African LanguagesHausa

Osinbajo ba ya raba wa ‘yan Najeriya tallafin dubu 33

Zargi: Wabi sakon WhatsApp na zargin wai mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo na rabawa ‘yan Najeriya tallafi na nera dubu talatin da uku uku 

Zaben shugaban kasa na shekarar 2023 na kara matsowa kusa-kusa inda ‘yan Najeriya za su yanke shawara kan wanda zai jagoranci lamuran kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Karbar kudin tukuici daga wurin ‘yan takara ya zama al’ada ganin yadda ‘yan siyasa ke amfani da tukuicin wajen jan hankalin wadanda suka cancanci yin zabe a Najeriyar.

A shekarar 2017 ta wallafa wadansu hotunan da ke nuna irin abin da ‘yan siyasa ke yi lokacin zabe dan jan ra’ayin ‘yan Najeriya.

Saboda irin arzikin da ‘yan siyasa suka yi a shekarun da suka gabata, DUBAWA ta yi binciken irin wadannan zarge-zargen da dama domin akwai masu zamban da su ke amfani da hotunan ‘yan siyasa su aikata ta’asa. Alal misali, mun fallasa cewa akwai mayaudaran da su ke amfani da sunan Tinubu suna damfarar mutane a shafukan yanar gizo-gizo.

Kwanan nan wani sakon da ake yadawa a WhatsApp, tare da zagin cewa mataimakin shugaban kasa kuma mai neman tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar Farfesa Yemi Osinbajo na bayar da dubu 33 kyauta ga ‘yan Najeriya.

A cewar sakon wanda ke dauke da wani adireshi, na cewa kudin ya fito daga asusun yakin neman zaben mataimakin shugaban kasar ne.

Domin kaifin wanann zargin da ma irin tasirin da zai iya yi kan masu zabe, DUBAWA ta ga ya kamata a binciki zargin.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi inda ta yi amfani da sunan mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo dan ganin ko akwai wani labarin tallafin da aka danganta da shi.

Abubuwan da ke sanya alamar tambaya ga sahihancin labarin

Binciken kwa-kwaf a shafin Domainbigdata – wanda ke tantance adiresoshin yanar gizo-gizo na kwarai da na bogi, mun ga cewa mutane da dama sun kai karar shafin suna zargin shi da karya doka.

Wani abun da aka cika samu a shafuka irin wannan shi ne shaidun karya wadanda za su fito su rika cewa sun sami alfanu daga duka abin da aka rubuta a ire-iren shafukan. Yawanci wadanda ke zamba a yanar gizo na amfani da wanann salon dan ta haka su ke jan hankalin wadanda ba su ji ba su gani ba. Haka nan kuma duk wani adireshi da ke kan shafin ba’a iya latsawa ko ziyartar shafin.

Bacin haka kuma shafin na cike da kura-kurai na nahawu da alamun rubuta, ko daya ba dadin karantawa. 

Sai dai sakon ya yadu sosai saboda wadansu sharuddan da aka yi amfani da su a shafin. Misali duk wanda ya karanta sakon ana bukatar shi ya raba da ‘yan uwa da abokan arziki. Masu yaudara na yawan amfani da wannan salon dan sun san duk wanda ya shiga shafin zai cika wannan sharadin.

Mun kuma ga wani katin da aka ce a latsa idan ana neman karin bayani. Shi ma mun latsa amma bai kai mu ko’ina ba.

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa Farfesa Yemi Osinbajo ba ya bayar da wani tallafin nera 33,000 ga matasa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button