aka ci sukari da yawa lallai zai shafi hawan jini.”

A karshe

Wannan da’awar zai iya ruda mutane. Yayin da cin sukari da yawa kan kara hawan jini, shi kadai ba tare da sauran sinadaran da aka bayyana ba, ba zai iya haddasa hawan jini ba. Gishiri ma na iya janyo hawan jinin a jikin mutun.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button