African LanguagesExplainersFeaturedHausa

Al’adu da zamantakewa: Kaciyar mata da matsayinta a wajen Hausawa

Getting your Trinity Audio player ready...

Kaciya wata hanya ce da al’ummomi daban-daban a cikin wannan duniya suke bi wajen cire fatar da ta rufe kan azzakarin namiji don yin biyayya ga dokokin al’ada ko addini. A al’adance tun kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa da kuma karɓar sa da Hausawa suka yi, al’ummar Hausawa na yi wa ‘ya’yansu maza kaciya. Karɓar addinin Musulunci a wajen Hausawa, ya ƙara masu ƙarfin gwiwa wajen ƙara riƙo da yi wa ‘ya’yansu maza kaciya. Wannan kuwa ya faru ne saboda samuwar wasu Hadisai na Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi, waɗanda suka bayyana alfanu da muhimmancin yi wa maza kaciya, a matsayin hanyar kula da lafiya da kuma yin koyi da Annabi.

Bayan kaciyar maza, akwai wasu al’ummomi da suke yi wa mata kaciya inda suke cire dukkan tsokar belun da take cikin farjin mace. Ita ma wannan ɗabi’a, ana yin ta don yin biyayya ga dokokin al’ada da na addini. A al’adance, al’ummar Hausawa ba sa yi wa ‘ya’yansu mata kaciya, amma akwai wasu ayyuka da ake yi wa wasu mata a farjinsu, kuma ba kowace mace ake yi wa waɗannan ayyuka ba, sai waɗanda ake haifa ko kuma suka sami matsalar bayan sun girma. Daga cikin ire-iren waɗannan matsaloli akwai angurya ko belun-mata da sadadda. Wanzaman gargajiya na Hausawa ne suke yin ire-iren waɗannan ayyuka a ƙasar Hausa. Ga bayanin yadda waɗannan matsaloli suke da kuma yadda ake magance su a tsakanin matan Hausawa a ƙasar Hausa.

Angurya ko Belun-Mata

Angurya ko belun-mata wani tantanin nama ne wanda yake kamanni da ‘ya’yan auduga bayan an cire kaɗar auduga wadda ake sarrafawa don yin kaɗi da saƙa. Saboda yadda ya yi kamanni da ‘ya’yan auduga waɗanda ake kira gurya, shi ya sa ake kiran lalurar da angurya. Ana haihuwar wasu mata da wannan lalura a cikin farjinsu, wasu kuma sai sun girma yake fito masu. Idan ba a cire shi ba yana iya hana mace saduwa da namiji idan ta girma. Wanzamai na gane mata masu fama da angurya a lokacin da suka zo cire beli ko hakin-wuya. A nan ne idan budurwa ce, sai su binciki farjinta su ga idan tana da angurya, sai su cire shi.

Wasu wanzamai na yin amfani da yatsa domin cire angurya. Suna sa babban yatsansu ne su tallabo shi daga tushensa sai su sa ‘yar tsaga su cire shi. Wasu na amfani da allura da zare domin cire shi. Ana tsiro shi da allurar ne da zaren sai a ɗaga sama a sanya askar aski a yanke shi. Wasu wanzaman kuma suna amfani da hantsaki domin cire shi, ana sanya hantsakin a kamo tushensa sai a sa askar aski a yanke shi.Wasu kuma na amfani da akaifar babban yatsansu su kama shi daga tushensa su sa askar aski su yanke shi. Bayan an cire shi sai wanzamin ya tauna ‘ya’yan bagaruwa ya furza a wurin, daga nan kuma, sai ya barbaɗa maganin da zai tsayar da jini da wanda zai hana shi sake tuƙowa.

Sadadda

Mace mai lalurar sadadda ana haihuwar ta ne da wannan laluri, domin ana samun ƙofar farjinta ‘yar ƙarama ce wadda fitsari ne kawai ke iya fita ta wurin ta, amma can daga cikin farjinta lafiya lau yake. Matsalar wurin ƙofar farjin take. Wasu kuma ana haihuwar su lafiya lau, amma saboda rashin tsabta da rashin kula daga wurin iyayensu ko masu riƙon su, sai ƙofar ta sake toshewa. Matan da suke da irin wannan matsala idan za su yi fitsari sai ya riƙa fita kamar na namiji. Idan iyaye sun fahimci haka, sai su sanar da wanzamin gidansu domin ya binciki yarinyar don ya gyara ta. Ana yin irin wannan gyara ne ta yadda aka fahimci matsala. Ga waɗanda aka haifa da matsalar sai an sanya askar aski an ƙara buɗa ƙofar farjin, daga nan sai a barbaɗa maganin da zai tsayar da jini da wanda zai sa wurin ya yi saurin warkewa. Ga kuma waɗanda suka sami matsalar sakamakon rashin kula ko rashin tsabta, ana amfani da hannu ne a sake buɗa ƙofar, daga nan sai wanzamin ya gargaɗi iyayen yarinyar ko masu kula da ita da su riƙa tsabtace farjin yarinyar ta hanyar wanke mata a duk lokacin da ta yi fitsari ko ta tashi daga barci.

Bisa la’akari da yadda Allah, Maigirma da Ɗaukaka ya halicci mutane, jikin mutum ba shi da wata cikakkiyar kariya daga kamuwa daga wasu cututtuka. Allah Maigirma da Ɗaukaka, cikin ikonSa, sai ya sauko da wasu cututtuka da kuma magungunansu. A fafitikar mutum wajen samo magungunan cututtukan da suke matsa masa, sai Allah Maigirma da Ɗaukaka ya sanar da wasu manazarta da masana kiwon lafiya na gargajiya da na zamani fahimtar cewa, cuta na iya kama kowane ɓangare na jikin mutum. Domin magance cutar ana bin hanyoyi daban-daban waɗanda suka haɗa da shan magani ko shafawa wurin da cuta take, ko kuma cire wurin da cuta ta kama. Dangane da haka, a iya cewa, al’ummar Hausawa suna bin hanyoyin gargajiya daban-daban wajen magance cututtukan da suke addabar al’ummarsu. Daga cikin su, akwai waɗanda ake samu a cikin farjin mata, amma al’ummar Hausawa ba sa yi wa ‘ya’yansu mata kaciya, sai dai suna gyara wasu matsaloli da ake haihuwar wasu mata da su, ko kuma suka sami matsalar bayan sun girma.

Farfesa Bashir Aliyu Sallau shi ne Sarkin Askar Yariman Katsina kuma ya turo mana wannan bayani na musamman ne daga Sashen Koyar da Hausa Tsangayar Fasaha a Jami’iar Gwamnatin Tarayya Dutsin-Ma inda ya ke koyarwa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »