African LanguagesFact CheckHausa

Shin mai ko turaran hammata (Deodorants) na da illa ga mata? 

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi:  Deodorants na kunshe na sinadarin aluminium da ke da hadari ga ‘ya’ya mata. 

<strong>Shin mai ko turaran hammata (Deodorants) na da illa ga mata? </strong>

Sakamakon Bincike: Yaudara. Bincikenmu ya gano cewa mai ko turaren hana wari hammata samfurin antiperspirants sune ke dauke da sinadarin aluminium ba deodorants ba, har ila yau bincike da ake da su yanzu kan sinadarin na aluminum da cutar daji ba su da yawa don haka ana bukatar a zurfafa bincike masu inganci.

Cikakken bayani 

Idan kai dan Najeriya ne musamman idan kana shiga shafin Twitter; za ka ga yadda ake ta musayar yawu kan batun warin jiki da bukatar a rika amfani da deodorants ko antiperspirants. 

Ana tsaka da wannan sai ga wani bidiyo a shafin Instagram da herneshealth ya wallafa cewa deodorants na haifar da tsirar ciwon daji saboda yana dauke da sinadarai na karafa masu yawa.

A wannan bidiyo an danganta amfani da deodorants da ciwuka irin na mantuwa da kaikayin jiki da rashin yin gumi da rashin daidaiton sinadaran jiki da matsalar da ke alaka da kwakwalwa da laka. 

A wannan bidiyo, matar da ke jawabi kan yadda abun yake ta ce:

“ Nonon mace na da wasu kananan halittu wadanda idan tana shafa masu aluminium a duk rana to tana zukar su a jikinta sai su samu waje su kwanta a nonon ba za su fita ba cikin sauki.”

Wannan wallafa da aka yi ranar Litinin 29 ga watan Agusta 2023 ta samu masu nuna sha’awa (likes) 121,000 da masu tsokaci (Comments) sama da 1,000 da wadanda suka yada (shares)4,000.

Yadda wannan bidiyo ya shahara da tunani neman wanin (Aure, Dove, Nivea, da sauransu.) na iya haifar da matsala fiye da maslaha wannan ya sa dole muka shiga bincike kan wannan batu.

Tantancewa

Deodorants an samar da su ne don su kawar da warin hammata da yawansu akwai sinadaran alcohol da turare da ke dakile wari. Idan aka shafa a hammata suna mayar da fata ta samu sinadarin acid wanda ke hana kwayoyin bacteria zama a waje.

Duk da cewa ba a fiya banbancewa ba tsakanin antiperspirants da deodorants, yayin da antiperspirants ke rage gumi shi kuma deodorants na kara yawan sinadarin acid ne na fata.

Hukumar kula da abinci da magunguna Food and Drug Administration (FDA) na kallon deodorants (a matsayin kayan kwalliya da aka tanada don tsafta da kawata jiki) shi kuwa antiperspirants (na a zaman kayan da aka tanada don kare cutittika da ka iya tasiri ga tsarin jiki da yadda yake aiki).

 Shin deodorants na kunshe da Aluminium?

Wata makala da Healthline ta fitar ta nunar da cewa deodorants baya kunshe da aluminium sabanin antiperspirants. 

Abu guda da ke kunshe da abubuwa biyu (Kayan da ke da wani sashi deodorant wani kuma antiperspirant) na kunshe da aluminium.

Kayan da ke kunshe da aluminium-antiperspirants na hana gumi fitowa ya shafi fata ta hanyar toshe mabubbugar yin gumin.

Shin aluminium da ke cikin antiperspirants na da alaka da cutar kansa ko daji?

Yayin da aka karkata kan batun idan fata na zukar aluminium zai iya shafar estrogen da ke cikin kwayar halittar nono, kwararru na the American Cancer Society sun bayyana cewa babu wata alaka ta zahiri tsakanin cutar kansa da aluminum da ke cikin antiperspirants don kwayar halittar da ke cikin kansar nono ba ta nuna cewa ita ke da rinjaye na sinaran aluminium ba, idan aka kwatanta da sauran sassa na jiki, bincike ya nuna cewa kadan ne na sinadarin na aluminium (0.0012 cikin dari) ake samu.

A shekarar 2017 wani bincike na kayan da ake amfani da su karkashin hammata  (UCPs) kan alakar kansar nono ya nunar da yiwuwar yawan amfani da UCPs da yawan aluminium a halittar ta nono da kansar mama.

Sai dai binciken bai gaza shakku ba, ma’ana ana iya samun taruwan sinadarin na aluminium a nono  ba tare da ingaza fargabar kamuwa da cutar ba.

Wani bincike da aka yi a 2018 kan alakar ta aluminium da ‘ya’yan halittar ta oestrogen kan batun na cutar kansa “ ya nunar da cewa idan aka samu sinadarin na aluminium da yawa na iya sauya yadda  oestrogen ke dabi’arsa a jikin mace. Yana da kyau a fahimci cewa tsarin kai komon ‘ya’yan halitta tsakanin sassa na jikin dan Adam na iya sauyawa bayan tsawon lokaci.

Cibiyar kula da cutar ta kansa ta Amurka ta ce duk da cewa binciken biyu sun nunar da yiwuwar alaka, wannan sakamakon bincike sai an yi taka tsantsan wajen bayaninsa saboda ba su da girma, don haka sai an yi bincike mai zurfin gaske.

Shin akwai alaka tsakanin aluminium da cutar mantuwa ?

Wani nazarin makaloli a 2016 kan yawan haduwa da aluminium da fargabar kamuwa da cutar mantuwa ya nunar da cewa idan ana haduwa da shi akai-akai mutum zai iya kamuwa da cutar da ke shafar kwakwalwa. 

Wani nazarin makalolin kuwa a 2018  “Circulatory Levels of Toxic Metals (Aluminum, Cadmium, Mercury, Lead) in Patients with Alzheimer’s Disease” da ya duba batun na aluminium da Cadmium da Mercury da Lead a marasa lafiya da ke da cutar da ta shafi kwakwalwa  ya nunar da cewa manya masu cutar akwai sinadaran a jikinsu, kuma hakan ba shi rasa nasaba da muhallin da suke zaune a cikinsa.

Ra’ayin Kwararru

Mun yi magana da kwararren likitan fata Ayo Aranmolate, wanda ya ce ba shi da masaniya kan binciken  kuma babu tabbaci na sahihancin sa. A martaninsa ya ce “Bani da masaniya kan wannan da’awa, babu tabbaci ko gaskiya ne.”

Mun kuma tuntubi  da wata masaniya kan fata  Shakirat Gold-Olufadi, sai  har zuwa lokacin fitar da rahoton ba a ji ta bakinta ba.

A karshe

Antiperspirants, ba  deodorants, shine yake kunshe da aluminium wanda ke da hadari ga mata, wasu binciken kuma sun nunar da alaka idan akwai yawan amfani da shi a kasan hammata . A karshe dai akwai bukatar a zurfafa bincike kan tasirin sinadarin aluminium ga hadarin kamuwa da cutar ta daji. Kazalika bincike kan alakar aluminium da ke cikin antiperspirant da cutar da kan shafi kwakwalwa ko haifar da mantawa shima bai kammala ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button