African LanguagesFacebook ChecksFact CheckHausa

A’a! Facebook ne ke cewa a saka lambobin sirri a shafin tura sakonni na Messenger ba Masu Kutse ba.

Da’awa: Masu kutse na cewa a saka lambobin sirri domin bada tsaro a manhajar tura sakonni ta Messenger, kuma duk wanda ya sa za a yi masa kutse a shafin sa.

Hukunci: Ba Gaskiya Ne Ba! Bincike ya nuna cewa sakon daga Facebook ya fito kuma saka lambobin zai kara bada tsaro ga sakonnin mutum.

Cikakken Bayani

Wasu bayanai da suka karade shafukan sada zumunta musamman Facebook sun nuna cewa, a ‘yan kwanakinnan ana turawa mutane sakonni a shafin su na sada zumunta na Facebook da ke cewa su saka lambobin tsaro a shafin su, sai dai wasu na zargin cewa masu kutse ne suka yi hakan.

Bayanin dai an fara yaɗa shi ne a ranar 25 ga watan Maris, 2024, kuma mutane da dama ne suka yaɗa shi. 

Ɗaya daga cikin bayanin wanda Aminu Mukhtar Balarabe ya wallafa, an danna masa alamar so (like) sau 36, anyi sharhi (comment) sau 20, yayi da aka yada shi (share) sau 8.

Dalilin da suka bayar kuwa shi ne, da zarar mutum ya saka lambobin za a rika tura hotunan batsa a shafin sa ba tare da ya sani ba wanda mabiyansa ne za su gani.

shi (share) sau 8.

Dalilin da suka bayar kuwa shi ne, da zarar mutum ya saka lambobin za a rika tura hotunan batsa a shafin sa ba tare da ya sani ba wanda mabiyansa ne za su gani.

A cikin sakonnin da masu amfani da shafin suka rika wallafawa, suna yin gargadi ne tare da sanar da abokannin su cewa sun saka wadannan lambobi kuma basu san abinda zai iya faruwa ba, saboda haka kar a zarge su idan aka ga wadannan sakonnin na batsa sun bayyana a shafin su.

Wasu sakonnin da aka rika wallafawa

Akan wannan ne, Dubawa ta bincika domin duba gaskiyar lamarin, kasancewar al’umma da dama sun shiga fargabar za’a bata musu suna ko su rasa shafin su na sada zumunta da kasuwanci a hannun masu kutse.

Tantancewa

 Mun yi kokarin saka wadannan lambobin sirri a wani shafi na musamman da muka kirkira na Facebook domin ganin ko masu kutsen zasu kwace shi, sai dai kwana uku da saka lambobin babu abinda ya faru da shafin.

Ci gaban binciken ya nuna cewa wannan sakon daga Facebook ya samu asali ba daga wasu masu kutse ba, kamar yadda muka zakulo bayanin da aka dora akan cibiyar agaji ta Facebook, sashen da duk wani bayani dake da alaka da shafin Facebook da na Messenger, da yadda ake amfani dasu yake kai.

Rubutun da muka tsakuro a shafin na agaji

Abinda wannan ke nufi shi ne: tsarin na saka lambobin sirri a Messenger an kawo shi ne domin dalilai na tsaro da kuma baiwa masu amfani da manhajar damar da zasu iya dora bayanan su a wata wayar ba tare da sun rasa sakonnin da suka tura a baya ba, idan suka saka bayanan su a wata wayar za a bukaci su saka lambobin na sirri domin sakonnin su sake dawowa, kasancewar Facebook zasu ajiye bayanan ne a cikin rumbun ajiya.

Wannan tsarin saka lambobin sirri domin bada tsaro an kaddamar da shi ne tun a karshen shekara ta 2023, sai yana kaiwa ne daya bayan daya ga masu amfani da dandalin na Facebook a kasashen duniya.

Me kwararru ke cewa?

Dr. Salisu Abdulrazak Saheel masani tsaron na’ura mai kwakwalwa ne a Najeriya kuma yayi mana bayanin cewa, wannan tsarin yunkuri ne da Facebook ya yi domin ganin cewa wadanda suke amfani da Messenger bayanan su basu fada hannun masu kutse ba, ko da kuma an yi musu kutse a ainahin shafin su na Facebook.

“Bai zama lallai a samu shiga a cikin sakonnin sirri da mutum yake turawa abokan huldarsa ba, kuma zaka iya hawa kan Messenger ka sanar da abokanin ka cewa anyi maka kutse a shafin ka” a cewar sa.

Dr. Saheel ya kara da cewa, “duk wadanda ke cewa idan sun sa wadannan lambobi ana yin kutse a shafin su, to su sani ba haka bane kuma su bincika wayar da suke amfani da ita, ta yiwu sun hada shafin nsasu da wata manhaja mai hadari ba tare da saninsu ba ko kuma cikin sani” 

“Wannan sakon daga Facebook ya fito saboda haka ba yadda za a iya kutse ta wannan hanyar sai dai ya danganta idan mutum mai shige-shigen wurare masu hatsari ne” inji shi.

A Karshe

Da’awar cewa masu kutse na cewa a saka lambobin sirri domin tsaro a manhajar tura sakonni ta Messenger, kuma duk wanda ya sa za a yi masa kutse a shafin sa Karya Ce! Bincike ya nuna cewa sakon daga Facebook ne kuma saka lambobin zai kara bada tsaro ga shafin mutum.

An yi wannan binciken ne karkashin shirin Binciken Gaskiya na DUBAWA wato Indeginous Language Fact-Checking 2024, tare da hadin gwiwar Vision 92.5FM, Sokoto, domin dabbaka labarun “gaskiya” a cikin aikin jarida da karfafa ilimin yada labarai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button