African LanguagesHausa

Yaudara ce! Hoton sojoji da aka kashe da ya yadu ba sojojin Najeriya ba ne

Getting your Trinity Audio player ready...

    Da’awa: Simon Ekpa ya wallafa a shafin Twitter wani hoto (an image) wanda ke nuna cewa wasu dakarun sojan Najeriya ne da ‘yan Biafra suka kashe.

    Yaudara ce! Hoton sojoji da aka kashe da ya yadu ba sojojin Najeriya ba ne

    Hukunci: Hotan na Mista Ekpa ba shi da wata alaka da dakarun sojan Najeriya, kuma abin da ake fadi a kai yaudara ce.

    Cikakken Sako

    A ranar 25 ga watan Yuli, 2024 Simon Ekpa dan fafutukar samun ‘yancin Biafra ya wallafa wani hoto da ke nuna wasu hotuna (posted two images) a shafin X tare da nuna alamar dariya cewa wannan hoto na wasu jami’an tsaron Najeriya ne uku da aka kashe cikin kayan soja a daji, yayin da daya hoton ya nuna rabin wasu’ya’yan itacen mangoro da aka sha aka yar.

    Wannan hoto ya yadu sosai mutane na ta sharshi kan gawarwakin da aka ce na dakarun sojan Najeriya ne da aka kashe yayin kai farmaki na masu fafutukar samar da yankin Biafra wato ‘yan IPOB.

     Ga misali @MidBrgie wani mai amfani da shafin yayi zolaya ga gawarwakin sojojin (mocked the deceased) yana mai cewa  “ ‘yanta’adda daga gidan zoo na dakarun sojan Najeriya sun fita shan mangoro sai suka yi bacci.”

    Wadannan kalmomi na gidan namun daji Zoo da ‘yanta’adda sune kalmomi da ‘yan IPOB ke amfani da su suke fassara Najeriya da sojojinta.

    Wani da ke jaddada labarin na “ Yaki a gidan Biafra” mai amfanin da shafin na X another user said yace an kashe sojoji lokacin da suke “lalata kasar Biafra”suna kashe mata da yara. 

    “Kun ga yadda aka kai su kasarmu su kashe mata da yara su kone gidaje da shaguna su kashe wanda suke so, amma dakarun na BLA/BDF sun kawar da wannan barazana.” abin da ya rubuta kenan a wallafar da yayi.

    Saboda saninsa da aka yi wajen tada hankali a yankin Kudu maso Gabashi dama kakaba wa al’umma dokar zama a gida mutumin da ke zaune a Finland Mista Ekpa a watan Maris na 2024 rundunar sojan Najeriya ta bayyana nemansa ruwa a jallo (declared wanted). Tsawon shekaru DUBAWA ya sha fallasa da’awar da yake a shafukan sada zumunta.

    Saboda kalaman harzuka jama’a da irin yadda yake yada bayanansa da sanin Mista Ekpa sai muka ga dacewar gudanar da bincike kan wannan da’awa ta hotuna da ya yada.

    Tantancewa

     Da aka yi amfani da dabarun gano asalin hoto an ga yadda wannan  hoto  ya bayyana a gumurzun da aka yi tsakanin dakarun soja da ‘yanta’adda a yankin Savanes da ke arewacin Togo.

    Kamar yadda mujallar  Journal Du Togo, ta ba da rahoto (reported), wadannan ‘yanta’adda sun kaddamar da hari a ranar 20 ga watan Yuli, 2024 inda suka kashe dakarun kasar Togo 12, da raunata wasu da dama sannan suka “dauke da lalata kayan sojoji da makamansu.”

     A wannan gumurzu dakarun kasar ta Togo sun hallaka maharan 40.

    A Karshe

    Hoton da Mista Ekpa ya wallafa ba shi da wata alaka da Najeriya ko sojojinta, kuma labarin da ake dangantawa da su yaudara ce.

    Show More

    Related Articles

    Leave a Reply

    Back to top button