Getting your Trinity Audio player ready...
|
Dogo Gide, sannane a fagen ta’addanci da garkuwa da mutane ana zargin yana da hannu a yin garkuwa da daliban nan 137 da aka dauke su daga wata makarantar firamare a jihar Kaduna, an dai samu rahotanni da ke nuna cewa an kashe shi a wani bata kashi da aka yi tsakanin ‘yanbindigar da dakarun tsaro a Najeriya.
Amma rahotanni sun nunar da cewa an samu yanayi na rudani a tsakanin sojoji da ke yaki da masu tada kayar baya da jami’an tsaron ciki da kwararru dama wadanda ke kusa da danta’addar, PREMIUM TIMES ta fitar da rahoto
An samu rahoto da ya nunar da cewa dakarun Operation Hadarin Daji (OPHD) sun raunata Mista Gide a dajin Madada da ke yankin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara a ranar 12 ga watan Maris kwanaki biyar bayan yin garkuwa da dalibai 137 a makarantar firamare da sakandaren Kuriga.
A cewar wasu rahotanni dan ta’addar daga bisani an dauke shi inda aka kai shi wani asibiti a jihar Sokoto inda anan ne ya mutu.
“Ku tashi da farin ciki na samun labarin cewar Dogo Gide ya mutu.” Wannan shine abin da tsohon mai taimakawa tsohon shugaban Najeriya kan harkokin yada labarai a zamanance Bashir Ahmad ya wallafa ( posted ) a shafinmsa na X.”Jagoran ‘yanta’addar ya mutu ne biyo bayan raunuka da ya samu a wata taho mu gama da dakarun Operation Hadarin Daji (OPHD)”
Imran Muhammed, shima fitaccen mai amfani da shafin na X wanda ke da mabiya sama da 124,000 shima ya yada wannan labari. “Duk da irin rauni da ya samu, mun samu labarin cewa Dogo Gide an dauke shi zuwa wani asibiti a Mabera da ke jihar Sokoto inda anan ne yace ga garinku nan.”Wannan shine abin da Muhammed ya wallafa (posted) inda yayi da’awar cewa jami’in tsaron da ya yayi wa danta’addar rakiya an kama ko tsare shi.
Sai dai wannan ba shi ne karon farko ba da aka samu rahoton cewa Mista Gide ya garzaya barzahu.
A shekarar 2021, an samu jita-jitar cewa na kusa da shi Sani Makama ya kashe shi, sai dai daga bisani masu sharhi sun nunar da cewa wannan farfaganda ce ta sojoji.
Da gaske ne ya mutu?
Bayan da aka samu labarin da ke cewa fitaccen dan ta’addar an kashe shi, wani hoto na wani mutum mai dan yanayin kama da shi ya karade shafukan sada zumunta kamar a nan (here, here da here.)
Bayan da aka yi amfani da hanyar gano asalin hoto ta Google Lens kafar yada labarai ta PREMIUM TIMES ta gano cewa wannan hoto na bogi ne kuma ma tsabar yaudara ce.
Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Abdallah Habeeb, ya bayyana cewa mutumin da aka nuna a hoton, sunansa Dan Asabe kuma dan asalin garin Kaduna ne wanda ya mutu a jihar Legas makonni biyu da suka wuce.
Wani hoto kenan da ya nuna mutum da ya so kama da Mista Gide da aka yada hotonsa a shafukan sada zumunta don a gaskata jita-jitar mutuwar Gide
“Dan Allah, kafin mu yada labari mu tabbatar da ingancinsa, na ga ana ta yada wannan hoto da sunan DOGO GIDE, ina fatan duk wadanda suka gani za su yi watsi da wannan labarim wannan ba DOGO GIDE bane sunansa Dan Asabe da aka fi sani da Sabebe,” Haka Mista Habeeb ya wallafa (posted) a Facebook.
“Dan asalin yankin Tudun Nupawa ne a nan Kaduna,” ya kara da cewa “ Dan kasuwancoin jari bola ne a Legas kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Lambu United… ya samu hadari ne a iyakar Seme wato Seme Border kusan makonni biyu da suka gabata.”
Duk da haka an ci gaba da samun labaran mutuwar ta Mista Gide mabanbanta, kamar yadda aka ji a tattaunawa da ka yi da mutane daban-daban da suka hadar da dakarun soja da kwararru kan yaki da ta’addanci da jami’an tsaro na ciki da mutanen da suka san halayya da irin ayyukan dan ta’addar a jihohin Zamfara da Kebbi da Niger.
Wata majiya ta jami’an tsaro da ke nazartar ayyukan ta’addanci a yankin Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamafara inda anan ne dan ta’addar ke da sansanoni musamman a dajikan Babandoka da Dan Gurgu da Kuyambana ta nunar da cewa jagoran ‘yanta’addar ya rasu a ranar Alhamis da ta gabata makonni biyu bayan bata-kashi da dakarun sojan Najeriya ana tsaka da yin garkuwa da daliban nan na Kuriga.
“Dogo Gide ya samu raunuka bayan fafatawa da sojan Najeriya,” wani da bai so a bayyana sunansa ba ya fada wa PREMIUM TIMES, cewa dakarun sun kuma kashe wasu na kusa da danta’addar. Ya kara da cewa wani da ke ba shi bayani a yankin ya fada masa cewa jagoran ‘yan ta’addar an dauke shi a kan mashin zuwa kauyen Kizara don neman kulawar lafiya.
“Amma sun fada mana cewa ya rasu a daren ranar Alhamis da ta gabata, mun kuma sanar da jami’an tsaro kamar ‘yansanda da sojoji da DSS, ” ya kara da cewa yayi mamaki yadda ya rika ganin wani sabon labari da aka jirkita yana kuma yawo mako guda daga baya.
“Cewa ya mutu a Sokoto kamar yadda wasu mutane ke cewa wannan babbar karya ce.” Ya jaddada cewa “Dogo Gide ya rasu ne a Zamfara.”
Sai dai babu wata sheda da ya bayyana wacce ta tabbatar da da’awarsa.
Wasu da ke kusa da Mista Gide a jihohin Kebbi da Zamfara suma sun ba da labarai mabanbanta, ko da dai suma sun ce ya samu raunuka sakamakon harbin da aka yi masa a lokacin fafatawa da jami’an tsaron sa’oi kadan bayan kama daliban Kuriga.
PREMIUM TIMES ta gano cewa wadanda suka yi garkuwa da daliban Kuriga sun fuskanci kalubale sosai don sojojin sun fi karfinsu don haka sai suka nemi Mista Gide ya kawo masu dauki.
“A lokacin kawo masu daukin ne ya samu raunika, yaransa da dama suka mutu.” Wani da ke kusa da wadannan ‘yanta’adda ya fada wa wannan jarida haka, inda ya nemi a boye sunansa don gudun kada ‘yan ta’addar su afka masa.
Amma wani da ke kusa da Mista Gide wanda a lokuta da dama ya shiga tsakanin sa da wadanda aka yi garkuwa da ‘yanuwansu ya jaddada cewa Mista Gide yana nan a raye.
Haka kuma wasu da dama suna fuskantar kalubale na bayyana halin da Mista Gide yake ciki, ciki kuwa har da jami’an soja.
Lokacin da wannan jarida ta nemi ji daga jami’in hulda da jama’a na dakarun na Operation Hadarin Daji a Zamfara, Suleiman Omale wanda ke da mukamin lutanal a sojan Najeriya ya fadawa wannan kafa cewa jami’ansu na ci gaba da bincike kan wannan rahoto.
Ya ce “sakamakon da muka samu”za a sanar da jama’a,
Shima kwararren masani kan harkar tsaro Yahuza Getso da ke bibiyar ayyukan wannan dan ta’adda da mabiyansa shima ya bayyana nasa ra’ayi da ke zama irin wannan.
Mista Getso da ke zama manajan darakta na kamfanin samar da tsaro na Eagle Integrated Security and Logistics Company da ke Abuja yace “A wannan yanayi da ake ciki ba za a tabbatar da sahihancin rahoton mutuwar ba, hoton da aka yi amfani da shi don tabbatar da labarin mutuwar Mista Gide na karya ne.”
Mista Gide a cewar kwararren masanin na tsaro “tabbas zai mutu” ko dai mutuwa daga Allah ko dakaru su halaka shi ko kuma daga bangaren wadanda yake jagoranta a harkar ta’addancin su halaka shi kamar yadda yayi wa shugabansa Buharin Daji a 2018 kafin shima ya samu tasa daukakar a ayyukan rashin imani.
”Wasu watanni da suka wuce Dogo Gide ya samu raunika ya fice daga kasar inda ya je yayi jinya.” haka Mista Getso ya fada wa PREMIUM TIMES, ba tare da ya bayyana wace kasa ce dan ta’addar yaje ba.
A watan Janairu, PREMIUM TIMES ta ba da rahoto kan yadda aka wargaza sansanin Gide bayan wata taho mu gama da aka yi tsakanin dakarunsa da ‘yan ta’addar Ansaru a Zamfara.
Dogo Gide: Dan ta’adda mai hadari wanda ke da alaka da kungiyoyi irin nasa
Mista Gide, wanda wadanda suka san shi sun ce asalin sunansa shine Abubakar Abdullahi. Dan asalin yankin Shiroro ne a jihar Niger, an haife shi a Palali a kusa da Chukuba yankin da kungiyarsa ta yi ikirarin cewa ta harbo jirgin sojan sama a wajen a shekarar bara.
Dan ta’addar kamar yadda bayanan kwararru suke nunawa dana jami’an tsaro shine cewa dan ta’addar na da alaka da kungiyoyin ta’addanci irinsu Ansaru da mayakan (ISWAP).
Mista Gide shike da hannu a hare-hare da aka kai a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Ya kasance kan gaba a wadanda ake zargi da kitsa harin da aka kai a ranar 28 ga watan Maris, 2022 kan jirgin kasa da ke jigila tsakanin Abuja da Kaduna.
A watan Yuli 2021 dan ta’addar da abokinsa Kachalla Ali da aka fi sani da Ali Kawaje sun kama sama da dalibai 100 da malamai takwas a Federal Government College (FGC) a Birnin Yauri, jihar Kebbi. Daga baya an rika sakin wadanda aka yi garkuwar da su daki-daki bayan sun biya kudin fansa.
Wata shekarar da ta zago sun sake kama wasu mutane uku kwararru daga kasar Sin da masu gadinsu biyu sai wani dan kasar ta Sin da aka kama a wajen aikin ginin Dam na Zungeru Hydro-electric Power Dam project a karamar hukumar Shiroro. Duk da cewa ba a samu cikakkun bayanai ba kan yadda aka saki kwararrun guda biyu daya daga cikinsu an sako shi daga sansanin Mista Gide daga baya.
Masanin tsaro wanda ke nazartar yadda ake ayyukan ta’addanci a arewacin Najeriya Murtala Ahmed Rufa’i ya wallafa a litatafinsa mai suna ‘I am a Bandit’ cewa Mista Gide na da kudade sannan yana da alaka da mutane yadda zai iya samo manyan kayan yaki. Yace “Dukkanin wadannan Gide da sauransu sun mallaki bundoiga kirar AK 47 sama da 500 ko bindigogi kirar AK 49, Wasu daga cikinsu kamar Gide da Mai Unguwa da Turji suna da manyan makamai irinsu RPGGS da bindigar kakkabo jiragen sama,” kamar yadda Mista Ahmed ya rubuta.
“Dogo Gide daga bisani yayi mubayi’a ga kungiyar Boko Haram a watanni hudun karshe na 2019. Wannan ya sanya daga sansaninsa a dajin Wawa a jihar Niger ya rika daukar mambobi karkashinsa sannan ya tabbatar da fadada yawan sansanoninsa zuwa 104 a Zamfara,”kamar yadda Mr. Ahmed Rufa’i malami a tsangayar koyar da ilimin tarihi a Jami’ar Usman Danfodiyo Sokoto ya rubuta anan ma.
Ayyukan ta’addanci na Mista Gide ya bar miki a zukatan iyalai da dama wadanda suka rasa masoyansu da kudadensu saboda ayyukansa na rashin imani da tausayi da ta’addanci a jihohin Niger da Zamafara da Kebbi da Kaduna.