|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa : Wani mai amfani da shafin Facebook, Israel Mossad, ya yada wani bidiyo da ya nuna wasu sanye da kayan sarki da mutane da aka kama, inda aka nuna cewa mabiya addinin Kirista ne da ake wahalarwa a Najeriya, a cikin al’amuran da suka shafi christians in nigeria.

Hukunci: Karya ce. Wannan bidiyo tsoho ne ba shi da wata alaka da batun “gallazawa mabiya addinin Kirista” kamar yadda ake ikirari.
Cikakken Labarin
Wannan labarin yana duba batutuwan da suka shafi christians in nigeria a halin yanzu da kuma tarihin su a Najeriya.
A ranar 20 ga watan Afrilu,2026 wani mai amfani da shafin Facebook Israel Mossad, ya yada wani bidiyo kamar yadda ake gani a nan inda aka nuna mutane dauke da bindigogi suna tsare da mutane. Israel yayi da’awa cewa bidiyon ya nuna yadda mabiya addinin Kirista suke fuskantar gallazawa a Najeriya.
Taken labarin ya nuna cewa “Mabiya addinin Kirista na fuskantar gallazawa a Najeriya, Allah Ya tsare su ya nuna masu mafita ta yadda za mu kawo karshen wa’adin ‘yanta’adda.”
Ya zuwa ranar 20 ga watan Afrilu,2026 wannan bidiyo ya samu mutane da suka kalla su 184,000 (views), da masu nuna sha’awa 3,400 (likes), da masu tsokaci 1,600 (comments) da sama da mutane 1,500 wadanda suka yada (shares).
Wannan wallafa har ila yau ta haifar da martani mai taba zuciya, daya daga cikin masu amfani da shafin Alkebulan Pple ya rubuta cewa, “Ina makomar Kirista a Lebanon da Palestine?””
Shi kuwa Zoe Consults,yayi tambaya ne da cewa “Suna sanye da kakin soja me hakan ke nufi ne?”
Romanus Okafor yayi nasa martanin ne da cewa, “Amurka da Isra’ila su kawo mana dauki don tseratar da rayukanmu.”
Haka kuma , Olajide Matthew Olusegun ya bayyana damuwarsa ne da cewa , “bani da kalmar da zance ina rokon Allah Ya kawo mana dauki a Najeriya Kirista da Kiristanci na bukatar kawo dauki.”
Kayormi Seed ya yi tsokaci ne da cewa suma Kiristan basu kai nasu farmakin?
Wannan wallafa dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yada da’awa kala-kala cewa kafafan sadarwar zamani na ba da labaran cewa Kirista na fuskantar kisan kiyashi a Najeriya. Wannan ya sanya ya zama dole mahukunta su tabbatar da sahihancin wannan bidiyo da abubuwan da ke tattare da shi.
Tantancewa
DUBAWA ta hanyar amfani da dabarun gano asalin bidiyo ta gano cewa wannan bidiyo tsoho ne, mun duba inda muka ga wannan bidiyo an taba sa shi a Magic FM, Aba, a watan Yuni,2023. An ce bidiyo ne na wasu kauyawa da ‘yanta’adda suka kama a jihar Niger.
A cewar sakon da kafar yada labaran ta Magic FM Aba, ta wallafa ta ce
Mutanen da aka kama an kama su a Kafin Koro da Kwagana a karamar hukumar Paikoro a jihar Niger inda suke barazanar cewa za su kashe mutanen idan ba a biya kudin fansa ba.
Da aka kara matsawa da bincike an kuma ganin wannan bidiyo an wallafa shi a shafin Linda Ikeji’s Blog da Tori News a watan Yuni,2023 wadanda dukkaninsu sun bayyana cewa ‘yanfashin daji ne suka kai farmaki inda kuma suka yi garkuwa da mutane a kauyikan Kafin Koro da Kwagana a karamar hukumar Paikoro a jihar Niger.
Babu wata sheda da ta nuna cewa wannan bidiyo a baya-bayan nan aka yi shi, ko ya nuna cewa farmaki ne aka kaiwa mabiya addinin Kirista kamar yadda mai da’awa ke ikirari.
A Karshe
Da’awar karya ce kasancewar bidiyon tsohon bidiyo ne wanda bashi da alaka da batun da ake magana. Bidiyon ya nuna farmaki ne da aka kai a 2023 a jihar Niger, ba abu ne da aka yi a baya-bayan nan ba me alaka da addini da ake gallazawa wasu.
