African LanguagesHausa

Bayanai na yaudara da suka mamaye lokutan zabe a Afurka ta Yamma a 2023

Getting your Trinity Audio player ready...

Shekarar 2023 ta zo da sauye-sauyen shugabanci a wasu kasashe na Afurka ta Yamma ga mkisali Najeriya da Laberiya da Saliyo. Kamr yadda aka yi tsammani an rika samun bayanai masu karo da juna da sauka daga kan layi inda aka rika sadar da bayanai marasa inganci ga al’ummar wannan nahiya.

A Najeriya bayanai da suka dabaibaye zaben shugaban kasa da gwamnoni da wasu zabuka da suka saba lokutan sauran zabuka a Najeriyar mambobi na gamayyar masu bin kwakwkwafi ciki kuwa har da na DUBAWA sun bibiyi lamuran da suka faru.

Wadannan na daga cikin labaran da DUBAWA ta lura da su a lokacin zabukan da aka gudanar da Afurka ta Yamma ba tare da ware wata kasa ba.

Barazanar karya ta tashin hankali a lokacin zabukan

A lokutan  zabuka a kasashen uku, ewasu sun yin da’awar cewa an samu ko za a samu wasu tashe-tashen hankula a wasu yankunan.Ganin alamu na cewa irin wannan da’awa na iya haifar da fargaba ko yana iya hana fitowar masu zabe. DUBAWA ta gudanar da bincike.

Sojoji ba su karbi mulkin Saliyo ba bayan sa’oi 24 na gudanar da zabe

Kafin zaben da aka yi a kasar Saliyo akwai wani hoton bidiyo da yayi shuhura inda aka ga wani mutum sanye da kayan sojoji yana cewa muddin ba a yi zabe mai adalci ba a Saliyo dakarunsa za su karbi mulkin kasar bayan sa’oi 24.

A lokacin da DUBAWA ya lura da shafin da aka wallafa wannan bidiyo ta gano cewa ba shi da wani jogo da zai sa ya zama barazana. Ana iya karantawa a nan ( here.) 

A Najeriya ma Dubawa ya gano  da’awar samar da tashin hankali da ta zo a karyar cewa ‘yanta’adda za su kai farmaki a kan ‘yantakara ko wakilan jam’iyya. 

A lokacin zaben gwamna a watan Maris shekarar 2023 a jihar Legas, akwai wani hotin bidiyo da ya nunar wai Olumide Oworu na jam’iyyar Labour da ke neman kujerar danmajalisa fuskar da jini da aka ce ‘yandaba ne da ‘yan jam’iyyar APC ta dauki nauyinsu suka kai masa farmaki. An gudanar da bincike kan wannan da’awa  (fact-checked,) an kuma gano cewa hoton daga wani shirin fim ne.

KARYA NE ! BA A YI GARKUWA DA Pat Utomi BA 

Har ila yau a lokacin zaben shugaban kasa, wata da’awar ta nuna wani hoton Farfesa Pat Utomi jagora na jam’iyyar Labour ‘yan daba sun yi garkuwa da shi a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Victoria Island a jihar Legas.

Hadakar masu binciken kwakwaf ta gano cewa wannan labari karya ne bayan da ta tuntubi mai magana da yawun jam’iyyar ta Labour Yunusa Tanko, shima Farfesa Utomi ya tabbatar da cewa “yana lafiya” ya bayyana labarin da zama shafcin gizo (false.) 

Karya ne! Boko Haram ba ta kwace ofishin INEC ba a Kaduna da Kano

Also, during Nigeria’s general elections, some social media users claimed members of the deadly Boko Haram sect attacked offices of the Independent National Electoral Commission (INEC) in Kano and Kaduna states. Kazalika a lokacin babban zaben Najeriya wasu shafukan a dandalin sada zumunta sun yi da’awar kunmgiyar Boko Haram ta kai farmaki a ofishin Hukumar Zabe mai Zaman kanta INEC a Kano da Kaduna. Rundunar ‘yansanda a jihohin biyu sun karyata (debunked) wadannan da’awowi.

Zabin Kabila ko Addini

DUBAWA ya kuma gano yadda maso yada labaran karya ke amfani da kabilanci ko addini don cimma manufarsu kan masu bin wani bangare na addini ko wata kabila, a wasu lokutan su yi amfani da hakan don bata wasu ‘yantakara. An ga wannan rawar a Najeriya da Laberiya. 

Gabanin kammala zaben  kasar Laberiya shafin farko na jaridar Front Page Africa da New Republic Newspaper an rubuta “Babu sauran gurbi ga Musulmi” da kuma “Babu Musulmi da zai yi Aiki a Gwamnatina” a babban shafi na farkon jaridun abin da ake cewa  Amb—Joseph Boakai jagoran adawa ne ya bayyana haka, abin da zai iya sadar da cewa Boakai idan ya kai ga mulki ba zai tafi da Musulmi ba.

DUBAWA ya duba fact-checked da’awar ya kuma gano cewa hotunan da aka nuna a jaridun dabaru kawai aka yi aka makala su a wadannan manyan jaridu domin babu irin wannan rubutu a shafukan jaridun da suka fita kasuwa.

Binciken Kwakwaf: Shin malamin addinin Islama a Kano ya bayyana kisan mabiya addinin Kirista a kudancin Kaduna a matsayin “Gargadi ga wadanda ba Musulmi ba?”

A Najeriya an ga irin wannan yayin da ake tunkarar zaben shugaban kasa. Wani bidiyo ya bayyana ta kafar intanet inda aka nuna wani malamin addinin Islama a harshen Hausa yana wa’azi ga magiya bayansa inda yake nuna masu cewa kisan da aka yi wa mabiuya addinin Kirista a Kaduna “Garagadi ne ga wadanda ba Musulmi ba” Yadda da dama masu amfani da kafafan yada labaran shafukan sada zumunta suka dauki labarin kenan.

DUBAWA ya tuntubi mai fassarar harshen na Hausa wanda ya fasara abin da malamin ke fadi. Ya kuma bayyana cewa an kawar da sakon da malamin ke son fada a sakonsa. Ma’ana ba haka yake nufi ba.

Lauyoyin da ke tawagar Peter Obi ba kabilar Igbo bane kadai kamar yadda wasu masu amfani da shafin Twitter suka nunar.

A wani labarin yaudarar da ke da alaka da zabe, wasu da ke amfani da shafukan sada zumunta sun bayyana cewa duk ‘yantawagar lauyoyi da ke bin shari’ar Peter Obi na jam’iyyar LP da yayi takarar shugabancin Najeriya dukkansu al’ummar Igbo ne.  

DUBAWA ya gudanar da bincike (research) inda ya gano cewa lauyoyin sun fito daga sassa daban-daban na Najeriya da suka hadar da na kabilar ta Igbo. Kuma tawagar lauyoyin sun banbanta da na Nnamdi Kanu.

Dagi ko zayyana da ke hular Tinubu ba ta da wata alaka da kungiyar asiri ta Ouroboros

A wannan gaba wasu da ke amfani da shafukan sada zumunta sun alakanta zanen zayyana da ke jikin hular Shugaba Tinubu da kungiyar asiri . A wani rahoto na BBC a 2017 ya nuna tarihin wannan alama da cewa tun daga asalin Turawan Girka da Misirawa, abin da a takaice ke nuna yadda rayuwa ke zagayawa daga haihuwa har zuwa mutuwa dama sake tasowa.

Binciken da aka ci gaba ya gano cewa alamar da ke jikin hular shugaban kasa ba ta da wata alaka da ta kungiyar asirin ta ( Ouroboros occult vector symbol); ya bayyana a wata tattaunawa da aka yi da shi inda yace alama ce ta “sarkar da ta tsince” abin da ke nuna alamar samun ‘yanci. Ana iya kara nazari (here.) 

Sanarwar karya da Jawabin karya

A lokutan zabe abu ne sananne a rika samun sanarwar karya a shafukan sada zumunta wadanda ke nuna cewa wani dantakara ya ajiye takararsa ko wata jam’iyya ta janye wani dantakara. A wasu lokutan ma har ana iya jin cewa wani dantakara ya rasu ko ace an soke zabe a wasu yankuna. Wadannan kadan ne daga cikin irin wadanda DUBAWA ya nazarta a zaben 2023.

A safiyar ranar zaben gwamna 18 ga Maris, 2023 a jihar Legas akwai sakoni da suka karade shafukan sada zumunta suna cewa jam’iyyar PDP ta karbi Gbadebo Rhodes-Vivour na jam’iyyar Labour a matsayin dantakararta. Ba da dadewa ba jam’iyyar PDP ta fito ta karyata (debunked) wannan da’awa.

A watan Nuwamba 2023 a lokutan zabukan zabukan jihohin Kogi da Imo da ke zama ba gama gari ba a Najeriyar , an rika samun da’awa daban-daban ko dai ace dantakara ya amince da wani ko ya janye daga takararsa.

Dantakarar gwamnan jam’iyyar PDP Dino Malaye yayi da’awar jam’iyyar LP ta amince da shi a matsayin dantakararta. Amma rahoton bincike (fact-check) namu ya nunar da cewa da’awar karya ce. 

Wani bidiyo da yayi shuhura a shafukan intanet yayi da’awar cewa dantakarar jam’iyyar PDP Sanata Samuel Anyanwu ya janye daga takararsa  ya kuma umarci magoya bayansa da su mara baya ga dantakarar jam’iyyar All Progressives Congress, Hope Uzodinma. Nazari  (analysis) da aka yi a kan bidiyon ya nunar da cewa karya ne.

A Laberiya wasu rahotanni da jawaban kafafan yada labarai sun nunar da cewa tsohon shugaban kasa George Weah ya samu goyon bayan ‘yanmajalisa 56 ciki kuwa har da Thomas Goshua da Grand Bassa wakilin lardi na #5 don ya sake neman kujerar mulkin kasar.

A cikin jerin sunayen da mai da’awar ya fitar 49 ne kacal na ‘yanmajalisar suka amince da Weah, yayin da Mista Goshua ya nuna kin amincewarsa na goyon bayan shugaban a wancan lokaci. Ana iya kara nazari (Read here.)

Har ila yau a kasar ta Laberiya, a wani shafi yayi da’awar cewa Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna goyon bayanta ga Joseph Boakai gabanin kammala zaben kasaer. Anan ma Kungiyar ta EU ta karyata (debunked) da’awar.

Za a iya ganin irin wadannan da’awa idan aka latsa nan here, da here da here

Idan muka koma Najeriya bayan zaben shugaban kasa na 2023 wasu al’ummar kasar sun zaga aminta da sakamakon da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta INEC ta bayyana, wannan ya sanya kokonto a zukatan wasu ‘yankasar.

Wasu da ke amfani da shafukan sada zumunta sun rika yayata bayanan cewa Peter Obi na jam’iyyar Labour ne yayi nasara a zaben sabanin Bola Tinubu da hukumar ta INEC ta bayyana, A cewarsu sakamako da na’urar IReV ta nunar ya nuna cewa Mista Obi shike da rinjaye na samun jihohi 19 na kasar.

Lokacin da shafin na DUBAWA yayi nazari kan shafin IReV ya ga cewa ba a kammala sanya sakamakon jihohin ba baki daya, kuma hoton da ke makale da bayanan an samo shi ne daga sakamakon jin ra’ayi da shafin Nextier yayi a ranar 27 ga watan Janairu , 2023. Ana kara iya nazari anan (here.)

Har ila yau a shafukan na sada zumunta an ga yadda aka wallafa labari da aka ce ya fito daga Kamfanin Dillancin Labarai na AP wanda ya nuna cewa Shugaban Amurka Joe Biden yayi kira da a soke zaben shugaban Najeriya 2023.  A bincike da muka gudanar ya nunar da cewa hoto da aka makala a shafin na AP dabaru ne kawai domin idan ka ziyarci hakikanin shafin na AP babu wannan labari.

Karairayi da aka yi wa hukumomin zabe A kwai labarai da aka rika sanya ayyukan hukumomin zaben Afurka ta Yamma a kan A kasar Laberiya ga misali akwai jaridar da ta wallafa labari cewa Hukumar Zabe ta Kasar ta soke kuri’u 27,000, amma bincikenmu (findings) ya nunar da cewa hukumar ta NEC ta cire kuri’u da aka maimaita sasu guda 27,192 , ba wai hukumar ta soke kuri’u 27,000 ba. 

Akwai wata da’awar mai kama da wannan a Najeriya da za a iya ganin anan (here.) 

A kasar Saliyo a kwai wata da’awa da ta yi shuhura cewa hukumar zaben kasar na yi wa kananan yara rijista , sai dai bincike (findings ) ya gano cewa hotunan da aka makala kan labarin ‘yandabaru ne kawai na masu kwarewa a harkar dora hotuna, ba haka lamarin yake ba. 

A Najeriya wani mai amfani da shafin kafar sadarwar zamani yayi da’awar cewa Mahmood Yakubu shugaban Hukumar Zane mai Zaman Kanta (INEC) an garzaya da shi kotu bayan da ya bayyana sakamakon wasu tashoshin kada kuri’a 18,088 da karin wasu 20,000 don tallafawa dantaarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu 

Binciken (Findings) DUBAWA ya gano cewa shugaban hukumar ta INEC bai bayyana sakamako mara inganci, kuma a wajen sauraren karar ma wakilta aka yi.

DUBAWA ya gano cewa sakamakon da Labour Party ta kawo ne ma ke da alamar tambaya bayan nazari kan sakamako da IReV ta fitar daga mazabu 18,088 wanda ta gabatar a gaban kotu a matsayin sheda.

Wasu daga cikin da’awowin da ke zama fitattu sune gabatar da takardar zabe da ba a yi mata maki ba jami’an INEC sun  kaita wurin kada kuri’a . An gudanar da bincike kan wadannan a nan (here) da nan (here.)

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button