African LanguagesHausa

Babu hujjar wai  Akpabio ya ce majalisar dattawa za ta “amince da shirin” sayen sabon jirgin sama wa shugaban kasa

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai shafin X na da’awar wa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya ce za su amince da shirin sayen sabon jirgin saman da shugaban kasa zai rika hawa duk da halin yunwar da ‘yan Najeriya ke ciki.

Babu hujjar wai  Akpabio ya ce majalisar dattawa za ta “amince da shirin” sayen sabon jirgin sama wa shugaban kasa

Hukunci: Karya ce! Babu hujjar wai  Akpabio ya ce majalisar dattawa za ta amince da shirin sayen sabon jirgin sama wa shugaban kasa

Cikakken bayani 

A ‘yan shekarun baya-bayan nan, ‘yan Najeriya sun yi fama da kuncin rayuwa, hade da talauci, da rashin tsaro da kuma tattalin arzikin da ke fuskantar koma baya. Haka ne ma ya sa furucin da wasu ‘yan siyasar Najeriya suka yi ya gamu da ashar, inda wasu ke zargin gwamnati da rashin tunani da ma rashin sanin abubuwan da ‘yan Najeriya ke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullun.

Kwanan nan cikin watan Yunin 2024, wani kwamiti a majalisar wakilan kasar ta bukaci gwamnatin tarayya ta saui sabbin jiragen sama wa shugaban kasa da mataimakin sa. A cewar kwamitin, sayen jiragen abu ne da zai taimakawa kasar wajen kaucewa daga wani abun da ba’a shiyawa ba saboda yadda jiragen tafiyar shugaban kasar ba su aiki.

Manuan ‘yan Najeriya da kungiyoyi sun yi watsi da wannan zancen na sayen sabon jirgin sama wa shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima duk da irin koma bayan da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.

Yayin da ake cigaba da mahawarori dangane da wannan batun, ranar 22 ga watan Yunin 2024, wani mai amfani da shafin X, Franklin Ekechukwu, ya wallafa wani bayanin da ke da’awar cewa shugaban majalisar dattawa ya nuna alamun za su amince da sayen sabbin jiragen sama wa shugaban kasa tunda nasa na yanzu na fuskantar matsaloli. Bayanin na cewa:

“Muna sane da cewa ‘yan Najeriya na jin yunwa, amma hakan ba zai hana my sayawa shugaban kasa jirgin sama ba. Rayuwarsa ya fi na ‘yan kasa mahimmanci a wurinmy. Dole mu saya jirgin nan ba da dadewa ba — Godswill Akpabio, wani irin cin fuska da rashin mutunci ne wannan!”
Da muka duba ranar 26 ga watan Yunin 2024, labarin ya sami baki sau 713,000, ya kuma sami alamar like 4,900, an sake rabawa 3,800 sa’annan akwai tsokaci 2,900 a kan shafukan soshiyal mediya.

Bacin haka ya kyma sami martani daga masu amfani da shafukan wadanda suka nuna rashin yarda da ma dai fushinsu dangane da batun.

Wani mai amfani da shafin da sunan @addel_cares, ya rubuta: “Idan dai da gaske ne ya fadi haka, ya nuna cewa ‘yan Najeriya sun cancanci irin wannan shugabancin saboda mutun irin wannan bai ma kamata ya na rike da irin wannan mukamin ba.” 

Yayin da shi kuma @mavisikpeme ya rubuta “Da ya ke na san yadda ya ke magana, lallai ya fadi hakan da ma fiye. Ubangiji ya taimake mu.”

Wani shi ma mai amfani da shafin, @emrayiam, mamaki abun ya ba shi: “Idan ba wai an kawo bidiyo an nuna mun shi a matsayin hujja, ya na fadar wannan maganan ba, a halin yanzu, ba zan taba yardar cewa ya fadi wannan maganar ba.”

Da muka ga irin wadannan mahawarorin da yadda batun ke daukar hankali, DUBAWA ta yanke shawarar tantance sahihancin labarin.

Tantancewa

DUBAWA ta tuntubi Mr Franklin wanda ya wallafa wannan da’awar a shafin shi na X ta ce masa ya turo hujjar da ya ke da shi na cewa Akpabio ya yi wannan bayanin, sai dai bai amsa ba har zuwa lokacin da muka buga wannan labarin.

Mun kuma gudanar da bincike a shafin Google dan gano ko da akwai wani rahoton da ke dauki da wannan furucin da ake zargin Mr Akpabio ya yi na cewa za su ba da amincewarsu a saya shugaban kasa da mataimakinsa jirgin sama. Amma duk da haka ba mu ga wtaa kafar yada labarai mai sahihancin da ta dauki batun ba. A maimakon haka sai dai muka ga wata hira da manema labarai a ranar 24 ga watan Yuni, inda ya ce jita-jita aikin masu nemna tayar da zaune tsaye ne kawai.

“Ban taba fadin haka ba. Ina Zanzibar na kasar Tanzania. Dan haka wannan aiki ne na ‘yan farfaganda da mutanen da ba su ganin duk wani abin kirkin da muke yi. Ku kwantar da hankalinku kawai, ku yi wa gwamnati addu’a ku yi hakuri ku kuma tabbata cewa da Tinubu da Shettima za su kawo mana arziki a kasar nan,” a cewar Mr Akpabio.

A karshe  

Bacin kuncin rayuwar da Najeriya ke fama da shi, babu wata hujjar da ta goyi bayan furucin da ake da’awar Mr Akpabio ya yi kan cewa majalisar dattawa za ta amince da sayen jirgin sama. Wannan da’awar karya ce kawai.

Wannan rahoto an fitar da shi ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararrun masu gano gaskiya labari na Kwame Karikari da hadin giwa da Diamond 88.5 FM Nigeria a kokarin da ake yi na mutunta fadin gaskiya a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »