African LanguagesHausa

BINCIKE: Duk da cewa an haramta amfani da shi a kasashe da dama ‘maganin nan mai illa’ da ake sha don kara kiba ko teba Apetamin, ana siyar da shi barkatai a Najeriya

Getting your Trinity Audio player ready...

Duk da cewa an haramta amfani da shi a kasashe da dama, maganin nan na (Apetamin syrup) maganin da ke sanya mutum ya rika cin abinci da  ake amfani da shi don kara kiba a wajen wasu- ana nan ana siyar da shi barkatai shagungunan siyar da magunguna a Najeriya ba tare da sanya ka’idoji ba.a rahoton da ELIZABETH OGUNBAMOWO ta hada wa DUBAWA ta binciko irin hadarin da wannan magani ke da shi ga lafiyar dan Adam da ma irin sakacin da hukumomin da ya kamata su sa idanu kan irin wadannan magunguna ke da shi, sun bari ana siyar da shi yadda aka ga dama a wannan kasa da ke da yawan al’umma a nahiyar Afurka. 

Daukar mataki kamar yadda ake fadi ne, na iya samar da nasara ko akasin haka, shekaru da suka gabata, Mis Indijo kamar yadda tafi so a bayyana sunanta ta dauki wani mataki da ya nemi zama sanadin salwantar rayuwarta.

A shekarar 2016 daya daga cikin kawayenta ta fada mata cewa tana iya amfani da maganin kwalbar na Apetamin, domin ta samu damar kara kiba, nan da nan kuwa ta rungumi yin hakan.

“Na gwada amfani da maganin na (Apetamin) domin na samu damar kara kibar jikina , ya dai zama sila ta kara samun damar cin abinci sosai a gare ni, sai dai ya sanya ni yawan kasala ina bacci, yana kuma sa min ciwon ciki.” Abin da ta fada wa DUBAWA kenan.

Wannan kawa ta Indijo da ta ba ta shawarar amfani da maganin ita ba likita ba ce ba kuma jami’ar kula da lafiya ba, ko mai ilimi a wannan fanni ba.

Duk da cewa Mis Indijo ta bayyana cewa maganin yayi aiki a kan kawarta, anata bangaren lamarin ba haka yake ba, domin a 2016 da ta fara amfani da maganin ya fara nuna alamar aiki a jikin nata sai dai daga bisani kibar ta gushe, a 2018 sai ta kara daura aniya ta amfani da maganin da zummar ta samu kiba ko teba ta dindindin.

Ba da dadewa ba ne bayan da ta kudiri aniyar amfani da maganin babu kakkautawa sai ta lura da irin barazana da take samu daga shan maganin.

Sai ta fara ganin fesowar kuraje abin da ya sanya dole ta je ganin likita, bayan an kwantar da ita a asibiti, an mata gwaji sai aka gano tana da wata cutar zubar jini ta Immune thrombocytopenia (ITP), wacce ta samu dalilin amfani da maganin na Apetamin., maganin ya sanya raguwar jini a jikinta.

Mis Indijo ta kara da cewa tana ci gaba da rayuwa da illar wannan cuta tsawonm shekaru shida, sai dai tana fatan za ta warke.

Hadarin amfani da Apetamin

Ita ma Mis Oluwadarasimi, ta bayyana cewa ta yi farinciki da ta zama a raye har take ba da labarin irin illar da maganin na Apetamin yayi mata.

Shekaru masu yawa ta dade tana fatan ta yi kiba don jikinta ya murmure, sai dai bukatar ta bata cika ba, sai dai bata karaya ba domin ta yi niyar sai ta cika burinta.

“ Gaskiya na so na yi kiba sosai, sai na fada wa kawata don na yi iya kokari na ganin na yi kiba duk kuwa da irin abincin da nake ci.” haka ta fadawa DUBAWA.

A shekarar 2023 Mis Oluwadarasimi ta samu shawara daga kawarta ta yi amfani da Apetamin a matsayin maganin da zai sama mata kiba, kamar ita ma kawar Mis Indijo wacce ta bata shawarar ta yi amfani da maganin duk da cewa ita ba masaniya kan harkokin kiwon lafiya ba ce. Kasancewar ta matsu ta ga ta yi kiba ta amince da yin amfani da maganin ba tare da yin wani tunani ba.

Da fari lamarin yayi kama da lokaci ne na kawo sauyi”Maganin na Apetamin ya sanya ina cin abinci sannan ina yin bacci sosai.”a cewar Mis Oluwadarasimi.

Sai dai kwanaki uku kadai bayan fara amfani da maganin sai ta fara lura da illar da maganin ke haifarwa ciki kuwa har da sanya mata ciwon ciki.

Da aka tambaye ta ko ta samu biyan bukata bayan shan maganin sai ta ce “Aa! Na tsayar da amfani da shi bayan kwanaki uku. Na lura da alamun illar da maganin kan haifar kuma suna da hadari, Damuwa ta so ta hana ni da gaske, zuciyata ta rika bugawa da sauri-sauri wanda babban hadari ne.” 

Hadarinsa ya fi amfaninsa

Ga Olorunfemi Raymond, kuwa yadda yayi amfani da Apetamin abu ne da ba zai manta da shi ba nan kusa. Dankasuwar mazaunin Legas ya fadawa DUBAWA cewa ya taba amfani da maganin na Apetamin don neman kara kiba.

Yace wani mai aiki a wajen siyar da magani ne a yankin da yake ya ba shi shawarar amfani da wannan magani don ya ba shi damar kara yawan cin abinci ta yadda zai kara kiba.

Kwanaki kadan daga bisani Mista Raymond yayi da na sanin bai yi amfani da shawarar da aka bashi ba daga wannan wajen siyar da magani kasancewar, dankasuwar mai hada-hadar kamfani ya rika jin ciwon ciki babu kakkautawa bayan shan maganin. 

Mista Raymond da fari yayi watsi da jin ciwon inda yayi tunanin dama ana iya jin hakan bayan shan maganin sai dai abin mamaki a gare shi ciwon cikin ya ci gaba da yin muni.

“Wannan ciwon ciki shi ya sanya na dena amfani da wannan magani ba da bata lokaci ba, kuma ban sake amfani da shi.’’ a cewarsa.

Dan shekaru 36 ya bayyana cewa yana cin abinci “fiye da lokutan baya kuma ina bacci sosai” a lokacin da yake shan maganin “hadarin maganin yafi alfanunsa”, wannan hali da na tsinci kaina ya sanya na dena amfani da wannan magani.

Wane magani ne  Apetamin?

Apetamin maganin ne da zai sa mutum ya rika cin abinci , sannan ya kan sa mutum ya kara kiba, kamfanin TIL Healthcare Pvt Ltd, shi ke yin maganin, wani kamfanin magani a kasar Indiya, sannan ana kasuwancinsa da rarraba shi a  Najeriya a kamfanin Grace Drugs & Healthcare Ltd wanda ke a 1A, Ogunlana Drive, Surulere, Lagos 

Da jaridar DUBAWA ta nazarci abubuwan da maganin ya kunsa ta gano ya kunshi sinadaran cyproheptadine hydrochloride (anhydrous), L-lysine hydrochloride, thiamine hydrochloride, hydrochloride, nicotinamide da dexpanthenol. 

Babban sinadari a cikin Apetamin shine cyproheptadine, sinadaran kwantar da cuta wanda ke bukatar ba da shawarar likita kafin amfani da shi kamar yadda hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka ta nunar (according to the US Food and Drug Administration (FDA).) Wani nazari da aka yi a 2020 ya gano cewa (established that the medicine ) wannan magani na kunshe da sinadarin cyproheptadine, (wanda ke da illa ko ke lalata hanta).

Tun asali an samar da maganin na  Apetamin ne don magani ga mutanen da suka rame lokacin da suke fama da wata rashin lafiya (treat weight loss symptoms associated with an illness) ko idan mutum na fuskantar rashin jin dadi da jikinsu ba dadi ba wai an tanadi mutane wadanda suke cikin koshin lafiya ba ne.

A shekarun baya-bayan nan mutane da dama a Najeriya sun rungumi amfani da maganin don samun kiba cikin sauri da ma fitar da wasu surori na jikin dan Adam. Amfani da Apetamin don neman kiba an kalubalance shi sosai ta hanyar bincike daban-daban, da ma aikin wasu cibiyoyi na gwamnati a fadin duniya saboda hadarin da wannan magani ke da shi, dama yadda wasu ke ba da bayanai a kan maganin bayan sun sha ko sun yi amfani da shi. A shekarar 2020 wani bincike da aka yi (study published) a rahoton mujallar ACG Case Reports Journal, masu aikin bincike sun gano wata mata ‘yar shekaru 40 da a baya ta kasance mai koshin lafiya sai dai daga bisani ta samu wata cuta da ta shafi hanta bayan da ta dauki mako shida tana shan maganin na Apetamin a kowace rana.

A binciken da suka yi sun bayyana cewa matar ta rika jin gajiya ko kasala da jin ciwo a barin cikinta da ciwon idanu makonni da ta fara amfani da maganin da ta ji labarin amfaninsa a “shafukan intanet kan yadda mace za ta gyara jikin ta ta zama mai sura.”

Saboda hadarin da wannan magani ke iya haifarwa, Apetamin an haramta amfani da shi a kasashe da dama da suka hadar da Faransa da Birtaniya da Amurka. A cewar US FDA “an gano irin illar da take biyo bayan amfani da wannan magani na Apetamin wanda aka bayyana da cewa an haramta amfani da shi don karin kiba da gyara surar jiki”.  

FDA ta nunar da cewa mutane da dama basu da masaniya kan irin illar da ke tattare da maganin na Apetamin da suka hadar da jin lalaci da gani garara-garara da samun saukar jini, Idan mutum ya zake kuma sai ya samu wata illar babba kamar shiga rudani da farfadiya har ma a iya rasa rai, musamman idan mutum na shan barasa ko wani abu da ke sa maye.

A kasar Canada,ana amfani da magungunan don neman karin kiba sai dai ana amfani da maganin ne bisa sharuda da likita ya gindaya (advice of a medical expert) don gudun wuce gona da iri.

An haramta kuma ana sa ido a wasu kasashe ban da Najeriya

A Najeriya Apetamin magani ne da kawai idan mutane suna son kara cin abinci ko suna son kara kiba sai su rika sha.Duk da cewa kasashen duniya na daukar matakai kan maganin na Apetamin ana siyar da shi a kasar barkatai.

Karkashin doka hukumar lura da abinci da magunguna ta kasa a Najeriya NAFDAC ita ce ke da alhaki (authorised to regulate) na sa ido da bibiya kan yadda za a yi magungunan da yadda za a shigo da su kasar ko ma a fitar da su, ko rarraba su ko tallansa ko siyarwa da amfani da abinci da magunguna da mayukan shafawa da wasu kayayyaki na magani da ruwa da ake yi na sha da sinadarai da sabulun wanki.  

An samar da wannan hukuma don kare lafiyar al’umma ta hanyar kula da magunguna da abincin da suke amfani da su, amma hukumar ta gaza wajen ba da kariya wajen siyar da maganin na Apetamin wanda ake siyar da shi a bayyane a kasuwanni da shagungunan siyar da magani a Najeriya.

Apetamin na nan a ko’ina

Domin gano yadda wannan magani ya bazu da ma yadda al’umma ke samunsa da ma  dubawa ko mahukunta na sa’ido akansa ko yadda ake siyar da shi a kasar. Mai daukowa DUBAWA rahoto ta ziyarci shagungunan siyar da magunguna guda takwas a jihar Legas, kuma abin da ta gano shine bawahala ake samun maganin kuma ba sa idanu akansa, daga cikin shagungunan maganin takwas, hudu suna da shi yayin da sauran hudun kuma suka ce da mai dauko rahoton ta DUBAWA taje ta dawo za a sama mata.

A wurin siyar da maganin Justrite Pharmacy da ke a Abule Egba, karamar hukumar Alimosho a jihar, mai daukowa DUBAWA rahoto ta bayyana cewa ta sayi maganin kan kudi  N6,000 zaa baka ba tare da neman wata takarda daga jami’in lafiya ba. 

 Haka lamarin yake a sauran shagungunan siyar da maganin. A shagon siyar da magani na Bydow Pharmacy, wanda ke kan hanyar Abeokuta, da zarar an sha U-turn a Abule Egba ana siyar da maganin a kan  N7,350. 

Lokacin da DUBAWA ta ziyarci shagon magunguna na Josfekmart Pharmacy Limited da ke kan hanyar Ekoro Road a Lagos, mai kula da ba da magungunan ya bayyana cewa ana siyar da maganin kan kudi  N6,500.

Yana da hadari shan maganin ba tare da umarnin likita ba

 Idan aka kalli takardar da ke like a jikin maganin na Apetamin mai nauyin 200 ml da aka siyo akwai gargadi da aka rubuta a jikinsa: “Yana da hadari yin amfani da wannan maganin har sai idan akwai kulawa ta likta.”

A dai jikin takardar gargadin an rubuta cewa wasu mutanen idan suka sha wannan magani za su iya samun kansu a yanayi na gani garara-garara ko jin hajijiya a lokacin da suka fara sha,  da zarar hakan ta faru mutum kada ya tuka mota ko amfani da wani mashin da ke zama mai hadari.”

Gargadin da ke jikin wannan magani ya nuna karara irin hadari da ke tattare da maganin muddin aka yi amfani da shi ba tare da umarnin likita ba. Wannan ya kamata a rubuta cewa bai kamata a yi amfani da shi ba tare da umarnin likita ba.

Sai dai duk da haka a Najeriya ana siyar da shi ga kowa ba tare da takardar likita ba, wannan kuwa na faruwa saboda rashin kulawa ta jami’an da suka kamata, hakan ke sanya rayuwar ‘yan Najeriya da dama cikin hadari kamar Mis Oluwadarasimi, wacce ke kallon maganin a matsayin mafita a gare ta ta samun kiba ko teba, duk da hadarin da ke tattare da maganin.

  “Ina samunsa a shagungunan siyar da magani ba tare da wata takarda ta likita ba a Najeriya.” kamar yadda Mis Oluwadarasimi ta bayyana abin da ke tabbatar da binciken DUBAWA, Sai dai ba ta bayyana sunan shagon maganin ba saboda tsaro.

INVESTIGATION: Despite ban in several countries, ‘harmful’ weight gain product, Apetamin, sold indiscriminately in NigeriaDaya daga cikin shagunan siyar da magunguna da mai daukowa DUBAWA’ rahoto ta ziyarta

Da aka sake zurfafa bincike ya nunar da cewa wannan magani ya samu amincewa ta hukumar da ke kula da abinci da magunguna NAFDAC har ma yana da lambar da aka yi masa rijista kamar haka A7-4783. 

Domin tabbatar da ganin cewa maganin mai kyaune ko mara kyau, DUBAWA ta yi amfani da hanyar gano gaskiyar magani mai kyau ne ko mara kyau (Authentication Service (MAS) scheme,) wanda ke zama, hanyar da hukumar ta NAFDAC ta samar don tantance inganci na magunguna.

Tsarin ana kankare kati a dauki wasu lambobi da ake tura gajeran sako (SMS) don tantance ingancin maganin a lokacin da aka je siya. Ta hanyar amfani da wannan hanya DUBAWA ta duba wadannan lambobi wadanda ta tura wato 3045305053247 zuwa ga 38353 a ranar 20 ga watan Agusta, 2024.

Jim kadan bayan tura sakon an dawo da sakon ba da tabbaci na cewa maganin mai kyau ne, “Ok. Genuine Apetamin,” a sakon na hade da lambar rijistar NAFDAC ta maganin.

INVESTIGATION: Despite ban in several countries, ‘harmful’ weight gain product, Apetamin, sold indiscriminately in Nigeria

Hoto na irin sakon MAS 

Apetamin ba tare da lambar NAFDAC ba

Baya ga siyar da maganin ba tare da takardar likita ba, wani abu da ke nuna kasawar hukumar da za ta sa idanu shine DUBAWA ta lura cewa akwai irin wannan magani ana siyar da shi a kasuwa ga al’umma ba tare da lambar NAFDAC ba. 

Mai dauko wa DUBAWA rahoto ta lura da hakan a lokacin da ta ziyarci shagon siyar da magani na MAMS Pharmacy da ke a Agbelekale a karamar hukumar Alimosho, jihar Legas. Lokacin da mai dauko rahoto ta tambaya ko za ta iya siyan wannan magani, mai kula da shagon ya tabbatar da cewa akwai maganin sai dai akwai alamu na dari-dari a fuskarsa.

“E, muna da shi sai dai wannan bashi da lambar NAFDAC amma duk abu guda ne muna siyar da shi a kan naira  N6,000,” a cewarsa.

Ganin martanin mai dauko rahoton kan cewa don me ake siyar da magani babu lambar NAFDAC sai da wani jami’i da ke zama shugaba a wajen ya shiga tsakani don daidaita lamura.

“ A kwai irin wannan magani  (Apetamin) guda biyu ne, daya shigo da shi ake yi daga kasar waje, daya kuma a nan gida Najeriya ake yinsa. Wanda aka yi a Najeriya shine ke da lambar NAFDAC wanda kuwa aka shigo da shi ba a yi masu rijistar NAFDAC, “ a cewarsa.

“Wanda aka shigo da shi daga ketare yana da kalar lemo ko jawa mai duhu, yayin da wanda aka yi a cikin gida ke zama kalar ta jawa mai haske idan ka kalli kwalinsa.”

Don kawai ita mai dauko rahoton ta nuna cewa ta gamsu da bayanansa, ta sayi guda daya akan farashi Naira 5500, bayan daukar lokaci ana ta ciniki kan farashin. INVESTIGATION: Despite ban in several countries, ‘harmful’ weight gain product, Apetamin, sold indiscriminately in Nigeria

Siyar da magani wanda bashi da lambar NAFDAC haramun (illegal) ne a Najeriya, kuma idan ma ka duba kwalin babu lambar nan da ake kankarewa don tabbatar da ingancin magani wannan babbar barazana ce ga al’umma.

Peter Akhidenor, wani ma’aikaci a fannin hada magunguna yayi gargadin cewa cyproheptadine wanda ke zama babban sinadari a cikin maganin na Apetamin na iya jawo babbar illa ta bugun zuciya ba kakkautawa ko zuciyar ma ta buga, ko ta rika daukar lokaci tsakanin bugun zuciya daya zuwa wani, musamman idan aka hada maganin da wasu magunguna.

Ya fada wa DUBAWA cewa wannan magani ana amfani da shi ba tare da ka’ida ba don neman kara kiba, ya kamata a ce likita ne kawai zai iya ba da umarni a yi amfani da maganin.

“ Wannan maganin (Apetamin) ya kamata a sha shi ne kawai bayan umarnin likita, amma ba shi kadai ba ne za ka ga wasu kamar Tramadol, mutane na amfani da shi ko’ina.”

Francis Agbaraolorunpo, kwararren masanin kimiyar halittar dan Adam a jami’ar jihar Legas ya fadawa DUBAWA magungunan da ake sha don kawar da wasu abubuwa kamar atishawa da kaikayin jiki irinsu Apetamin  suna da irin illa da suke haifarwa a jikin mutum. Sai ya shawarci mutane da su rika zuwa ganin likita maimakon yin amfani da magani da ka, kasashen yamma na matukar kula da batun umarnin likita kafin amfani da magani, sabanin a nan Najeriya. Mista Agbaraolorunpo ya bayyana cewa ita fa kiba sau tari gado ce, ya kuma ba da shawarar koma kibar ake son yi abi hanyar cin abinci mai gina jiki da samun isasshen hutu na yin bacci.

Sharhi kan yadda ake tallan Apetamin a kafafen sadarwar zamani

Bincike ya nuna cewa akwai ka’ida kan siyarwa da tallan maganin na Apetamin a shafin TikTok, an sa Apetamine cikin abubuwan da suka saba “halayya ko abubuwan da ake tsammani a sharuda”na shafin, sai dai wadanda ke amfani da shafin ko masu siyar da kayayyaki a shafin sun shigo da wata hanyar ha’inci ta yadda suke sauya sunan ga misali  “apetami” da “apetaminsirop” don kawar da hankali yadda shafin zai gano.

Karin wasu kalmomin sun hadar da #apetaminplug, #apetaminsyrup #thicksyurp #skinnygirlproblems #gainweight #healthtips.

DUBAWA  ta gano wasu shafuka da ke bawa mutane shawarar amfani da Apetamine don samun kiba kamar haka; It Girl Dime, Monae Herron, the real bubbles, Miss Wisdom, Anikemi da Dom Weight gains.

INVESTIGATION: Despite ban in several countries, ‘harmful’ weight gain product, Apetamin, sold indiscriminately in Nigeria

Hoto na dilar maganin a TikTok tana amfani da sunayensa kala-kala 

Idan ka duba a shafin na TikTok akwai daruruwan shafuka da ke nuna mabanbantan magungunan na sha da na kwaya da wadanda aka yi a kamfani da wadanda aka yi a gida.

A shawarar da Instagram kan bayar a game da siyarwa da amfani da magunguna yana ba da shawarar masu amfani na iya neman taimakon masana idan suka ji cewa sun kamu da son sha , sannan ya ba da shawarar a nemi karin haske, wanda babu wannan a TikTok.

INVESTIGATION: Despite ban in several countries, ‘harmful’ weight gain product, Apetamin, sold indiscriminately in NigeriaHoton irin shawara ko jan hankalin Instagram.

A shafin Facebook, talla a kan maganin na Apetamin abu ne da ba zaka taba rasa gani ba, da zarar ka nema za ka ga an yi wallafa da dama a shafuka da ma rukuni ko guruf na shafi wadanda a bayyane suke tallata wannan magani tare da hadawa da hotuna da yadda za a iya tuntubar masu siyarwa.

Rashin sanya ka’ida kan wannan ya sanya masu tallata maganin suke baje hajarsu ta Apetamin a shafin na Facebook inda ake hada masu siya da siyarwa da ma irin martani da mutane ke yi. Yawan wannan tallata maganin ya nunar da yadda ake wannan hada-hada ba tare da taka birki ba ga wannan magani da ake ta cece-ku-ce a kansa.

Sharhi da aka yi kan shafin X ya nunar da cewa masu amfani da shafin basa siya ko siyar da maganin a kan manhajar, sai dai ana tattauna irinm illar da ke tattare da maganin ko kuma a bawa wasu shawarar amfani da maganin. Shima a wannan shafi bamu ga wani sharadi na taka birki ba kan amfani da maganin.

Masu amfani da maganin na Apetamin na nuna hotuna (representation) kala biyu na farko hotonsu kafin su fara amfani da maganin da hotunsu bayan sun fara amfani da maganin da yadda suka kara kiba, “a lokacin da ya dace”  dama yadda ake amfani da maganin da tallansa.

Duba da yadda wadannan shafukan sada zumunta suke a duniya, abune mai sauki a hadu da masu siya a hada yadda za a kai kayan duk inda suke bukata.

Sai dai a hannu guda a dokance karkashin hukumar ta (NAFDAC) duk wasu kaya ko abinci ko kayan kwalliya da magunguna da sauransu muddin ana so a siyar da su a Najeriya sai an yi rijista da hukumar kafin a siyarwa ko a rarraba su.

Dokar kula da abinci da magunguna da dangoginsa (Act Cap F.33) ta haramta “hada kayayyakin ko siyarwa ko rarrabawa da tallatawa  na duk wasu nau’ikan abinci da magunguna da kayan kwalliya da kayan da ake amfani da su a harkokin kula da lafiya ko ruwansha”

NAFDAC ta ba da amsar tambayar DUBAWA kan batun maganin na Apetamin

A ranar 11 ga watan Satumba,2024, DUBAWA ta tura tambaya karkashin dokar fadin albarkacin baki (FOI) kan batun na maganin na Apetamin, cikin abubuwan da aka tambaya sun hadar da neman karin haske ko NAFDAC ta yi rijista ta maganin don amfanin al’ummar Najeriya kasancewar baya cikin jerin magunguna da hukumar ta yi wa rijista a littafinta na Greenbook. 

Ana so kuma a sani ko hukumar ta sanya maganin cikin wadanda ta bayyana da cewa sai da umarnin likita za a iya amfani da su (POM) ko kuwa magani ne da kawai za a iya zuwa shagon siyar da magunguna a siya (OTC) ganin cewa maganin na kunshe da sinadarin cyproheptadine.

Kuma duba da bukatar ta fadin albarkacin baki za a so sanin wane dalili ya sanya maganin baya cikin jerin magunguna na Greenbook da hukumar ta NAFDAC ke da shi. Dama jin matakan da hukumar ke dauka don gudun kada ‘yan Najeriya su rika amfani da maganin barkatai.

”Ya  zuwa ranar 19 ga watan Satumba hukumar ta mayar da amsa ta hanyar ofishi mai kula da harkokin fadin albarkacin baki na FOI inda takardar dauke da sa hannun jami’ar ofishin Offiah Nneka, a madadin babbar daraktar hukumar Moji Adeyeye, tace ta ga sakon na DUBAWA amma “ina bukatar a bada lokaci kafin ba da amsa.”

A sakon ta na tabbatarwa da ya zo a watan Oktoba, NAFDAC ta tabbatar da cewa maganin an yi masa rijista, tana kuma hada kai da sauran masu ruwa da tsaki ta yadda za a kaucewa amfani da magunguna barkatai ciki kuwa har da Apetamin.

NAFDAC, bata ce komai ba game da ko shi maganin an tsara shi cikin wadanda ba a iya amfani da su sai da umarnin likita (POM) ko wanda kawai za a iya shiga shagon siyar da magunguna a siya a tafi. 

“Maganin na Apetamin Cyproheptadine Lysine da Vitamins Syrup an yi masu rijista da lamba A7-4783. Ba a sanya wannan magani cikin littafin na Greenbook ba saboda hukumar na aikin gyara shafinta don shigar da duk magunguna da ya wajaba sai da umarnin likita za a yi amfani da su (POM), da maganin da za a iya siya a shagon magani (OTC) da abinci da ke zama magani. NAFDAC na gudanar da aikinta na ba da kariya ga lafiyar ‘yan Najeriya, tana hada kai da sauran masu ruwa da tsaki don yakar shan magunguna barkatai a Najeriya. NAFDAC ta dakatar yin rijista ko sabuntawa na irin wanna gambiza,” wannan wani bangare kenan na martanin hukumar ta NAFDAC. 

Ko da yake NAFDAC ta bayyana cewa “ta dakatar da yin rijista ko sabuntawa ta irin wannan gambiza tana nufin wato sinadaran da ke cikin Apetamin”, bata kara ba da bayani ba kan wannan.  

NAFDAC ba za ta karbi wani sabon neman rijista ba na maganin da ake shigo da shi kamar yadda yake a jerin abubuwan da gwamnatin tarayya ta haramta shigo da shi (NAFDAC Ceiling List and Banned formulations),”  abin da hukumar ta bayyana a jawabin da ta fitar (its 2023 statement).

Har yanzu ba a kai ga tantancewa ba ko Apetamin na cikin abubuwan da gwamnatin tarayya ta haramta a shigo da su ko cikin wadanda hukumar ta NAFDAC ta jera wadanda ba ta aminta da abubuwan da ke cikinsu ba. 

A ranar 7 ga watan Oktoba, 2024, DUBAWA ta tura sako zuwa ga kamfanin TIL Healthcare wadanda ke hada wannan magani, don su mayar da martani kan abubuwan da wannan bincike ya gano, har zuwa lokacin hada wannan rahoto kamfanin da ke da cibiya a kasar Indiya bai ce komai ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »