Getting your Trinity Audio player ready...
|
A cikin watan Disemban 2024, Asusun Kula da Ilimi da Kimiya da Al’adu na Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ya sanya Hawan Sallah ko Daba cikin manyan ababen tarihi na kasar Hausa saboda muhimmanci da wannan al’adar ke da ita a yankin da ke da akasari Hausawa mabiya addinin Islama. A cikin wannan gudunmawar, Yusuf Bala Nayaya ya yi mana nazarin wannan al’adar da ma irin kimar da take kara wa kasar Hausa
Hawan Sallah wanda daga baya ake kiransa da sunan Hawan Daba al’ada ce mai dadadden tarihi a kasar Hausa tun kafin zuwan Shehu Usman Danfodiyo, ma’ana tun kafin Jihadin Shehu Usman Danfodiyo zuwa kasar Hausa.
Yadda sarki ke fita Hawan Daba: Hoto daga Culture Nigeria
Wannan hawan Daba ana yinsa a kasar Hausa tun a karni na 15, akasari sau biyu a shekara a lokacin Sallah Karama wato Eid al-Fitr da Sallah Babba Eid al-Adha wato wata na 10 da na 12 a kalandar Musulinci, a wasu yankunan a lokutan Mauludi kamar a kasar Gumel da ke jihar Jigawa a yanzu, inda za ka ga dubban mahaya dawaki da masu bushe-bushe da kade-kade da mafarauta da ‘yan lufudi da ‘yan tauri ko mafarauta da masu kwari da baka da sauransu suna rakiya ga sarki lokacin da yake zagayawa a titunan biranen da suke kamar na Kano ga misali, yana gaisuwa da dubban al’ummar Kanawa da suka fito don yin gaisuwar sallah ga sarki.
DALILAN HAWAN DABA A KASAR HAUSA
Makasudin Hawan shi ne domin Sarakuna su zagaya su sadu da talakawansu su yi wa juna hoho a yi wa Allah S.W.T godiya ko dai don an shekara lafiya bayan kammala ibadar Azumi ko lokacin Sallah Babba wato bayan Mahajjata wadanda suka je aikin Hajji a kasar Saudiyya sun dawo daga Makka wadanda suka je aikin Hajji.
Wannan ya na da kokarin sada zumunci da kuma karfafa kauna tsakanin shugabanni da talakawansu, ana kuma amfani da wannan dama dan jama’a a gwangwaje su da irin bukukuwa na al’adun gargajiya da ke karfafa zukata, domin a irin wannan lokaci ne ma sarakuna ke kara nunawa talakawansu irin tanadin da suke da shi na kayan yaki don kare mutuncin al’ummarsu, saboda kowace tawaga ta na tahowa a shiri na yaki.
Haka nan kuma masu hawan sukan yi shiga cikin tsari na kyautata irin kayayyaki da ake yi na saka da jima da rini da sauransu, domin dawaki da su kansu mahayan dawakan kan sako kayayyaki masu ban sha’awa abin da ke kara zaburar da masu yin wadannan kayayyaki cewa abin da suke yi akwai kasuwarsa.

Yanayin mahaya da kwalliyarsu a lokacin hawan Daba a Kano: Wanda ya dauki hoto: Yusuf Nayaya: DUBAWA
AMFANIN HAWAN DABA GA CI GABAN TATTALIN ARZIKIN HAUSAWA
Daba na da amfani ga rayuwar al’umma musamman bayan lokacin da Turawa suka zo don ziyarce-ziyarce kasancewar ana samun baki daga sassa daban-daban na duniya wandanda sukan zo ziyartar kasashen na Hausa musamman jihar Kano.

Farfesa Tijjani Muhammad Naniya, masanin tarihi a Jami’ar Bayero Kano: Hoto daga jaridar Punch
A cewar masanin Tarihi a Jami’ar Bayero da ke jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Farfesa Tijjani Muhammad Naniya “A irin wannan lokaci bakin da suka zo suna kwashe kwanaki, kai wasu ma su yi kusan wata guda su ziyarci wurare da kasuwanni na gargajiya irinsu kasuwar Kurmi mai dinbin tarihi inda suke siyan kayayyaki a wurin Kanawa abin da ke sama masu da kudaden shiga, su kan je wurin Majema masu sana’ar jimar fata da Masaka masu saka tufafi da kayayyaki da Marina masu yin rini da Makera, don su Turawan irin wadannan kayayyaki na gargajiya su suka fi siya, don haka masu irin wadannan sana’oi a lokacin suke baje hajarsu, abin da ke bunkasa al’adunmu da tattalin arzikin al’ummarmu.” A cewar masanin Tarihin Naniya.

Wani mai aikin rini a Majemar Kofar Mata Kano, irin kayan da Turawa ke siya, Wanda ya dauki hoto: Yusuf Nayaya: DUBAWA
Wannan gani da ido da Turawan kan yi a lokacin da suka ziyarci Kano a lokutan Daba na nuna masu cewa al’ummar jihar na da kwarewa wajen yin sana’aoinsu kala-kala kamar yadda aka bayyana a baya, tun kafin ma zuwan Turawa kasar Hausa wanda har yanzu an ci gaba da irin wadannan sana’oi don har yanzu a lokuta irin na Daba irin bakin da ke zuwa har kawo yanzu suna zuwa siyan irin wadannan kayayyaki kasuwarsu bata mutuba. A cewar Farfesa Naniya.
KALUBALEN SIYASA A HARKOKIN MASARAUTU YA RAGE TASIRIN DABA
Daba a kasar Hausa musamman a jihar Kano ta samu koma baya dalilin shigowar harkokin siyasa dumu-dumu a cewar masanan tarihi kamar su Farfesa Tijjani Muhammad Naniya. “Babban kalubalen Daba a yanzu shine shigar siyasa kan sha’anin harkokin masarautu, ya kawo rarrabuwar kawuna ana rarraba masarautu, ana dukusar da su, babu yadda za ka samu Daba a wata murabba’in masarauta da aka kirkiro ta ba dalilin tarihi ba, da ba ta fi mutane dubu 200,000 ba ko 300,000 kuma ace an bata masarauta, to me za a yi Daba a nan wajen? Ai ita Daba shi yasa ta Kano tafi armashi domin kasar Kano babbar kasa ce kuma mai arziki don shi sarki zai kira dukkanin hakimai daga kananan hukumomi 44, sanda kuma ana tsohuwar Kano har ma da sauran masarautu irinsu na Gumel da Hadeja da Kazaure suna zuwa domin ana zuwa biki ne na duk kasa. To amma raba Kano gida biyu ya rage mata armashu saboda sarakunan suna zama ne a can.”
Masanin Farfesa Naniya ya kara da cewa ko da aka raba Kano aka fitar da jihar ta Jigawa wacce ke da masarautun na Gumel da Hadeja da Kazaure armashin Daba a Kano ya dan ragu kadan suna can amma duk da haka dai ya ci gaba da wanzuwa da armashi kasancewar tana da kananan hukumomi 44 kafin daga baya-bayan nan lokacin gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje aka rarraba masarautar ta Kano zuwa masarautu biyar wato masarautar Kano da Karaye da Bichi da Gaya da Rano abin da a cewar masanin na da illa ga makomar masarautun. “Kokarin da ake yi na kakkasara masarautun a rika kirkiro kanana dalili na siyasa, gaskiya fisabilillahi bama a siyasance ba, ba a hadin kan jama’a ba, shi kansa a tasirin da Daba ke yi na jawo baki ya kassara wannan abun kuma in muka ci gaba da haka to maimakon yadda duniya ke hadewa wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewa to mu ragewa wannan abubuwan muke yi kuma wannan zai kawo mana tarnaki a rayuwarmu da kuma yin gasa da sauran al’adu da jama’u na duniya baki daya.”