African LanguagesHausa

Bidiyon TikTok da ke nuna Haaland na nadamar tsawaita kwantiragunsa kwaskwarima ce  

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin TikTok yayi da’awa (claims) cewa danwasan gaba na Man City Haaland, yayi nadamar tsawaita kwantiraginsa da kulob din. 

Bidiyon TikTok da ke nuna Haaland na nadamar tsawaita kwantiragunsa kwaskwarima ce  

Hukunci: Karya ce. Bincike ya gano wannan bidiyo kwaskwarima ce aka yi masa daga asalin bidiyon da kafar yada labarai ta Sky News ta wallafa, inda a tattaunawa da Haaland a Man City ake tambayarsa a dangane da zargin rashin mutunta dokokin kudi da suka shafi gasar ta firemiya.

Cikakken Sako

A ranar 17 ga watan Janairu, 2025 dan wasan gaba na Manchester City kuma dan wasan gaba na kasar Norway  Erling Haaland, ya faranta rai na tarin masoya bayan da ya amince da tsawaita kwantiraginsa da shekaru tara da rabi (agreed to a nine-and-a-half-year contract extension) da babban kulob din da yake takawa leda. 

An shuga yanayi na kila-wa-kala (uncertainty grew) a karshen shekarar bara kan cewa ko dan wasan da ya lashe lambar Ballon d’Or ta danwasa da ya fi iya murza leda a 2023 ko zai ci gaba da zaman a wannan kulob da yayi nasarar lashe gasar firemiya tsawon shekaru takwas.

Bayan ya amince da ci gaba da zama a kulob din na Etihad wanda ke nuna cewa ya kama hanyar zama mafi dadewa (the longest ever witnessed in the English league,) mai amfani da shafin na TikTok thedangerousai, yayi da’awar cewa dan wasan dan asalin kasar Norway ana zargin yayi danasanin kulla yarjejeniyar.

Haaland, a wannan bidiyo mai tsawon dakika 19, an yi zargin yayi nadamar sanya hannu na tsawaita kwantiraginsa inda ya nuna da cewa kaddara ce, yayi ne cikin yanayi na maye. Har ma ya nuna cewa ta yiwu ma kulob din ya gaza nasara kamar kulob din da ke London ta Arewa wato Arsenal.

“Na yi takaici na sanya hannu na tsawaita wa’adi, wannan bai rasa nasaba da rashin lafiyar da na yi a makon jiya, ban san mai nake tunani ba, Ina zaton biyo bayan maye da na shiga ne na sanya hannu.” Kamar yadda ake zargin Haaland ya bayyana. 

“Za mu ci gaba da fafatawa ne, muna fafatawa, ina fargaba za mu iya zama Arsenal 2.0,” ya kara da cewa.

Ya zuwa ranar Litinin 27 ga Janairu, 2025 wannan bidiyo da aka sanya a shafin TikTok ya samu wadanda suka nuna sha’awarsu 7,986 Likes da wadanda suka yi tsokaci 39 (comments), da masu nuna alamar za su sake karantawa 431 (bookmarks) da wadanda ke sake yadawa (797) shares.

A shashin tsokaci wasu daga cikin masu martani a shafin na TikTok suna nuna shakku kan wannan bidiyo inda suke nuna cewa ba na gaskiya ba ne, wasun kuwa na nuna cewa sun amince da shi.

“Hadarin amfani da  AI.” abin da Isaac Nhassengo ya bayyana kenan game da bidiyon.

“Wanda yayi amfani da AI wajen hada wannan labari ya iya aiki.”  a cewar Philip Brian.

“Gaskiya ta kare mana (Matsaya ta kenan).” Blogger Assanful ya bayyana.

“Mai tsaron gida shine matsalar Man City ,” a cewar Ryan Halbert.

Ganin girman wannan lamari a game da bidiyon da aka sanya a shafin na TikTok DUBAWA ta shiga aikin bincike don tantance wannan da’awa.

Tantancewa

DUBAWA ta sanya wannan bidiyo a manhajar gano asalin bidiyo ta (Google Reverse Image Search,) sai ya kaimu ga shafin sky sports inda suka yi wani rahoton bidiyo, a hoton da ya bayyana a bidiyon iri daya ne da na mai da’awar sai dai sun banbanta ta wajen abin da maganar ke fadi.

Sabanin abin da mai waccan da’awa a shafin na TikTok ke fadi, a rahoton na Sky Sports Haaland ya nuna yana tare da Man City a zarge-zarge 115 na karya dokar da ta shafi wasannin na firemiya. Man City dai na jiran hukuncin kotu (awaits a verdict ) bayan makonni 12 ana sauraren shari’a, wacce za ta nuna ko kulob din na Ingila ya karya ( breached) dokoki da suka shafi kudade a kakar wasannin na shekarun 2009/2010 da 2017/2018, inda ake nemi kulob din ya bayyana cikakken bayani kan yadda yake  

A rahoton kafar yada labaran ta Sky Sports, da aka tambayi Haaland ko yana da fargaba kan makomarsa ganin yadda ake da tarin tuhuma kan kulob din ta fuskar kudade har sau 115, sai ya ce yana da kyakkyawan fata ga kulob din zai iya da batun.

“A’a ni bantaba ma tunanin haka ba, ko wani abu mai kama da haka, ina da kyakkyawan zaton cewa kulob din ya san abin da yake yi. Tabbas a karshe , ba na tunanin ma ya kamata na yi magana mai tsawo anan, ina da kyakkyawan fata a kan wannan kulob,” abin da dan wasan dan asalin kasar Norway ya fada kenan. 

Har ila yau DUBAWA ta lura cewa mai amfani da shafin na TikTok ya wallafa bidiyon ne a ranar Alhamis 23 ga Janairu,2o23, kwana guda bayan Sky Sport ta wallafa tattaunawar  (published) haka suma kafafen yada labaran ONEFOOTBALL da BESOCCER da Mail Online suma sun wallafa labarin irin na Sky News.

Haka zalika babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da rahoto da ya nuna danwasan gaban na Man City na waccen nadama kamar yadda mai da’awar ya nunar.

A Karshe

DUBAWA ta gano cewa zargin da ake na cewa Haaland yayi nadamar tsawaita kwantiraginsa karya ce kawai, bidiyon ne aka yi masa kwaskwarima.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »