African LanguagesHausa

Babu hujjar kimiyya kan ikirarin wani malami cewa kashin beraye na warkar da cututtuka

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani da ya bayyana kansa a matsayin malamin addini, ya yi ikirarin cewa kashin beraye na iya warkar da appendicitis da ƙurajen kai.

Babu hujjar kimiyya kan ikirarin wani malami cewa kashin beraye na warkar da cututtuka

Hukunci: Karya ne. Babu wani bincike ko madogara ta kimiyya ko binciken lafiya da ya goyi bayan amfani da kashin beraye a matsayin magani.

Cikakken Bayani

A ranar 4 ga Yuni, 2025, wani malamin addini mai suna Ibraheem Niass Kusfa, almajirin Sheikh Usman Kusfa Zaria, Kaduna – wanda aka fi sani da “Rigi Rigi” – ya wallafa bidiyo guda biyu (mai daƙiƙu 39 da 44) a shafin Facebook yana ikirarin cewa kashin beraye na iya warkar da cutar appendicitis da kuma ƙurajen kai.

A cikin harshen Hausa, Niass Kusfa ya yi bayanin yadda ake amfani da ƙazantar beraye wajen magance cututtuka na ciki da na jiki, yana danganta ikon warkarwar ga ikon Allah da albarkar Annabi Muhammad (SAW).

Da’awa game da Appendix

“Kashin bera na warkar da ciwon appendix. Idan ka tara kashin beraye da yawa sai ka jika a ruwa, sai ka ba wanda ke fama da appendix, za ta narke duwatsun da ke jikinsa ta fito da su ta bayan gida. Ko yara ma da suke ci abincin da ke da duwatsu suna iya amfani da shi – da ikon Allah, da albarkar Annabi Muhammad, za ta narke.”

Da’awa game da ƙurajen kai

“Ga masu ƙurajen kai, a tara kashin beraye a busar da shi a rana, a niƙa ta ta zama gari sannan a haɗa da kowace man shafawa, a shafa a kai. Da albarkar Annabi za ka warke – ko ƙuraje ne, ko pimples, ko kowace cutar gashi.”

Waɗannan ikirarin sun bazu sosai a kafafen sada zumunta, inda bidiyoyin suka samu sama da kallo 33,000 da 13,000 kowanne, har zuwa 4 ga Agusta, 2025.

Wani mai amfani da Facebook mai suna SafWan RidWan wanda ya yi tsokaci da gargadi cikin barkwanci ya ce: “Lassa fever, salamu alaikum.” 

Wasu kuma sun yi maraba da bayanin musamman maganin ƙurajen kai, inda wani Imam Hussain Rigi Rigi ya gode wa malamin: “Alhamdulillah Maulana, Allah ya saka maku da alkhairi.”

Saboda irin wannan jan hankali da bidiyon suka yi, DUBAWA ta binciki gaskiyar lamarin.

Tantancewa

Apendis ko kumburin wata cuta ce da ke faruwa yayin da wani sashe na ciki ya samu, wanda a mafi yawan lokuta ake bukatar tiyata domin a cire ta, don kauce wa fashewa. Idan ta fashe ba tare da an yi mata magani da gaggawa ba, hakan na iya haifar da mummunar illa ga rai.

Babu hujjar kimiyya kan ikirarin wani malami cewa kashin beraye na warkar da cututtuka

Hotun da ke nuna cutar apendis. Hakkin Mallaka: ALP

A gefe guda kuma, scalp acne na nufin kuraje ko kaikayin fatar kai, wanda yawanci ke faruwa sakamakon toshewar ramukan fata, yawan maski a fata, ko kuma kamuwa da cutar ƙwayoyin bacteria.

Babu hujjar kimiyya kan ikirarin wani malami cewa kashin beraye na warkar da cututtuka

Hoton da ke nuna kurajen kai. Hakkin Mallaka:Tiktok

Yayin da cutar kumburin ciki ke buƙatar kulawa ta gaggawa daga likita, ƙurajen fatar kai kuwa ana iya magance shi da kayan kula da fata ko kuma magungunan rigakafi gwargwadon yadda matsalar ta tsananta.

Shin najasar bera tana da amfani wajen maganin kumburin ciki ko kurajen kai ?

Mun gudanar da bincike ta hanyar amfani da kalmomin bincike (keyword searches) amma ba mu samu wani sahihin binciken kimiyya ba da ke goyon bayan ra’ayin cewa cin najasar bera zai iya warkar da kumburin ciki.

Mun yi nazarin matsayar kimiyya ta yanzu daga manyan cibiyoyin binciken lafiya da tiyata, irin su StatPearls, MDPI, SAGES, Mayo Clinic’, da WSES Jerusalem, amma ba mu samu wani abu da ke tabbatar da wannan ikirarin ba. Haka kuma, mun duba wasu manyan majiyoyin lafiya, kamar MedlinePlus, NHS UK da NIDDK – NIH.

A gefe guda kuma, a cewar shafin WebMD, kashin bera na da matuƙar haɗari kuma yana ɗauke da ƙwayoyin cuta masu haddasa wasu manyan cututtuka, wadanda ke yaduwa ta hanyar taba kashin beraye.

Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Amurka (CDC) ta tabbatar cewa wasu cututtuka na iya yaɗuwa daga beraye zuwa mutane ta hanyar hulɗa kai tsaye da berayen da suka kamu da cuta.

Ra’ayin Masana

DUBAWA ta tuntubi Muhammad Zainu Sabitu, ƙwararren likitan cututtuka a fannin ƙwayoyin cuta a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, wanda ya karyata ikirarin yana cewa ƙarya ne kuma abu ne mai haɗari.

“Akwai hanyoyin magani da aka tabbatar da sahihancinsu da aminci wajen magance kumburin ciki da ƙaiƙayi/ƙurajen fatar kai. Amma ba a taɓa yin gwaji ko amincewa da kashin bera don yin magani ba.” in ji shi.

Muhammad Shakir Balogun, ƙwararren likitan ƙwayoyin cuta kuma mai ba da shawara a cibiyar African Field Epidemiology Network (AFENET), ya gargadi cewa mutane na iya fuskantar haɗarin kamuwa da ƙwayoyin cuta masu haɗari ta hanyar taɓawa, shakar ƙamshi ko cin kashin bera.

Ya ce wannan kuwa sun haɗa da: kwayar Hantavirus (mai jawo cututtukan numfashi da na koda), ƙwayar Leptospira (mai lalata hanta/koda), kwayar Lassa virus (mai haddasa mummunar zazzabin jini), Salmonella, LCM virus, da sauran su.

A Karshe

Da’awar cewa amfani da kashin bera na iya warkar da kumburin ciki (appendicitis) da ƙaiƙayi/ƙurajen fatar kai (scalp acne) ƙarya ne kuma ƙwararru sun tabbatar yana da matuƙar haɗari.

Show More

Related Articles

One Comment

  1. the end of mummy water and the native son Nigeria biography life insecurity, corruption, bribery, military begged traffic, boko haram,abduction, price unconditional, all are foundation today president bola Ahmed tunibu Togo 2027 oh wohoho

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »