HausaAfrican Languages

Da’awar Facebook cewa Osimhen ya rattabawa kulob din Man United hannu ba a tantance ba 

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa claims Man United ta amince da sanya hanun Osimhen.

Da’awar Facebook cewa Osimhen ya rattabawa kulob din Man United hannu ba a tantance ba 

Hukunci: Karya ce. Osimhen a hukumance babu wani kulob da yace zai rattaba wa hannu, bai bayyana aniyarsa ba tukuna kowane kulob zai sanyawa riga a lokacin bazara. Ya dai yi bayani ne da cewa “Yana jin dadinsa a wannan lokaci” a kasar Turkiya. Kuma shima kulob din na Manchester United bai bayyana ba a hukumance cewa ya amince zai sayi danwasan dan asalin kasar Najeriya.

Cikakken Sakon

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United na bukatar dan wasa mai zura kwallaye bayan da a wasannin da ta buga a cikin gidanta ta ci kwallaye 32 ne ya zuwa yanzu,inda dan wasan kuliob din na tsakiya Bruno Fernandes ya zura kwallaye 8. Danwasan dan asalin kasar Portugal ya taka muhimmiyar rawa (impressed greatly) duk da cewa a bana ba su taka wata muhimmiyar rawa ba, ganin da kyar suka tsallake fadawa kulob din da ke kasa da matakin da suke taka leda a yanzu.

Duk da haka Kulob din na RedDevils zai so ya kara dagowa daga inda yake, bukatar ya zuba sabbin ‘yankwallo shi ya kamata ya zama abin da kulob din ya sanya a gaba. Kulob din na dogara da ‘yanwasan gaba Alejandro Garnacho da Rasmus Hojlund wadanda gaba dayansu suka ci kwalllaye takwas. Amad Diallo, dan shekaru  22 da a bana ya taka muhimmiyar rawa da cin kwallaye shida, ya samu jin ciwo a agararsa tun a watan Fabrairu kuma an ajiye shi gefe tun daga wancan lokaci. Shi kuwa Joshua Zirkzee, da aka siye shi a kan kudi Euro miliyan 36.5 gabanin kakar wasa ta shekarar 2024/2025.  

Ana tsaka da wannan takaddama kan yadda za a warware halin da Man United ke cikin , sai ga wani mai amfani da shafin na Facebook na wannan da’awa Man United News Today, cewa Man United ta amince da sanya hannun dan wasan Napoli da aka ba da shi bashi Victor Osimhen. 

“A karshe Man United ta amince Victor Osimhen zai sa mata hannu daga Napoli.” kamar yadda wani bangare na bayanan na Facebook ke cewa.

Ya zuwa ranar Litinin 14 ga watan Afrilu, 2025 wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu su 456 kana akwai mutum daya da ya sake yada wannan wallafa.

Wasu daga cikin masu amfani da shafin na Facebook sun dagawa wallafar hannu suka nuna amincewarsu yayin da wasu kuma ke nuna tantama.

“Man Utd ya kamata ta nemi ‘yanwasan gaba da suka kware wajen taka leda su dena neman VO,” a martanin Sunday Makinde.

“Shin Man UTD tana sane da wannan?” Jude Ejior Adagwa ya kalubalanci wallafar.

“Abubuwa za su iya gyaruwa !’’ a cewar Andy Crowther.

DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike don tabbatar da ingancin wannan da’awa don kaucewa yada labaran karya ko wane iri ne. 

Tantancewa

DUBAWA ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ta nemi ganin wannan labari a Google sai dai bata samu wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da rahoton ba da aka wallafa a Facebook. Har ila yau mun kuma duba shafin Man United website anan ma babu wani labarai da kuluob din ya wallafa a dangane da haka.

Sanarwa ta baya-baya da aka wallafa kan musayar ‘yanwasa (Football Transfers ) inda aka bayyana ta “yanwasa da aka ba da su bashi a Napoli, a rahoton da aka wallafa Osimhen ana alakanta shi da gasar ta Premier League a matsayin dan wasan kasa da kasa daga Najeriya wanda a yanzu ke muradin wasanninsa a kulob a Turkiya na Galatasary. 

A wannan wallafa ta bayanan musayar ‘yanwasan Football Transfers ta rawaito Osimhen na bayyana cewa “Galatasary a ko da yaushe yana cikin zuciya ta.”

“A ko da yaushe ana rade-radi a kai na; Ina ganin kawo yanzu ina jin dadin halin da nake ciki; magoya baya na bani karfin gwiwa, a wannan lokaci matsaya mafiya kyau za a bayyanata ”a cewar Osimhen a tattaunawa da NTV.

Ko da yake kulob din na Galatasaray na iya zabar siyan dan wasan gaban, idan zai ajiye Euro miliyan 75 da ake bukata kafin sakinsa da biyan Euro miliyan 11 duk shekara a matsayin albashi kudin da ake ganin suna da yawan gaske ga kulob din.

Har ila yau wata kafar yada labaran wasanni a Turkiya Haber Sarikirmizi ta ba da rahoto a ranar Lahadi 13 ga watan Afrilu,2025 cewa Osimhen zai iya tafiya Bercelona (Inda aka yi hasashen cewa zai maye gurbin Robert Lewandowski) ko ya tafi jagora a Serea A a Juventus amma babu wani bayani da ya fita a hukumance.

A Karshe

Da’awar karya ce, dan Najeriyan da ke taka leda tsakanin kasa da kasa bai bayyana a hukumance ba, kan kulob din da zai tafi a lokacin bazara, haka nan ita ma Manchester United bata yi wani jawabi ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »