African LanguagesFact CheckHausa

GASKIYA! Onome Ebi ta kasance ta farko a  Afurka da ta je wasan kwallon kafa na duniya sau shida tana da shekaru 40

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi:  Fitacciyar ‘yarwasan Super Falcons Onome Ebi ta kasance ‘yar Afurka ta farko da ta je wasan kwallon duniya sau shida tana da shekaru 40.

<strong>GASKIYA! Onome Ebi ta kasance ta farko a  Afurka da ta je wasan kwallon kafa na duniya sau shida tana da shekaru 40</strong>

Sakamakon binciken: GASKIYA Fayyatattun bayanai sun nunar da cewa Onome Ebi ta kasance ‘yar Afurka ta farko da ta je wasan kwallon duniya sau shida tana da shekaru 40.

Cikakken bayani

Mai amfani da shafin Facebook Seraph Yomi ya yada labarin cewa ‘yar wasan kwallon kafa da ke tsayawa a baya tsakiya Onome Ebi ta kasance ‘yar Afurka ta farko da ta bayyana a wasan kwallon duniya sau shida tana da shekaru 40.

“At 40. Veteran #NGN defender Onome Ebi becomes the first African player – man and woman– to appear at the World Cup (s)ix times,” ya wallafa.

Wannan na zuwa ne ana tsaka da wasannin kwallon duniya na mata a Ostareliya da New Zealand wanda kasashe sama da 32 ke halarta ciki kuwa har da kungiyar kwallon kafa ta matan Najeriya Super Falcons, wacce aka fitar da ita a wasan a zagaye na 16 bayan fafatawa da England’s Lionesses ‘yanwasan mata na kasar Ingila aka ta shi hudu da daya.

Ebi wacce ke daura kambun Kaftin ta jagoranci sauran ‘yanwasan na Falcon, a wata hira da BBC ta fadi cewa samun dama da ta yi ta buga wasan mata na duniya har sau shida “ba ta taba tsammani ba.”

‘Yar wasan da ta yi shuhura ta fara bayyana a wasan duniya a 2003 lokacin tana da shekaru 20 sai kuma ta je ta buga wasannin a shekarun 2007 da 2011 da 2015 da 2019 da da 2023 bayan da Najeriya ta samu dama.

Irin wannan labari da aka wallafa ya dauki hankali tare da martani kala-kala, an nuna sha’awarsa (likes) sau 71,000 da tsokaci (comments)1500 da yadawa (shares) 435 ba kawai a wannan kafa ba.

A tsokaci da John Park yayi ya ce “ Aikin ki yayi kyau, Ina taya ki murna,” Shi kuwa Inemo Ikamo ya rubuta cewa “Tana da kima. Taki amincewa ta ba da shekarun karya.Ba ta kara shekara ko da guda ba shekarunta 40 ne. Allah Ya albarci gaskiyarki.”

Bayan da aka ga yadda wannan labari yayi shuhura DUBAWA ya ga ya dace yayi nazari kan wannan labari/da’awa.

Tantancewa

Mun shirya mu duba kasashen Afurka da suka je wasan duniya, mu kuma duba bangaren maza da mata.

Kasar Kamaru ta je sau takwas ‘yan wasa maza kenan da Najeriya da Maroko da Tunusiya sun je sau shida, Ghana ta je sau hudu.

Mun gano cewa Roger Miller shine dan wasa mafi yawan shekaru daga Kamaru da yaje irin wannan wasa ya kammala da shekaru 42 ya buga sau uku  sai Mohammed Lawal na Najeriya da yayi ritaya a shekaru 42 shi ake alakantawa da wasannin maza na Olympic na 1968.

Jalili Fadili dan Maroko  ya yi ritaya daga buga wasan kasa da kasa yana da shekaru 47 a wasan da aka yi na duniya 1970.Haj Hannachi  ya bugawa Tunisia wasan karshe yana da shekaru 57 ya buga wasannin sada zumunta tsakanin kasa da kasa biyu da wasannin kasashen Afurka CAF sau daya.

Amma a bangaren mata ‘yan Najeriyar ta sha gaban takwarorinta nata na Afurka da suka tsallaka zuwa wasan duniya ta shiga wasannin sau tara ta sha gaban Ghana da wasanni uku da inda ta je sau uku ita kuwa Kamaru ta je ne sau biyu

Duk da rashin kididdigar bayanan shekarun matan da ke takawa Najeriya kwallo wani bincike daga majiya mai tushe kamar ta CNN da Punch da Daily Sport sun nunar da cewa Ebi ita ce kadai mace da ta ciri tuta tsakanin takwarorinta mata ta shiga wasan kwallon duniya sau shida tana da shekaru 40.  

Kafar yada labaran BBC ma ta rawaito cewa Ebi tana daga cikin mutane biyar da suka je wasan kwallon duniya sau shida Ebi (40), Christine Sinclair ‘yar Kanada tana da shekaru (40), ‘yar Brazil Marta Vieira da Silva (37) sun shiga wasannin da aka yi na duniya a Australia da New Zealand ga kuma Homare Sawa (37) ta wakilci Japan a 2015 sau shida kuma na karshe.

A wani labarin kuwa zakarar kwallon kafar nan ta Brazil Miraildes Motada aka fi sani da suna (Formiga) ta buga wasan duniya sau bakwai tsakanin 1995 zuwa 2019 kafin ta ajiye takalmin kwallonta tana da shekaru 43.

A karshe Hukumar FIFA da ke shirya wasannin na duniya ta wallafa a shafinta na Intanet kan batun na Ebi cewa ita ce ‘yar wasa daya tilo daga Nahiyar Afurka da ta yi wasan kwallon duniya sau shida idan ta bayyana a shekarar ta bana.

A Karshe

Labarin da aka wallafa gaskiya ne ta tabbata a mataki na gida dama tsakanin kasa da kasa cewa Ebi ita ta taka kwallo a wasan kwallon duniya sau shida wacce kuma ta kasance ‘yar wasan Afurka ta farko da ta taba yin haka.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button