African LanguagesHausa

Ba kasar Saliyo ba ce kan gaba wajen tallafawa mata a duniya, kamar yadda shugaba Bio ke ikirari

Zargi: Shugaba Bio na Saliyo na zargin wai duk inda aka je a duniya Saliyo ce kan gaba wajen tallafawa mata su zama masu dogaro da kan su

Ba kasar Saliyo ba ce kan gaba wajen tallafawa mata a duniya, kamar yadda shugaba Bio ke ikirari

Duk da cewa Saliyo na samun cigaba wajen inganta rayuwar mata, ba ta kai matakin da za’a ce tana kan gaba tsakanin kasashen duniya ba

Cikakken labari

Shugaban kasar Saliyo, Birgadiya Julius Maada Bio mai ritaya, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na cika duk alakawuran da ta yi wa mutanen Moyamba.

Daya daga cikin wadannan alkawuran shi ne gina gadar Mabang wadda ta yi shekaru cikin wani yanayi na lalacewa.

Tuni aka gyara gadar kuma har an yi bukin kaddamar da ita. Lokacin bukin kaddamarwar ne shugaba Bio ya jinjinawa dangantakar da ke tsakanin gwamnatin shi da Kungiyar Tarayyar Turai, ganin yadda bangarorin biyu suka hada kai suka samar da ababen more rayuwa a duk fadin kasar.

Gadar ta Mabang mai tsawon mita 231 ta hada masarautar Ribbi a gundumar Moyamba da ke yankin kudancin kasar da masarautar Port Loko da ke yankin arewacin kasar. Hakan na da mahimmanci sosai sakamakon ayyukan tattalin arzikin da ake yi a wadannan yankunan. Shekaru taran da suka gabata gadar ta rushe kuma  sai yanzun ne aka iya gyarawa.

Lokacin kaddamarwar, shugaba Bio ya fadada bayanansa zuwa taron da aka kammala kwanan nan na UNESCO a birnin Paris, dangane da illimi, inda ya yi ikirarin cewa kasashen duniya na la’akari da Saliyo a matsayin kasar da ke kan gaba wajen ilimi. A cewarsa, gudunmawar da gwamnatinsa ta yi a fannin illimi a shekaru hudun da ya ke mulki ne ya sa UNESCO ta gayyace shi ya zama daya daga cikin masu jagorantar taron da aka yi kan illimi kuma wannan kimar da ya ke da shi a idon jama’a ne ma ya sa aka sake gayyatar sa zuwa babban taron Majalisar Dinkin Duniyar da za’a yi a watan Satumba.

Ya ce: “Ni ba mutun ne da ke saurin jin kunya ba amma na yi mamaki kwarai lokacin da shugaban UNESCO ya ce mun yana so ya kawo ziyara Saliyo ba dan ya koyar da mu ba amma dan ya koyi matakan da muka dauka duk da irin matsalolin da ke tattare da COVID-19.”

Ya kuma kara da cewa ana sanya Saliyo a matakin farko idan ya zo batun tallafawa mata 

Tantancewa

Wannan zargi na cigaban da mata ke samu a Saliyo ya zo tsakanin dakiku 0.13 -0.20 na jawabin da shugaban ya yi. Shugaban ya yi amfani da harshen Krio wanda aka fi amfani da shi a kasar a lokacin da ya ke kaddamarwar. An kuma dauki bukin a duk kafafen yada labaran kasar.

Sai dai wannan zargin da ya yi babba ne tunda ya shafi kasashen duniya baki daya, abin da ya sa DUBAWA ta yanke shawarar gudanar da bincike dan tantance gaskiyar batun, inda ta fara da suba rahoton binciken da ke duba banbancin da ke tsakanin jinsuna na 2022. Rahoton na watan Yuli wanda shi ne ya fita kwanan nan, ana iya samun shi a shafin Dandalin Tattalin Arziki na Duniya wato World Economic Forum a turance.

Ma’aunin gibin da ke tsakanin jinsi a duniya ya yi la’akari da abubuwa guda hudu ne wajen auna sauyin da ake samu a yanayin gibin da ke tsakanin jinsi a yanzu haka a cewar babban darektan da ya sanya hannu kan rahoton wati Saaida Zahidi. Wadannan abubuwa hudu suna da mahimmancin gaske a duk sadda ake batun tabbatar da ci-gaba wajen karfafa jinsi. Wadannan abubuwa sun hada da shiga ko kuma samun damar taka rawar gani a harkokin tattalin arziki, illimi, kiwon lafiya da damar shiga harkokin siyasa.

Bisa bayanan rahoton, kasashe 146 sun rufe gibin da ke tsakanin jinsi da kashi 68.1 cikin 100. Sai dai rahoton na kiyasin cewa zai dauki shekaru 132 kafin a iya daidata tsakanin jinsin. Rahoton ya kuma kasa ci-gaban da aka samu wajen daidaita tsakanin jinsin zuwa gida hudu, inda a bangaren kiwon lafiya an rufe gibin da kashi 95.8 a fanin damar samun ilimi da kashi 94 damar shiga harkokin tattalin arziki kuma kashi 60 a yayin da damar shiga siyasa kuma ya ke kan kashi 22, duk a cikin 100.

A shafi na biyar na rahoton, duk da cewa babu kasar da ta iya daidaita tsakanin jinsunan akwia kasashen da suka yi ficce saboda matakin da suka kai wajen inganta rayuwar jinsunan  kuma kasar Saliyo ba ta cikinsu kamar yadda shugaba Bio ya fada. Kasar Iceland ce ta kasnce kan gaba da kashi 90.8 cikin 100, inda ta ke biye da Finland mai kashi 86, Norway kashi 84.5. Kasashen Afirka guda biyu ne suka kasance tsakanin kasashe goma na farko wadanda suka hada da kasashen Ruwanda da Namibia.

Saliyo ta kasance a mataki na 109 tsakanin jerin kasashen duniya, a yayin da ta kasance a mataki na 22 a kasashen Afirka idan ana maganan rufe gibin da ke tsakanin jinsi da tallafi. Kasashen Afirkan da su ka yi fice wadanda kuma suka kasance a matakin biyar na farko sun hada da Rwanda, Namibia, Burundi, Mozambique da Cape Verde. Bisa wadannan bayanan, furcin shugaba Bio ba gaskiya ba ne

A Karshe

Duk da cewa Saliyo na samun cigaba a fuskar daidaita tsakanin jinsi, ba ta kai matakin da za’a ce tana jagora a tsakanin sauran kasashen duniyar da ke yunkuri a wannan fannin ba. Dan haka zargin shugaba Bio ba gaskiya ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button