African LanguagesFact CheckHausa

Aa! Ba’a amfani da bishiyar Goba don a samar da kwai 

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi:  Wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa yadda ake shuka kwai ta hanyar amfani da bawon Goba da Aloe Vera da kasar lambu.

<strong>Aa! Ba'a amfani da bishiyar Goba don a samar da kwai </strong>

Hukunci: KARYA. Hoto da ya nuna kwai yana girma gyara shi aka yi. Bayani na masana kimiya ya tabbatar da cewa babu yadda za a shuka kwai.

Cikakken sakon

Kwai abu ne da ke da bawo mai karfi wanda dangin tsintsaye ke yinsa. Yayin da ya kasance abin da ake bukata daga kwai shine a samar nau’ikan ‘ya’yan kwai , da dama kwai kaji na gida ke yinsa, sai dai wadanda ake samarwa daga kajin wadanda ba a bukatar a kyankyashe su sai a fitar da su don amfanin al’umma.

Yawan samun hauhawar farashin kwai da ya kamata a ce abu mai sauki don samun sinadarin Protein a Najeriya. Farashin sa na ci gaba da hauhawa ta yadda ba duk iyali ke iya samunsa ba.

Saboda wannan ne masu fasaha na Rana Craft suka fito da bidiyo na yadda ake fitar da kwai ta hanyar amfani da bawon itacen  goba da aloe vera da kasar lambu.

A hoton bidiyo na mintuna hudu an ga wani mutum na yanka rassa na goba sannan ya hada da aloe vera sai ya fasa kwai ya hada da wasu sinadaran saiwa da lemon kwalba  don ya taimakawa kwan ya girma cikin sauki. Ya ce idan aka tsaya wata guda za a ga sakamako da ake bukata.

Wannan bidiyo da ya shahara ya samu masu sha’awa (likes) 6,200 da masu tsokaci (comments)1000 da wadanda suka kalla 42,500 ya zuwa 17 ga watan Agusta 2023.

Shuhurar da bidiyon ya samu da tasirin da zai yi ta fuskar tattalin arziki ta sanya DUBAWA shiga bincike kan wannan bidiyo da aka wallafa.

Tantancewa

Mun gudanar da binciken kwakwaf da nazarin bidiyon don gano siddabaru da aka yi, yanayin kyan hoton da kura-kurai sun nunar da cewa an sauya hoton.

Wannan bidiyo da hanyar da aka nunar da karbuwarsa zai iya tasiri a zukata amma mun gaggauta gano cewa babu wani batu na bishiya ta fitar da kwai da ke da yauki ko kwanduwa a cikinsa.

Hanyar da ake hada kwai

A kimiyance dama hanyar da kowa ya sani kwai na samuwa ne a mahaifar tsintsaye.

Hanyar da ake samun kwan ta kasu gida biyu kwanson gefen mahaifa (ovary) da hanyar da ke sadarwa zuwa ovary(oviduct). A Ovary anan ake tattara yaukin nan(kwanduwa) ta cikin kwai idan ya kai wani mataki sai ya rika fita yana girma ya zama dantayi cikin kwanaki 21 kafin kyankyasa.

Kwan kaza da ake siyarwa a shaguna baya fidda da saboda ba a samu saduwa kaza da zakara ba . 

Mun gano cewa wannan kwai mai rai bayan lokaci yana rubewa ne ya bi kasa ya zame mata taki. 

A Karshe

Babu wani bayani a kimiyance da ya nuna yadda ake dasa kwai ya fita daga cikin kasa. An tsara bidiyon ne aka yi masa gyare-gyare don jan hankalin al’umma.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »