African LanguagesHausa

Da gaske ruwan kwa-kwa na tsayar da gudawa?

Zargi: Ruwan kwa-kwa na tsayar da gudawa

Da gaske ruwan kwa-kwa na tsayar da gudawa?

Bincikenmu ya nuna cewa wannan ba daidai ba ne. Idan har an yi amfani da ruwan kwa-kwa dan kishi ne da kuma mayar da ruwan da jiki ya rasa sakamakon gudawar, ba dan ya tsayar da gudawa ba.

Ruwan kwa-kwa ya zama wani abin shan da ake yayi a wannan zamanin, ba dan zakin shi ko kashe kishin ruwan da ya ke yi kadai ba amma saboda sinadarai masu amfani wajen inganta jikin da ruwan ya kunsa. A cikin kwa-kwa ne ake samun ruwan bayan an fasa. Daga gani dai ruwa ne amma kuma yana kunshi da wasu sinadaran da ba’a samu a ruwan da aka saba amfani da shi kullun.

Kwannan nan wani shafi a Facebook wanda ake kira Aduramingba Herbel Remedies wato magungunan gargajiya na Aduramingba ya yi zargin cewa ruwan kwa-kwar na tsayar da gudawa.

Masu shafin suna zargin wai idan har jaririn da ke kasa da watanni shidda (6) na haihuwa na gudawa, ana iya bashi babban cokalin ruwan kwa-kwan guda biyu kwani sa’o’i shidda yayin da jariran da suka wuce wata 6 su kuma ana iya ba su babban cokali hudu. Yara kanana kuma wadanda suke tsakanin shekara daya zuwa biyu na haihuwa ana iya ba su rabin kofi sa’annan masu shekaru biyu zuwa sama suna iya shan kofi guda.

“A bayar da ruwan kwa-kwa ga duk yaron da ke fama da yawan bayangida, gudawa ko atini,” shafin ya bayyana.

Tantancewa

Gudawa wanda ke nufin bayangidan da kan kasance ruwa-ruwa wanda a kan samu sau uku ko fiye a rana abu ne da ya kan afku ga dan adam sakamakon cututtuka kamar mura, ciwon ciki, cin abincin da ya gurbace ko mai dauke da guba ko kuma dai wanda bai zauna sosai a cikin mutun ba, magunguna da sauransu.

Yawan gudawa kan janye ruwan jikin mutun da ma sinadaran electrolyte wadanda su ke taimakawa dan adam wajen motsa gabobin jiki da kuma daidaita kwayoyin halittan da ke ciki da wajen jiki. Rashin kan kasance babban matsala. Duk da cewa rashin ruwan jikin yana a mataki na biyu cikin jerin manyan abubuwan da ke kashe yaran da ke kasa da shekaru biyar na haihuwa, abu ne da ake iya karewa daga faruwa.

Ruwan kwa-kwa abu ne da aka tabbatar ya kunshi sinadaran da ke inganta lafiyar dan adam kuma yana taimakawa wajen mayar da ruwan jiki, shi ya sa mutane ke amfani da shi a lokacin da suke gudawa ko kuma suka kamu wani abin da ke rage ruwan jiki.

Sinadaran Potassium, Sodium, Calcium da Magnesium din da ya ke dauke da shi ne ma aka tabbatar suna daidaita tsakanin kwayoyin halittan da ke cikin jikin dan adam. To sai dai kuma, yawan wadannan sinadaran da ake samu a cikin ruwan ya danganci shekarun kwa-kwan, wato ko an samo daga tsohuwar bishiya ko kuma bishiyar da ba ta dade da yin wayo ba. Bishiyoyin da suka fi dadewa sun fi kasancewa da sinadirai mafi yawa.

Banda haka yana da mahimmanci kuma a gane cewa shan ruwan kwa-kwar da yawa na iya janyo gudawa domin akwai wadanda jikin su baya shiri da sinadarin Potassium idan ya yi mu su yawa sai su tsure.

Domin irin wannan dangantaka da mu ka gani tsakanin ruwan kwa-kwar da gudawa, mun nemi jin ta bakin kwararru dan sanin ko ana iya baiwa jarirai da kananan yara ruwan kwa-kwar.

Mun ga wani labari wanda ya bayyana wasu daga cikin ire-iren alfanun da ruwan kwa-kwar ke da shi amma kuma ya yi gargadin cewa bai kamata a baiwa jariran da ke kasa da watanni shidda da haihuwa ruwan ba saboda yana iya janyo musu rashin lafiya (Kaikayi ko kuraje). Wani labarin a shafin parenting.firstcry.com, shi ma ya goyi bayan hakan, ya ce lallai ruwan kwa-kwa na da amfani amma bai kamata a baiwa jarirai kasa da watanni shidda na haihuwa ba.

Me Kwararru ke cewa? 

Wani babban ma’aikaci a babban asibiti na kasa da ke Abuja wato National Hospital Mr. Jeremiah Agim ya bayyana cewa ruwan kwa-kwa na daya daga cikin magungunan gargajiyar da ake amfani da su a gida idan mutun na gudawa domin mayar da ruwan da ya fita daga jiki.

Mr: Agim ya kuma kara da bayyana wadansu karin abubuwan da ake amfani da su a gida a lokacin da ake zawo, wadanda suka hada da ruwan garin rogo da da na shinkafa, sai dai ya ce wadannan da ma ruwan gishiri da suga ba su kadai ne ake amfani da su idan aka kamu da gudawa ba.

“Idan har an ga mutun na gudawa akan bukace shan maganin asibiti na antibiotics,” ya ce.

Ya ce yawan ruwan kwa-kwar da shafin ta ce a bayar ma ba dai-dai ba ne domin kamata ya yi a bayar da shi kamar yadda ake bayar da ruwan gishiri da suga:

“Yawan da suka bayyana ma a nan ba daidai ba ne, za’a bai wa yaro ruwan ne bayan an duba ko ya rasa ruwa a jikin shi, abin da likitan yara zai tantance kafin ya yanke shawarar yawan ruwan da za’a bayar.”

Haka nan kuma idan har aka je asibiti da gudawa ba wannan ruwan ne za’a ce a bai wa yaro ba sai dai idan abin da iyayen za su iya saye ke nan.

“Ka da ku je asibiti kuna tunanin likita zai ce ku bai wa dan ku ruwan garri ko na shinkafa ko na kwa-kwa. Kamar yadda na bayyana magungunan gargajiya ne ba abin da likitan yara zai bayar da shawarar saye ba. Ana bayar da irin shawarar ne kadai idan har mutun ba zai iya saye ko hada ruwan gishiri da suga ba,”

Alabi Olukoayode likitan yara a asibitin Cedarcrest da ke Abuja ya ce babu wata hujja ta kimiya dangane da sahihanci amfani da ruwan kwa-kwar kuma a ra’ayin shi amfani da shi ma zai iya janyo koma baya a yunkurin neman maganin gudawar.

“Babu wata hujja ta kimiyya na amfani da wadannan magungunan gargajiyar. Yawancin gudawa a yara kwayoyin cuta ne ke janyowa. Amfani da ruwan kwa-kwa ma kananan yara bai dace ba kuma yana iya janyo tsaiko wajen samar da maganin abin da ke damun yaran ko kuma ma ya zama wani ciwon da ke da babban barazana ga rayuwar yaran,” ya ce.

Haka nan kuma, ma’aikacin lafiya a asibitin kwararru na Rehoboth da ke Lokoja, Okpanachi Achille, ya ce ba zai iya cewa ruwan kwa-kwa na tsayar da zawo ba, amma dai a kan bayar da shawarar amfani da shi a madadin ruwan gishiri da suga (ORS)

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa wannan batu ba gasjiya ba ne ana amfani da ruwan kwa-kwa wajen mayar da ruwan jiki ne kawai ba dan tsayar da gudawa ba. Bacin haka, ba mu ga sakamakon wani bincike na kimiya da ya bayyana ruwan kwa-kwa a matsayin maganin da ke tsayar da gudawa ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button