Zargi: Wata mai amfani da shafin soshiyal mediya na zargin wai ta haifi jariri mai hakora a cike.
Akwai tatsuniyoyi da yawa dangane da jarirai masu hakora, akwai wadanda ke bayani kan sadda hakoran ke fita, yadda su ke fita, wata sa’a ma har da dalilin da ya sa su ke fita. Misali mai kyau shi ne wani labarin da aka wallafa a shafin instagram mai suna “Yourblackizmagic” inda aka sanya wani hoton da aka samu daga shafin wata Kaitlyn Valdes tare da zargin cewa an haifi jariririyarta da hakoranta a cike.
Masu shafin Yourblackizmagic sun wallafa labarin tare da tambayoyin ko hakan na iya kasancewa a zahiri “Wannan da gaske ne?” Kanun labarin ya tambaya. Hoton da aka sanya wanda aka danganta da shafin Kaitlyn Valdes ya gwado hotunan jaririya na dariya da manyan hakora irin na magidanta.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da bin diddigin ainihin hotunan zuwa shafin Kaitlyn Valdes wadanda aka wallafa a shafukan Instagram da Facebook ranar daya ga watan Mayun 2022. Taken hotunan shi ne “kun tuna wannan? Ga yadda ta zama yanzu. Kun fara ji kamar kun tsufa?” Hotunan sun nuna yarinyar tana jaririya da kuma sadda ta fara tafiya.
A gurbin da ake tsokaci, mun lura da cewa babu wanda ya yi la’akari da hakoran jaririyar ko ma ya yi magana a kai. Yawancin wadanda su ka yi tsokaci sun ma fi mayar da hankali kan tallace-tallace ko kuma tambayoyin da su ka danganci kasuwanci.
Yin hakori wani bangare ne na bunkasar yara. Ya kan faru ne lokacin da suke watanni hudu zuwa bakwai amma bincikenmu ya nuna mana cewa akwai wadanda ake haifa da hakora.
Hakora na Haihuwa ko kuma Natal Teeth a turance
A kan haifi wadansu jarirai da hakora daya ko biyu wadanda ake kira natal teeth da turanci domin suna nan da aka haife su.
Ana yawan samun natal teeth amma kuma kanana ne ba su riga sun gama tsurowa ba, sa’anan yawancin lokuta ba su da karfi sosai kuma launinsu ya sauya. Wannan bitan da muka yi ya gano cewa a kan sami irin wadannan hakora akalla sau daya cikin haihuwa dubu biyu zuwa uku.
Babu wanda ya san dalilin da ya sa ake samun natal teeth a jarirai amma kuma ana yawan danganta shi da abubuwa kamar kwayoyin halitta, zazzabi, cuta, rashin abinci mai gina jiki. Masu bincike kuma suna zargin mai yiwuwa akwai wadansu yanayin kiwon lafiya da ke janyowa.
Duk da cewa akwai labaran da suka tabbatar cewa ana samun natal teeth, har yanzu babu rahoton da ya tabbatar da abin da ke janyo shi. Wajibi ne mu banbanta natal teeth da neonatal teeth wanda kan fito a bakin jariri a watan shi na farko.
Da muka duba hotunan Kaitlyn Valdes, mun lura cewa hakoran da ke hoton sadda ‘yare ke jaririya sun banbanta da na yanzu. Dan haka an gyara hoton ne an sanya mi shi hakora? Ko kuma an cire hakoran da aka haifi ‘yar da su ne kuma har sabbi sun fito a bakinta yanzu?
Domin amsa wadannan tambayoyin, mun duba shafin google domin gano sadda hotunan su ka fara bayyana a shafukan yanar gizo wanda ya kai mu zuwa ga wadansu rahotanni.
AbcNews da Healthline sun wallafa wannan hoton amma da bayanin cewa ba irin wadannan hakoran ne ake haifan jarirai da su ba.
A waje guda kuma wani rahoton da jaridar Legit.com ta wallafa a watan Mayun 2021, ta wallafa wadannan hotunan tare da zargin cewa hoton jaririyar da aka haifa da hakora a cike ya janyo matsala a shafin yanar gizo. Sai dai labarin bai bayar da cikakken bayani kan yadda aka haifi yarinyar ba, ko sunan ‘yar da na iyayenta. Wani shafin kuma mai suna thepreachersportal ya yi kokarain bayar da bayani a addinance ba tare da bayar da cikakken bayani kan jaririyar ko inda su ka sami labarin ba.
Binciken kwa-kwaf din da mu ka yi bai nuna mana cewa an gyara hoton hakoranba. Sai dai DUBAWA ta gano wani manhaja mai suna FaceApp wanda a baya wata mai daukar hoto ta taba amfani da shi wajen sanya hakorin magidanta a bakin jariri. Wannan mai daukar hoton mai suna Amy Haehk ta yi amfani da FaceApp wajen nuna yadda fuskar jarirai zai fito idan har suna da hakora. Hotunan da Amy ta samu sun yi kama da abin da aka gani a shafin Valdez.
Mene ne FaceApp
FaceApp Manhaja ce da ke amfani da amfani da illimin fasaha wajen gyara hotuna da bidiyo. An kaddamar da shi a ios ne a waan janaitun 2017 sa’annan a Android a watan Fabrairun 2017. Akwai hanyoyi daban-daban na alkinta hotuna ta yin amfani da manhajan. Misali ana iya sauya yanayin fuska, ana iya yin kwalliya, ko murmushi, ko sauya launin gashin kai, ko sanya tabarau, ko kara shekaru ko kuma sa gemu da gashin baki.
Ba mu ga wata alamar kokarin gyaran hoton ba da mu ka yi binciken kwa-kwaf domin an yi amfani da FaceApp ne. Tunda ba kara abubuwan ake yi da fasahar photoshop ba yana da wahalar gane wuraren da aka yi aiki a kai.
Hakoran dai ba natal teeth ba ne domin ba su yi kama da hakoran da ake haifan jarirai da shi ba sun yi kama da na magidanta ne.
A waje guda, hoton diyar Valdez da aka nuna bayan ta dan kara girma ya nuna cewa tana da irin hakoran da aka san yara masu wannan shekarun da ta ke su ke da shi (wajen guda 20) hakoean cikin hoton ba su yi kama wadanda su ke hoton farkon ba. Hoton ya nuna tana da hakora biyu a dasashin sama, hudu a na kasa wadanda ko daya ba su yi kama da abin da aka nuna a hoton farko ba.
Sharhi daga kwararru dangane da batun
Da DUBAWA ta tuntubi kwararru na fannin kiwon lafiya kan yiwuwar samun jariri da hakora radau a baki daga haihuwa da ma ainihin yadda ya kamata bakin su ya kasance, wani likitan mata a asibitin National Hospital da ke Abuja, Jeremiah Agim ya ce ya taba ganin wadanda ke da hakoran natal health amma bai taba gani wani abu mai kama da hoton jaririryar Valdez ba.
“Natal teeth hakora da kan fito a bakin jarirai tsakanin kwanaki 28 da haihuwarsu. Irin wadannan hakoran yawanci ba su da yawa, ba su da karfi kuma ‘yan kanana ne. Wadansunsu dai na da girma. Ba zan iya karyata abin da ke cikin wadannan hotunan ba domin ni ba likitan hakora ba ne. Sau daya na taba ganin irin hakoran lokacin da nake dalibi da na je aiki a sashen kula da yara da jarirai,” ya bayyana.
Da ya ke ba mu shawarar tuntubar likitan hakora ya ce “idan an haifi jarirai haka, abin yi shi ne a cire hakoran, kuma wannan aikin likitan hakora ne. Wato hakoran da ba su tsuro yadda ya kamata ba. Babu shakka liktan hakora ya ga ire-iren wadannan hakora a aikin shi.”
Wata ma’aikaciya a sashen kula da hakora Agu Chioma, a asibitin Kungiyar Matan Sojojin Najeriya (NAOWA) da ke Abuja ta ce babu yadda za’a yi a haifi jariri da irin hakowan da ke cikin hoton Valdez domin wadanda ma aka haifa da hakori ba su zuwa da hakora cike kamar yadda aka gani a hoton.
“Wannan ba zai yiwu ba, wata kila fasahar gyara hoto na photoshop aka yi amfani da ita. Ana iya haifar jariri da hakora amma ba duka a cike ba,” ta bayyana
A Karshe
Bincikenmu wanda ya sami goyon bayan kwararru ya nuna cewa babu shakka a kan haifi wasu jarirai da hakora amma ba a cike da bakin ba. Dan haka abin da aka gani a hoton karya ne an yi amfani da wata fasaha ne wajen gyara hoton.