African LanguagesHausa

Abin da ya kamata a sani game da ganin “bakuwar” tuta lokacin da Tinubu ke jawabi ga ‘yan kasa

Getting your Trinity Audio player ready...

Tutoci da ake gani suna kadawa a cikin iska ba kawai yadi ba ne kowane iri; alama ce ta mulki da tarihi da kimar kasa ko wata hukuma ko wata al’umma a ko’ina a duniya. Launika da zane da ake gani a jikinsu kowanne na da manufarsa, tuta na ba da labarin hadin kai da alfahari da al’ada.

Haka nan ma abin da za a ce kenan kan tutar da aka yi ta cece-kuce akanta a kafafan sada zumunta. A ranar daya ga watan Agusta 2024, ‘yan Najeriya sun fita zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa karkashin mulkin Shugaba Tinubu, ana tsaka da wannan zanga-zanga sai ga wasu a jihar Kano (Kano State protesters were spotted) an gano su suna daga wata tuta mai kama da ta kasar Rasha. 

Wannan lamari ya ja hankali sosai tsakanin ‘yan Najeriya, haka nan ya jawo tambayar ko kasar Rasha na da aniya na kutsa kai kan zanga-zangar kamar yadda aka yi zargin gwamnatin ta Putin a zanga-zangar Jamhuriyar Nijar (Vladimir Putin’s alleged involvement), haka kuma irin wannan tuta ko me kama da ita aka gani a kusa da shugaban kasar ta Najeriya a lokacin da yake gabatar da jawabi ga ‘yankasar a ranar Lahadi 4 ga Agusta,2024, wannan ya kara tada wani rudanin inda ‘yan Najeriya ke tambayar shin ita kuma wannan tutar daga ina? “Yan Najeriya wannan tuta me take nufi?” 

Da dama kamar  Kayode Ogundamisi, ya kammala zancensa da cewa wannan tuta da aka gani a Kano iri daya ce da “tutar kasar Rasha” da kuma ke a gefen shugaban kasa.

A rubutun da yayi a shafin na Twitter (his tweet) Mista Ogundamisi ya rubuta cewa, “ abin da ake tsammani mu ci gaba da tattaunawa a kai a shafukan sada zumunta shine batun konanniyar ayaba ko agada. Yayi nuni da tutar da ke bayan shugaban kasa wacce ke iri guda da Tutar Rasha.”

What you should know about the “strange” flag spotted in Tinubu's broadcast

Najeriya An shiga rudani kan wannan tuta ta bayan Mista Tinubu

Rashin ba da bayanai masu inganci na iya kawo rashin yarda daga al’umma ko wasu hukumomi abin da ka iya haifar da rade-radi  sannan ya janye hankula daga muhimman batutuwa a lokacin zanga-zangar da ma lokutan wasu abubuwa da suka shafi kasa. Wannan makala ta yi kokarin warware wannan matsala ta rudani.

Wace tuta ce masu zanga-zangar suka daga a Kano?

Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta #EndBadGovernance  ta rikide da zama tarzoma. Kamar yadda aka gani a rahotanni, ‘yandaba sun karbe ta da sace-sacen kayan gwamnati da na daidaikun jama’a, dalilin da ya tilasta gwamnati ta dauki matakin sanya dokar hana fita ga al’umma tsawon sa’oi 24 ( impose a 24-hour curfew).

 Ana tsaka da wadannan abubuwa sai  Instablog9ja wani mai shafin blog a intanet ya rika yada wasu hotuna kala-kala (shared multiple images)  wadanda ke dauke da masu zanga-zangar suna kada tutoci masu launin fari da shudi da ja  yayin da wasu suka rika daga hotunan Mista Putin, daga cikinsu akwai wanda DUBAWA ta yi nazarinsa an kuma gano an wallafa shi tun a ranar  1, Maris 2023  yayin wata zanga-zanga a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango (DRC) inda aka yi zargin hannun Mista Putin, duk da haka bamu kai ga tabbatar da cewa sauran an daga su a jihar ta Kano ne ba, kamar yadda aka nunar.

Wasu sun ce tutar da masu zanga-zangar suka daga ta gidan sarautar Kano ce. DUBAWA ya tabbatar da cewa wannan karya ce saboda tutar Kano na dauke ne da launin ja da dorawa da shudi da kuma farin tauraro. A takaice dai tutar da masu zanga-zangar suka daga tayi kama da ta Rasha.

What you should know about the “strange” flag spotted in Tinubu's broadcast

Duba banbanci da ke akwai tsakanin tutar Rasha da ta masarautar Kano

Duk da cewa tutar da ke kusa da shugaban, lokacin da yake jawabi ta so kama amma sun banbanta, sabanin tutar Rasha tana da launika ja da shudi da fari da kore a jere, duk da cewa ba a ga koren ba, hakan ya faru ne saboda yadda aka sanya kamera daukar hoton.

Tinubu a matsayin jagora na shugabannin sojojin kasar

 A lokacin da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, tutar da ke gefensa ta bayyana wanan matsayi da karfin iko da yake da shi.

What you should know about the “strange” flag spotted in Tinubu's broadcast

Tutar shugaban kasa a matsayin jagora na shugabannin sojoji a Najeriya

A matsayin shugaban sojojin Najeriya haka al’adar take a rika ganin tutar ta sojoji da ta Najeriya a jera su a gefen shugaba ko a bayansa, duk lokacin da zai wani abu a hukumance. Anan ga Shugaba Tinubu da wasu shugabanni da suka gabace shi da wannan tuta da ke nuna matsayinsu biyu kamar yadda zaa gani a kasa.

What you should know about the “strange” flag spotted in Tinubu's broadcast

What you should know about the “strange” flag spotted in Tinubu's broadcast

Mista Tinubu lokacin da yake jawabi a ranar Dimukuradiyya a 2024

What you should know about the “strange” flag spotted in Tinubu's broadcast

Muhammadu Buhari lokacin da yake ban kwana da ‘yankasa a 2023

What you should know about the “strange” flag spotted in Tinubu's broadcast

Goodluck Jonathan lokacin da yake jawabi ga ‘yan kasa a ranar Dimukuradiyya 2010

Ta dai tabbata cewa tutar da aka gani lokacin da shugaban kasa ke jawabi ta banbanta da tutar da aka gani ta yadu lokacin zanga-zangar a Kano, DUBAWA bai gano wata hujja ba da ke nuna cewa Rasha na da wata alaka da zanga-zangar ko wani shiri kan zanga-zangar tsadar rayuwar ta #EndBadGovernance kamar yadda ake zargi.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button