African LanguagesHausa

Bidiyon karya da yayi shuhura cewa mutanen da aka yi wa rigakafi sun zama haja ya sake bayyana WhatsApp

Da’awa: Kotun kolin Amurka ta fitar da hukunci cewa mutanen da aka yi wa allurar rigakafi da kwayoyin halitta da aka jirkita na mRNAs a fadin duniya, sun zama haja (kayayyaki).

Sakamakon bincike: KARYA NE. Hukuncin kotun kolin Amurka da aka fitar 2013, ya nunar da cewa kirkirarriyar kwayar halitar DNA (cDNA) abu ne da ke da hakkin mallaka, sabanin kwayar halitta ta asali daga Allah (DNA). Wannan hukunci ba shi da alaka da mutanen da aka yi wa rigakafi da mRNAs. 

Cikakken Sako

Kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nunar allurar rigakafi ba ta da illa tana kuma da sauki, hanya ce ta samar da kariya ga dan’Adam daga cutittika masu hadari kafin su kama mutum. Allurar rigakafi na nuna turjiya daga wasu cutittika na musamman da ka iya kama mutum su ba shi garkuwa da za ta yi yaki da cutar.

Lokaci mai tsawo allurai sun samu (evolved) bayan da mutane suka rika samun cutar kyanda (smallpox) a karni na 15 har zuwa yanzu da ake samun allurai na kwayoyin halitta na (Deoxyribonucleic acid (DNA) da Ribonucleic acid (RNA)).

Alluran kwayoyin halittar DNA da RNA kan yi amfani da wasu kayayyaki na halitta (use genetic material) ya sadar da bayanai zuwa kwayoyin halittar jikin dan’Adam, abin da ke taso da garkuwar jiki ta yi aikinta. A baya-bayan nan wata mata ta fito tana da’awa  kala-kala kan mutane da aka yi wa allurar rigakafi da irin hakkin da suke da shi, kuma bidiyonta ya yadu kamar wutar daji a shafukan WhatsApp.

Tace tun daga shekarar 2013, duk mutanen da aka yi wa alluran rigakafi da kwayoyin halitta da aka jirkita na (mRNAs)  a tsarin doka su ba mutum ba ba gawa ba (Transhuman). Wannan na nufin ba za su ci moriya ba ta duk abin da ake wa mutane ko hakkinsu a kasa.

“A Amurka, Kotun Koli ta fitar da hukunci cewa duk mutanen da aka yiwa allurar rigakafi sun zama haja (kayyaki) da hakkin mallaka a kansu, karkashin dokar Amurka wacce ke tantance mutanen da aka yi wa allurar rigakafi.”

”Ba su cika ka’idar zama mutane ba, a takaice dai ana nufin mutanen da aka yi wa allurar rigakafin ba a  daukarsu mutane a dokar kasa ko ta kasa da kasa.”

Duba da yadda ake ta ci gaba da shela da gangami na wayar da kan jama’a kan yaki da nau’ikan cutika daban-daban, irin wannan da’awa na iya zama babbar barazana ga lafiyar al’umma, kasancewar tana iya sawa mutane su kauracewa zuwa alluran rigakafi. Hakan yasa dole a tantance wannan da’awa.

Tantancewa

Da aka zurfafa bincike ta hanyar amfani da (Google search) da aka sanya wasu muhimman kalmomi an gano wata wallafa ta Europe Renaissance da aka yi a 2021 mai lakabin (“Vaccinated Humans are Legally Patented State-Owned Properties No Longer Subject to Human Rights,”) Wannan wallafa ta yi daidai da abin da ke a bidiyon wannan mata.

Kalmomin da aka yi amfani da su sun kuma kai ga gano wasu bincike-bincike na  kafofin yada labaran Reuters, USA Today, da AP News, dukkaninsu sun yi watsi da da’awar da suka ce ba a fahimci hukuncin da kotun kolin ta yi ba a shekarar 2013, wacce kacokan ta mayar da hankali kan wasu kwayoyin halitta da ke kara bazanar haifar da cutar dajin mama da mahaifa.

Public Health Communications Collaborative itama ta karyata da’awar inda ta kafa hujja da wadannan jerin bincike da aka yi a sama.

Me hukuncin na 2013 ke cewa ne?

Kotun kolin Amurka a 2013 ta fitar da hukunci kan hakkin mallaka na wasu gwaje-gwaje da aka yi kan kwayoyin halitta da ke kara barazanar kamuwa ta cutar sankara ko dajin mama da sankarar mahaifa. Wannan hakkin mallaka ya ba wa kamfanin dama shi kadai yayi gwaji da zai ba da dama ta ware kwayoyin halittar DNA na gaskiya da makwafinsa (complementary DNA (cDNA) ) wanda yayi kama da na gaskiyar da dan banbanci kadan.

Za’a iya ganin hukunci na ( Association for Molecular Pathology et .V. Myriad Genetics Inc et al. anan (here.) 

Hukuncin Kotun ya bayyana cewa kwayoyin halitta da aka samar ta hanyar bincike (cDNA) na da hakkin mallaka sabanin DNA na halittar gaskiya.

Labaru daga(news article by CBC News,) sun nunar da cewa kwararrun sun yi amanna cewa hukuncin zai taimaka wajen kula da marasa lafiya inda ma ya dauko jawabin  Clarence Thomas wanda shine ma ya rubuta hukuncin hadakar alkalan kotun.

“Mun amince cewa kwayoyin halitta DNA da suka samu daga Allah, abu ne da Shi yayi su, babu wanda zai ce nasa ne saboda daban suke.”

Mene ne patent?

Abin da ake nufi da  patent kalmar Turanci ce wacce ke nufin  wani hakkin mallaka ne da ake ba wa abin da wani ya kirkiro a kokari na samo sabbin dabaru na kawo mafita ko warware wata matsala.

Shi (patent) wani hakki ne da ake ba wa wanda yayi kirkirar (right granted to an inventor), gwamnatin tarayya ke ba da damar ga wanda yayi kirkirar shi kadai. 

Ofishin da ke ba da hakkin na mallaka  (US State Patent and Trademark Office (USPTO ) na da wasu tsare-tsare da ka’idoji (breakdown guiding inventors ) kan hakkokin mallaka daban-daban da yadda ake cike takardun nemansu.

A karshe

Da’awar da aka yi kan hukuncin Kotun Kolin Amurka a 2013 cewa duk mutanen da aka yi wa allurar rigakafi sun zama haja (kayayyaki) karya ne. Kotun tace ne kwayoyin halittar (cDNA) da aka kirkira a dakin gwaje-gwaje na da hakkin mallakar wanda yayi shi sabanin DNA na gaskiyar hallitta. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button