African LanguagesHausa

Ayyukan da ‘yar majalisa Ireti Kingibe ta Birnin Tarayya Abuja tayi da’awar aikatawa Karya ta jagoranci Gaskiya

Getting your Trinity Audio player ready...

Ireti Kingibe, ‘yar majalisa daga jam’iyyar Labour Party da ta cika shekara guda akan kujerarta a majalisa a ranar 12 ga watan Yuni, 2024. Makonni kadan da suka gabata ta gudanar da bikin cika shekara guda a kan kujera inda anan ta gabatar da abubuwan da ta cimma da suka hadar da kudirai da ta gabatar a majalisa da ayyuka da ta gabatar a mazabarta kamar yadda ta wallafa a shafinta na X account (archived).

Cikin ayyukan da ta ce ta aiwatar sun hadar da aikin gina hanya a Kpaduma, da Karu da Gwagwalada. Haka kuma ta lisafo aikin samar da hasken lantarki a tituna a Karamajiji da Mpape da Kwali da Jikwoyi da aikin samar asibiti mai gadaje 50 a Dobi da gina dakin kwanciya a asibitin Abuja da ke a Gwagwalada kamar yadda ta zayyano cikin abubuwan da ta cimma.

Cikin abubuwa da DUBAWA ta lura da su ta gano cewa ‘yar majalisar ta zayyano ayyuka 29 baki daya, mafi akasari ba ta bayyana inda aka yi ayyukan ba, amma DUBAWA ta gudanar da bincike kan ayyuka guda tara da ke zama sanannu. 

Ireti Kingibe’s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts

Da’awa da ke zama ta gaskiya


Daga cikin ayyuka guda tara DUBAWA ta gano ayyuka guda uku da ke zama na gaskiya. Mun fara da aikin gina asibiti mai gadaje 50 a Dobi da Gwagwalada wadanda sanatar ta ce  aikin ana ci gaba da “gudanar da shi.” A farkon watan Agusta mai dauko rahoto ya je wurin da ake aikin inda ya ga cewa ana kan aikin ba a kammala ba. Inda ake aikin ba shi da nisa da wata cibiyar kula da lafiya a yankin. 

Ireti Kingibe’s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts

Aikin gina asibiti mai gadaje 50. Wanda ya dauki hoto: Phillip Anjorin

A aiki na biyu da aka tabbatar. mun je aikin gina hanya ta  Ishan Road a Karu sannan an tabbatar da rahotanni (reports) na gina hanya mai kwalta mai nisan kilomita 6, daga nan sai muka nufi yankin Karamajiji inda tayi da’awar cewa ta samar da fitulu 23 wanda ke zama na uku cikin ayyukan da muka tabbatar. 

DUBAWA ta ga fitila ta farko a hanyar shiga yankin al’ummar wacce aka bata lamba ta 12, wadannan fitulu na jere kusa da juna.

Ireti Kingibe’s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts

Fitilun titi a Karamajiji. Wanda ya dau hoto: Phillip Anjorin

Ta bayyana cewa an sanya fitilun titi 23 a Anagie da Sangaruwa da Ajegunle da Gbagi village da  Mashapa. DUBAWA ta tabbatar da ganin fitilu hudu a Gbagi village, yayin da a sauran wuraren babu labarin ganin wata fitialar titin a bangaren, al’ummar yankin ma sun tabbatar da cewa basu ga wani aiki ba mai kama da wannan.

Wurin da aka ga wallenta

Anthony Udeh, mai tuka babur na haya a yankin Jikwoyi da ke a wajen Abuja, yayi gatsine ne lokacin da mai aiko mana da rahoto ya bayyana cewa ai ‘yar majalisa daga yankin ta gina hanya mai nisan kilomita 1.5 a Phase 1. A lokacin da yake tafiya a wannan yanki da ake fadi, yayi da’awar cewa shekara guda da ta gabata yayi hadari akan wannan hanya sai da aka garzaya da shi zuwa asibiti ya kwashe watanni uku. Bayan da muka isa hanyar, ya bayyana cewa tituna a wasu rukunan na Jikwoyi an masu kwalta shekaru biyu da suka gabata , amma a rukunin farko phase 1  an dai kawo mota ta share titun don kaucewa zaizayar kasa.

“A tsawon sama da shekara guda ban taba ganin wani babban inji wanda zai yi aiki a kan gyara wannan titi ba, ballantana ayi maganar gina titi sai dai idan share titi na nufin an gina titi kenan.” kamar yadda ya fada a turancin pidgin.

Hanya kuwa a Jikwoyi Phase 1 ta zaizaye babu wata alama da ta nuna cewa ana aikin gina hanya, a tsawon shekara guda da ta gabata ko ya zuwa watan Agusta 2024. Sai dai abin da ke a zahiri DUBAWA ta lura da cewa an kafa alama ko allo a kan hanyar: Da suna  “ Aikin kare zaizayar kasa a hanyar God of Elijah, Jikwoyi a Abuja Fadar Gwamnatin Tarayya.

Ireti Kingibe’s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts

Jikwoyi Phase 1. Wanda ya dauki hoto: Phillip Anjorin

DUBAWA ta tabbatar da cewa hanyoyin da ta fada dama anyi masu kwalta tun tuni idan aka cire ta Jikwoyi Phase 1. Har ila yau wanda ta gada Philip Aduda na jam’iyyar PDP shi ya tabbatar da ganin ayi su a kudurin kasafin kudi na 2023 wanda aka sawa hannu ya zama doka a ranar 3 ga watan Janairu,2023. Mun samu bayanai daga Tracka, wata kafa da ke bibiyar ayyukan da ake yi a cikin al’umma don tabbatar da ganin an yi su.

A 2023 ayyukan gwamnatin tarayya na yankunan al’umma da kudaden da aka ware don aiwatarwa (consolidated capital projects) a birnin tarayya an warewa aikin gina hanya ta Jikwoyi Phase 1 Naira miliyan 90 da lambar aikin ERGP202301237 a lokacin Aduda. Hukumar da ke lura aikin itace ta raya kogin Niger (Upper Niger River Basin Development Authority (RBDA), an ba da N7,616,744.18 a ranar 14 ga watan Agusta,2023, don fara aikin gina hanyar mai kwalta kamar yadda yake a GovSpend, wata kafa da ke ba da bayanai kan yadda gwamnatin tarayya ke kashe kudadenta.KO da yake a lokacin Kingibe tana sanata, a lokacin Aduda ne ya sanya aikin a kasafin kudi.

Haka nan shima hanyoyi da kwalbati a Kpaduma 1 da 3,  wanda shima tayi da’awar aiwatarwa. Naira miliyan 100 aka ware don ginin hanyoyin a 2023 da lambar ZIP20231339 kuma ana ci gaba da wannan aiki tun a ranar 29 ga watan Dismba, 2022, inda aka saki kudade N45,469,767.45. 

DUBAWA ta je wurin sai ta gano cewa an yi wani bangare na aikin. Shi kansa wannan fara aikin bai nuna alamar na baya-bayan nan ba ne. Haka allo da ke nuna shedar wanda yayi aiki ya nuna cewa Mista Aduda ne yayi.

Ireti Kingibe’s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts

Allo da aka kafa a Kpaduma 1 & 3. Wanda ya dauki hoton: Phillip Anjorin

Ko da yake bamu samu shedu ba kan kudade da aka ware don aikin Pai a Kwali daga kafar samun bayanan ta GovSpend, mun gano cewa an ware Naira miliyan 100 don aikin gina hanya da hanyoyin ruwa ko kwalbati a ayyukan da za a yi a 2023 inda aka ba wa aikin lamba ERGP202301236 kamar yadda yake a bayanan Tracka, a wannan lokaci Aduda ne sanata an kuma bayyana shi a matsayin “aikin da ake tsaka da yinsa” lokacin da muka je wajen mun gano cewa an yi rabin aikin.

Ireti Kingibe’s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts

Allo da ke nuna aikin gina hanya a Pai, Kwali. Wanda ya dauki hoto: Phillip Anjorin

Ms Kingibe ta yi da’awar gina ofishin kwararun likitoci a asibitin koyarwa na Abuja da ke Gwagwalada, amma ba ta bayyana cewa ana yin aikin bane.

Har ila yau bayanai da aka tattara sun nunar da cewa Mista Aduda ne ya jagoranci wannan aiki kamar yadda aka gani a Tracka. Ga ma lambar aikin ERGP202301233, an kuma ware masa Naira miliyan 100.

 A ranar 3 ga Disamba, 2023 GovSpend ta bayyana cewa an ware kudi N72,159,994.5  don wannan aiki, abin da ya hadar da harajin aikin, da tsarin zanensa da ginawa, watanni shida daga bisani kuma aka sake biyan N18,893,874.92 don ci gaba da aikin. Baki daya abin da aka kashe N91,053,869.42. Kamar yadda aka fadi a baya wannan ya sa aka ga rashin gaskiyar da’awar sanatar na bayyanar aikin cikin nasarar da ta cimma. 

Ireti Kingibe’s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts

Ofishin kwararru a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja. Mai hoto : Phillip Anjorin

 Haka zalika sanatar ta yi da’awar kammala aikin hanyar Angwan Dodo, amma DUBAWA ta gano yadda aka kammala aikin. Amma kafin ta zama sanata an ware miliyan N150, ga ma lambar aikin ERGP202301239 kamar yadda yake a kan Tracka. 

Ireti Kingibe’s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts

Jadawali da ke nuna yadda ake tsara kudade da ake kashewa da yadda ake sakin kudaden don aikin kammala hanyar  Angwan Dodo. Wanda ya tsara Phillip Anjorin

Bayanai da aka tattaro daga GovSpend sun nunar da cewa an fara biyan kudaden aikin tun 12 ga Disamba,2020 lokacin da aka ba da kudi N27,065,861.61 don aikin gina hanya mai tsawon kilomita 1.3km. Domin aiwatar da aikin mai tsawon kilomita 1.3km a 2021. Gwamnatin Tarayya ta saki kudi N38,649,234.10 a ranar 25 ga watan Maris sai ta sake sakin N31,544,509.22 a ranar 4 ga Oktoba sai kuma N29,935,452.07 a ranar 29 ga Fabrairu, 2022. Ya zuwa 14 ga Agusta, 2023 gwamnatin Tarayya ta fara aikin sakin kudade don tsara kammala ayyukan, wanda aka kashe N8,030,697.69. An saki kudade sama da miliyan N127 don kammala aikin ya zuwa 20 ga Maris,2024 ga ma lambar aikin kwantiragin ERGP202301239.  

Ireti Kingibe’s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts

Kasafi-kasafi na ayyukan mazaba da aka gudanar da binciken gaskiya a kansu. Wanda ya tsara Phillip Anjorin

Bayani kan ayyukan mazabu

Ayyukan mazabu a Najeriya, ayyuka ne da gwamnatin tarayya ke daukar nauyinsu  wadanda kan inganta rayuwar al’umma da suka fito daga mazabun ‘yanmajalisar tarayya. Tun bayan da aka dawo tafarkin dimukuradiyya a 1999, an ware miliyoyi dubbai na naira ta yadda za a tabbatar da ganin al’umma sun amfana kai tsaye daga kudaden da gwamnati ke kashewa.

Babbar manufar irin wadannan ayyuka shine a tabbatar da ganin al’umma sun amfana da ayyuka na gwamnati kamar a fannoni irin su samar da ababen more rayuwa da fannin lafiya da ilimi da tallafin ayyukan gona wadanda ‘yanmajalisa kan gabatarwa wasu ma’aikatu don tabbatar da ganin an aiwatar.

Duk da cewa wasu rahotanni sun yi nuni da cewa an ware tsabar kudade tiriliyan 2 don gudanar da irin wadannan ayyuka (constituency projects) tun daga 2003 zuwa yau, inda aka ware ayyuka sama da 18,000 a fadin Najeriya, da dama irin wadannan ayyuka ba a yi su ba, koma an yi almundahna wajen aiwatarwa (poorly implemented,). Abin da ya jawo lalata dukiyar al’umma.

Dukkanin shugabannin Najeriya da suka gabata in ban da Umaru Yar’adua sun soki wannan tsari har wanda ke a gaba wato Olusegun Obasanjo.

Har ila yau Lukman Raji wani lauya kuma darakta a fannin shari’a a cibiyar Elites Network for Sustainable Development (ENetSuD), ya bayyana cewa aikin wanda ake kira Zonal Intervention Project (ZIP)-ba aiki bane da ‘yanmajalisa suka kirkira, amma aiki ne na hadin gwiwa tsakanin majalisar zartarwa da majalisar dokoki.”Tsari ne da aka fito da shi don a tabbatar da ganin cewa al’umma sun sharbi roman dimukuradiyya a mazabunsa.”

Ko da yake a tsarin kundin mulkin kasa babu wani aiki wai shi na mazabu, Mista Raji yace ‘yanmalisa na gabatar da shi kamar wasu nasarori da suka cimma, wannan na iya zama yaudara.”Yanmajalisa na gabatar da su ga al’umma a matsayin su suka yi su, har wasu lokutan suna alfahari wanda ba haka lamarin  yake ba, burin da ake da shi shine a kai aiki ga al’umma na mazabu ba wai danmajalisa ya rika nuna cewa shi yayi ba, wannan ne  ya sanya ake ganin ayyukan da ake a mazabu a matsayin wani makami ga dan siyasa sabanin ace ana yinsu ne don samar da ci gaba a yankunan na mazabu.

 A cewar Ijeoma Okereke, manaja a cibiyar bibiyar ayyuka ta UDEME Africa da ke duba ayyuka karkashin CJID, ta kara da ba da bayani kan aiwatar da ayyuka, tace ko da danmajalisa ya kammala wa’adin mulkinsa ayyukan da suke lura da su za su ci gaba da bibiya muddin an ba da kudaden aiwatarwa.

Ta kara da cewa “Idan dan majalisa ya kammala wa’adin mulkinsa, irin wadannan ayyuka za su ci gaba saboda ai dama an riga an saki kudade don gudanar da ayyukan daga ma’aikatar kudi da kasafi zuwa ga ma’aikatu da hukumomi da aka dorawa alhakin gudanar da ayyukan.”

Kazalika tace  danmajalisa da ya gaji wani zai ci gaba da lura da irin wadannan ayyuka yayin da a bangare guda kuma dan majalisar shi ma zai gabatar da nasa aikin idan ya lura da akwai bukatar yin hakan.

“Muna bukatarsu”- Mazauna yankuna 

Yankunan al’ummar guda biyar da Ms Kingibe ta bayyana a Mpape basu da hanyoyi masu kyau da masu amfani da babura za su yi amfani da su musamman da dare,ba gaskiya ba ne an sanya fitilun titi, Eunice Adelabu mai sana’ar POS a Ajegunle tace ta daina kasuwanci da dare tun bayan da aka yi mata fashi a watan Afrilu, watan da ya gabata ne ta dawo bakin aiki.

Ta kara da cewa ”Masu sana’ar tukin babur sun dena shigowa wannan hanya da daddare saboda munin hanyar, idan da a ce an samar da haske a hanyar da za su rika iya bin hanyar suna kaucewa ramuka, rashin masu baburan ya sanya har aka yi min fashi, ai da na bar hanyar da wuri.”

Ireti Kingibe’s claims on first-year constituency projects in FCT had more flaws than facts

Yadda hanyoyi suke a yankunan al’ummar Mpape. Wanda ya dauki hotunan Phillip Anjorin.

Yakubu Aliu, manomi ne a Ledi, ya ce idan aka kammala aikin gina asibitin Dobi cikin gaggawa zai taimaka mana wajen kula da lafiyarmu.” Idan aka samar da isassun ma’aikatan lafiya sabon asibitin zai taimaka ganin yadda ake samun cikowa a cibiyar kula da lafiya ta Dobi, musamman ga al’umma da ke zama makota za su fi amfana da wannan asibiti sabanin suce sai sun je Asibitin Gwagwalada.”

Duk da abin da ya fada tun da fari Mista Udeh yace yana fatan ganin an kammala aikin hanyar ta Jikwoyi Phase 1 don samun saukin zirga-zirga.

Aduda ya ciri tuta, Kingibe ta kwashi kunya

An yi kokari a lokuta da dama don yin magana da Ms Kingibe ta kiran wayar hannu da WhatsApp amma bata dauki wayar ba. Mun kuma aika mata da sako ta Twitter da e-mail amma babu wata amsa da ta bayar har lokacin hada wannan rahoto. Da muka tuntubi mai taimaka mata kan harkokin yada labarai Kennedy Nwankwo, yace zai tuntube mu bayan tuntubar mai kula da aikin a ranar 2 ga Oktoba,2024, shima babu abin da muka ji daga gare shi lokacin kammala wannan rahoto.

A tattaunawa ta wayar hannu da DUBAWA tayi da Mista Aduda yace ayyukan da ake da’awa sun kasance wani bangare ne na ayyukan da shi da abokin aikinsa a majalisa suka amince da su .”Kasafin 2023 an amince da shi kafin ma sabuwar gwamnati ta zo a watan Yuni. A lokacin da ni  nake kan kujerar, ina tabbatar da cewa an fara aiwatar da kasafin kafin ma wa’adin mulkinta ya fara.” A cewarsa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »