Dalibai na karbar darasi:Asalin hoton Ripples Nigeria
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X na da’awar cewa fiye da kashi 70 cikin 100 na al’ummar Najeriya ba su da ilimi.

Hukunci: Karya ce! Binciken baya-bayan nan wanda ma’aikatar ilimi a Najeriya ta yi ta yi kiyasin cewa kashi 31 cikin dari ne kadai ba su da ilimi.
Cikakken bayani
Yayin da ake cigaba da takaddama tsakanin sanata Natasha Apoti da Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa, wani bidiyo ya bayyana a soshiyal mediya ya na nuna rukunin wasu mata a jihar Kogi a sunan wai sun taru ne domin su bukaci da a kira Sanata Natasha.
Yayin da ya ke bayyana ra’ayinsa a shafin Twitter/X dangane da wannan lamarin, Shehu Sadiq, mai amfani da shafin X, ya ce matan da ke cikin bidiyon ba su ma da ilimi. Sadiq ya bai wa rashin ilimi da talauci laifin gazawar mulkin dimokiradiyya a kasar, ya kuma yi da’awar cewa kashi 70 cikin 100 na ‘yan Najeriya ba su je makaranta ba.
Hoton bayanin Sadiq a shafin X . Asalin hoton: X.
Wannan bayanin na Sadiq ya janyo mahawara mai zafi tsakanin masu amfani da shafin. Yayin da wasu ke nuna akasin wannan bayanin, wasu irin su ’@UchennaObi36947, sun yi bayani kamar haka:
“Na amince da kai, aboki na, amma kuma dole ka yi la’akari da cewa wayewa ma wani bangare ne na ilimi kuma kashi 90 cikin 100 na al’ummar ‘yan area ba su waye ba kuma kashi 70 cikin 70 na mutanen Najeriyar da ka ke kira marasa ilimi su ma duk ‘yan arewa ne.”
@brenokwaraji, wani shi ma mai amfani da shafin cewa ya yi adadin ya ma fi haka yawa. “Kashi 90 cikin 100 ne ma. Wasu masu rike da digirin digir-gir ma na cikin wannan rukunin,” ya bayyana.
DUBAWA ta gudanar da wannan binciken ne dan kashe wutar wannan rikicin da ke ruruwa ta kuma fayyace gaskiyar lamarin.
Tantancewa
Rashin ilimi ba rashin iya karatu da rubutu ba ne. Yawancin lokuta lamarin ya fi haka zurfi kuma sakamakon matsaloli ne wadanda suka hada da rashin samun ilimin boko, rashin muhalli mai tsabta, kuncin rayuwa, da rashin samun karatu da wuri. Talauci kuma na kara ta’azzara lamarin, kuma wasu batutuwan da suka shafi zamantakewa su ma sukan kara na su, batutuwa irinsu jinsi, kabila da yanayin rayuwa duk su kan haddasa hakan.
Wani kiyasin da aka yi a shekarar 2022 wanda kuma ma’aikatar ilimin Najeriya ta wallafa ya sa yawan mutanen da ke fama da rashin ilimi a kasar baki daya a kan kashi 31 cikin 100. A shekarar 2025, kafofin yada labarai da Gwamnatin Tarayya na cigaba da amfani da wadannan alkaluman domin kwanan nan aka fitar da su ba’a riga an yi wani binciken ba bare a sami wasu alkaluman.
A waje guda kuma, wadanda suka yi karatu a Najeriya sun kai kashi 69 cikin 100 wanda a cewar Gidauniyar samar da tallafin cigaba, ya nuna cewa na sami karuwa da kashi 17 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda lamarin ya ke shekaru 15 da suka gabata.
Duk da cewa ana iya wa alkaluman kallon cewa sun tsufa saboda sadda aka yi su, a kuma yi tunanin ba lallai ne su kasance abun da ake gani zahiri a kasar ba yanzu.
Bayanan da ke nuna alkaluman masu ilimi a Najeriya. Asalin hoton: Dataphyte.
A Karshe
Wannan da’awar cewa kashi 70 cikin 100 na ‘yan Najeriya ba su da ilimi karya ne. Bisa bayanan ma’aikatar ilimi ta kasa kashi 31 cikin 100 ne kadai ba su yi makarantar boko ba.
