African LanguagesHausa

Babu kwakwarar hujjar cewa ‘yan awaren Biafra sun kai hari kan motar sojoji a yankin Kudu maso gabashin Najieriya har sun yi awon gaba da makamai

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Dakarun Biafra sun kama wata motar sojoji sun kai mata hari sun kwashe makaman da ke ciki.

Babu kwakwarar hujjar cewa ‘yan awaren Biafra sun kai hari kan motar sojoji a yankin Kudu maso gabashin Najieriya har sun yi awon gaba da makamai

Sakamakon binciken: Karya! Motar da aka yi amfani da ita wajen kwatanta lamarin ba ma motar sojoji ba ce.

Cikakken bayani

Yakin basasar Najeriya wadda aka fi sani a turance da Biafra War (wanda aka fara daga 6 ga watan Yulin 1967 har zuwa 13 ga watan Janairun 1970) yaki ne na siyasa wanda yunkurin ballewar yankin kudu maso gabashin kasar ya janyo. Yankin wanda ya kunshi lardunan da yawancin al’ummominsu kabilar Igbo ne ya yi yunkurin yin hakan ne da nufin girka kasar da za su kira Jamhuriyar Biafra.

Simon Ekpa, daya daga cikin jagororin mas rajin girka ‘yantacciyar kasar Biafra, ya wallafa a shafinsa na X cewa kungiyar ta kama sojojin Najeriya ta kashe su ta kum kwashe makaman da suke tafe da su a cikin motarsu.

Hotuna da bidiyoyin da ya wallafa sun nuna wata mota na cin wuta, da wasi bangarorin da suka balle wadanda duk ake zargin cewa daga jikin motar sojojin suka fito.

Wannan batun ya janyo ra’ayoyi mabanbanta a wurin da ake tsokacu. Misali @charloE80 ta rubuta “Kun yi da kyau ‘yan uwa, Bravo!

Ko da shi ke wani mai amfani da shafin, @SpiceP2E, ya tambayi abun da ya sa lambar motar ta fita daban da na motar sojoji kamar yadda aka san su.

Tun da aka wallafa wannan labarin, alkaluman da ke kan shafin sun nuna cewa an kalla sau 429,000 an sake wallafawa sau 2,000, mutane  3,000 sun latsa alamar like, wasu 152 sun yi amfani da labarin wajen wallafa batun a shafukansu. 

Ra’ayoyi mabanbanta da yawan mutanen da suka yi ma’amala da labarin ne ya sa DUBAWA ta yanke shawarar tantance sahihancin wannan batun.

Tantancewa

Mun yi nazarin hotunan da aka wallafa da kyau inda muka ga cewa lallai lmabar motar ba ta dace da irin lambobin da sojojin Najeriya ke amfani da su ba.

Babu kwakwarar hujjar cewa ‘yan awaren Biafra sun kai hari kan motar sojoji a yankin Kudu maso gabashin Najieriya har sun yi awon gaba da makamai

Lambar motar na ‘yan sanda ce ba ta sojoji ba

Irin motar da aka yi amfani da shi ma duk da cewa an gane wai na ‘yansanda ne, ba ma irin wadda suke sintiri da ita irin ta rakiya ce. 

Babu kwakwarar hujjar cewa ‘yan awaren Biafra sun kai hari kan motar sojoji a yankin Kudu maso gabashin Najieriya har sun yi awon gaba da makamai

Wannan hoton na dauke da irin motar da ‘yan sanda ke fita sintiri da ita. 

Mun kuma dauki lamabar motar mun sa a manhajar da ke tantance lambobin motoci a Najeriya wadda aturance ake kira National Vehicle Identification system, a nan kuma manhajar ta tabbatar mana cewa ba ta san lambar ba kamar yadda za ku gani a hoton shafin da ke kasa.

Babu kwakwarar hujjar cewa ‘yan awaren Biafra sun kai hari kan motar sojoji a yankin Kudu maso gabashin Najieriya har sun yi awon gaba da makamai

Babu wata hujjar da ke nuna cewa an karbi wasu makamai daga wurin sojoji. Mun kuma gudanar da bincike na musamman kan wannan zargin, kuma nan ma babu abun da muka samu, hatta kafofin yada labarai masu nagarta ma ba su dauki labarin ba.

A Karshe

Hoton motar da Mr Ekpa ya wallafa yana zargin wai na sojoji ne ba haka ba ne. Lambar motar ta banbanta da irin wanda aka san sojoji na amfani da su.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button