African LanguagesYoruba

Ba gaskiya bane wai Dangote zai karkatar da kasuwancin sa zuwa kasar Amurka

Zargi: Wani sakon WhatsApp da aka rika yadawa ya bayyana cewa wai fitaccen attajiri wanda ya fi kowa karfin arziki a nahiyar Afirka Aliko Dangote zai zuba jarin kashi 60 na dukiya da kaddarorin sa a kasar Amurka domin kare dukiyar iyalin sa na wani tsawon lokaci.

Sabanin zaton da aka yi na cewa Dangote zai sanya kashi 60 cikin 100 na kadarorin sa a Amurka, Dubawa ta gano cewa Dangote ya ce zai kai wani kaso na kudaden sa kasashen da ba a nahiyar Afrika ba ne.

Cikakken Bayani

Wani hoto da ya bayyana a WhatsApp ranar 28 ga watan Mayu ya ambato attajirin na cewa “Zan bude wani ofishi na iyali na a birnin New York in zuba jarin kashi 60 cikin 100 na kaddarori na a Amurka domin kare dukiyar iyali na, na wani tsawon lokaci.”

Idan aka duba abin da wannan ke nufi, sai a ga cewa wannan matakin zai yi tasiri sosai a kan tattalin arzikin Najeriya da ma Afirka baki daya idan har attajirin ya mayar da kasuwancin sa zuwa kasar Amurka.

Sunan Dangote ba boyayye bane idan aka yi la’akari da yadda kayan abinci da kamfanonin sa ke sarrafawa wanda suka karaɗe ko’ina a fadin kasar da kasashen Afirka. Kayan masarufi da kamfanin ke sarrafawa sun hada da filawa, suga, gishiri, talliya da sauran su. Lallai idan har Dangote ya cire jarin dukiyar sa da kadarorinsa a nahiyar Afrika, Nahiyar za ta afka cikin halin matsi da kakanikayi. Hakan yasa Dubawa bi diddigin wannan magana da ta yadu a yanar gizo domin bayyana sahihancin sa.

Aliko Dangote Aliko Dangote shine attajiri da yafi kowa arzikin kudi da kadarori a nahiyar Afrika.

Tantancewa

Dubawa ta fara da gudanar da bincike a shafin google inda ta gano wata hira da Dangote ya yi da wani dan jarida mai suna David Rubenstein inda ya bayyana cewa yana da ofis a birnin Landan kuma zai sake bude wani a birnin New York na Amurka.

Hirar mai tsawon mintuna 24 wanda aka saka a YouTube a watan Janairun 2020 ya nuna inda Dangote ke fadawa Rubenstein cewa yana da burin fadada kasuwancin sa zuwa wajen nahiyar Afirka amma bai ambato Amurka ba kamar yadda sakon WhatsApp din ya bayyana. A kalmominsa cewa ya yi, “Ba zamu ci gaba da tsayawa a Afirka kadai ba, za mu fadada zuwa wajen Afirka”

Yayin da yake bayani kan shirye-shiryen sa na zuba jari a wajen Afirka, ya ce a wancan lokacin, kudaden shigan kamfaninsa ya kai dala biliyan 4 kuma yana so ya habaka kudin zuwa dala biliyan 30 a cikin shekaru biyu. Daga cikin wadannan kudaden da yake hasashen samu ne zai zuba jari a wajen Afirka.

Duk da cewa ya ce kaso mai tsoka ne na dukiyar sa zai kai su kasashen da ba a Afirka ba, bai fadi yawan arzikin sa da zai saka fidda ba sannan ba ambaci kasar da zai fadada kasuwancin na sa a can ba, ya dai ce kawai zai ci gaba da fadada kasuwancin sa.

A karshe

Sabanin zaton da aka yi na cewa Dangote zai sanya kashi 60 cikin 100 na kadarorin sa a Amurka, Dubawa ta gano cewa Dangote ya ce zai kai wani kaso na kudaden sa kasashen da ba a nahiyar Afrika ba ne. Attajirin bai fadi wata kasa da yake burin zabga dukiyarsa ciki ya dai ce zai yi amfani da wani kaso mai tsoka idan wajen bunkasa kasuwancin sa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button