African LanguagesHausa

Binciken gaskiyar mahimman batutuwan da ke kunshe cikin jawabin shugaba Tinubu na Ranar Bukin Samun ‘Yanci kai

Getting your Trinity Audio player ready...

Cikakken Sako

A ranar Talata daya ga watan Oktoba, 2024 Najeriya ta gudanar da bikin tuni da ranar da ta samu “yancin kanta, a wannan rana ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu a jawabinsa da ke zama na biyu ga ‘yankasa irin wannan (Independence Day speech) ya amince cewa ‘yan Najeriya na shan fama da tarin matsaloli inda yace ya dukufa wajen nema wa al’ummar kasar mafita mai dorewa.

 A cikin jawabinsa yayi tarin wasu da’awa kan irin nasarori da ya cimma a tsawon mulkin gwamnatinsa na watanni 16. DUBAWA ta gudanar da bincike kan wasu daga cikin da’awar shugaban daban-daban.

Da’awa ta  1: Gwamnatin Shugaba Tinubu ta gaji Dala miliyan dubu 33 da aka killace sannan ta yi nasarar kara wannan kudade inda suka kai Dala miliyan dubu 37.

“Mun gaji kudaden ajiya sama da dala miliyan dubu 33 watanni 16 da suka gabata….. Duk da wadannan kalubale mun daga kudaden da ke zama na ajiyarmu a kasashen ketare inda suka koma dala miliyan dubu 37.”

Kudin ajiya a cewar Babban Bankin kasa Central Bank of Nigeria (CBN) kudade ne da ake ajiyewa a asusun ketare wadanda ake iya amfani da su a lokaci da aka samu kai a yanayi na takura ko tangal-tangal.

 A Najeriya abubuwan da ake kira na ajiya sun hadar da zinare da kudade da Asusun ba da Lamuni IMF ke da ta cewa inda kasashe ke ajiyewa (Special Drawing Rights (SDRS) da kudade da ake iya sauya su. Manyan hanyoyi da ke zama sila ta samo irin wadannan kudade sun hadar da hanyoyin musayar kudade da suka hadar da na dangogin harkar manfetir, da kudaden da ke zuwa daga ayyuka da wasu abubuwan da ma ba a bayyana ba, da biyan kudaden haraji da kudaden haraji na harkokin tsaron ketare da kudaden da ake karba bashi da tallafi na kasashen waje da kudaden tallafi da kayayyaki da ake fitar da su kasashen waje wadanda ba su shafi manfetir ba, da kudaden da wadanda ke zaune a kasashen waje ke aikowa gida daga kasashen na ketare, baya ga saura.

Bayanai da aka tattara daga babban bankin kasa (data from CBN) ya nunar da cewa ya zuwa ranar 26 ga watan Mayu, 2023 kafin shugaban Najeriya ya hau karagar mulkin Najeriya abin da kasar ke da shi a asusunta na kasashen waje ya kai  $35,147,391,757 wato idan aka kididdige kusan miliyan dubu $35.15 na dalar Amurka.

Ya zuwa ranar 27 ga watan na Satumba, 2024  kudin ajiyar ya kai miliyan dubu 38.

Binciken gaskiyar mahimman batutuwan da ke kunshe cikin jawabin shugaba Tinubu na Ranar Bukin Samun ‘Yanci kai

Hukunci: GASKIYA CE

Bayanan da Babban Bankin Najeriya CBN ya tattara, sun nunar da cewa abin da kasar ke da shi na ajiya dala miliyan dubu $35.15 kafin Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki, ya zuwa 27 ga watan Satumba kasar ke da adadin da ya kai dala miliyan dubu $38.

Da’awa ta biyu 2: Gwamnatinsa ta biya kudaden kwantan bashin harajin ketare da ta gada wato kudade da aka biyo bashi dala miliyan dubu $7.

“Mun biya kudaden bashin kudaden da ke zama kwantan bashinketare da muka gada dala miliyan dubu  $7.” wani bangaren a jawabin shugaban .

Foreign exchange (FX) na nufin kudaden da ya kamata a biya wato kwantan bashi daga wasu huldodi da aka yi tsakanin kasa da kasa.

Idan za a iya tunawa a watan Fabrairu 2024 bankin na CBN ya bayyana (revealed) cewa ya gaji kudaden bashi na huldar ketare dala miliyan dubu $7, kuma daga cikin wannan adadi akwai kudaden da ake da alamar tambaya kansu ($2.4 billion had issues) wanda hakan ke nufin ba fahimta cikakkiya a kansu.

Daga bisani a watan Maris, 2024 an samu rahotanni da kafofin yada labaran Premium Times, Bloomberg, Channels Television da Reuters, suka wallafa wadanda suka nunar da cewa an warware takaddamar kudaden ketaren da suka makale. A cewar wadannan rahotanni Babban Bankin Najeriya CBN ya kammala biyan kudade dala miliyan dubu da rabi $1.5, matakin da ya sanya ya warware kudaden harajin ketare da suka makale ko bashi na masu ajiya.

Binciken gaskiyar mahimman batutuwan da ke kunshe cikin jawabin shugaba Tinubu na Ranar Bukin Samun ‘Yanci kai

Hukunci: GASKIYA CE

Kafofin yada labarai da dama na cikin gida da wajen kasa sun ba da rahoto cewa duk kwantan bashi na harajin ketare Babban Bankin Najeriya CBN ya kammala biyansu ya zuwa watan Maris,2024….

Da’awa ta 3: Mun warware basuka “Ways and means” na sama da naira tiriliyan 30

Dataphyte ta bayyana “Ways and means” a fahimtar Najeriya da kudaden da Gwamnatin Tarayya ke karba bashi don warware wasu matsaloli na gajeran wa’adi ko gaggawa, wato kudade da take karba daga Babban Bankin Najeriya.

 A watan Mayu 2024 Ofishin da ke lura da harkokin  bashi (DMO) ya duba batun sake fasaltawa ko sake masu makoma (securitised) na kudade naira tiriliyan 22.7 da gwamnatin ta karba bashi karkashin tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya zuwa ranar 28 ga watan Disamba,2022 inda aka bukaci (requested)  a mayar da kudaden zuwa takardun lamunin gwamnati.  

Tsarin sake fasaltawar na (Securitisation) na nufi tattara kalolin basuka a siyar da su a matsayin lamuni ga masu zuba hannun jari.

Wannan na nufin bashin za a sake masa fasali a karkasa tsawon sama da shekaru 40. A shekaru uku na farko na sake biyan bashin, gwamnatin tarayya na da damar ta biya CBN amma ba gundarin bashin da ta karba ba.

Gwamnatin Tarayya za ta biya kudin ruwa ne a tsawon shekaru ukun, inda za ta rika biyan kaso 9 cikin dari a duk shekara, kasa da kaso 21 cikin dari da yake tun farkon ba da bashin. Bayan shekaru uku sannu a hankali kuma za ta biya bashin a tsawon shekaru 37.

Karkashin gwamnatin Mista Buhari kudin da ake karba bashin (Ways and Means) sun girmama daga naira miliyan dubu N656 zuwa naira tiriliyan N23.7.

Binciken gaskiyar mahimman batutuwan da ke kunshe cikin jawabin shugaba Tinubu na Ranar Bukin Samun ‘Yanci kai

Hukunci: KARYA CE

Bayanan ofishin da ke lura da harkokin bashi na DMO sun nunar da cewa bashin an sake fasalta shi don biya a sama da shekaru 40, sabanin abin da Shugaba Tinubu ke fadi cewa an biya kudaden bashin baki daya babu su.

Da’awa ta 4: “Mun rage kudaden da muke biya na bashi daga kaso 97 cikin dari zuwa kaso 68 cikin dari.”

A cewar jaridar BusinessDay, kiyasin kudin bashi da abin da ke zama kudin shiga ya ragu da kaso 74 cikin dari a watanni ukun farko na 2024, adadin da ke zama mafi kankanta a tsawon shekaru biyar. Kafar yada labaran ta rawaito Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar da bayanai cewa kiyasin bashi da abin da ke shigarwa kasa ya zama kaso 74.3 cikin dari (N1.31 tiriliyan) yayin da abin da ya shigarwa kasar ke zama N1.76 tiriliyan a watanni ukun farko na 2024. Wannan adadi yayi kasa da kaso 149.5 cikin dari (1.97 tiriliyan) a irin wannan lokaci a 2023. 

Ita ma jaridar Punch ta wallafa nata rahoton tsakanin Janairu zuwa Mayu 2024 inda tace Najeriya ta biya dala miliyan dubu $2.18 wanda ke zama kusan N3.4 tiriliyan a matsayin biyan bashi.

Har ila yau BusinessDay ta ba da rahoton cewa an yi hasashen samun kaso 110.4 cikin dari a 2024 duba da kalubale na iya biyan bashin da ya zama wajibi idan aka kwatanta da abin da ke shigowa.

Binciken gaskiyar mahimman batutuwan da ke kunshe cikin jawabin shugaba Tinubu na Ranar Bukin Samun ‘Yanci kai

Hukunci: KARYA CE

A cewar BusinessDay, gwamnatin tarayya ta biya kaso 74.3 cikin dari (N1.31 tiriliyan) daga N1.76 triliyan na abin da ke hannunta na kudin shiga a watanni ukun farkon 2024. Jaridar Punch ta ba da rahotanni cewa gwamnatin tarayya ta biyan ninki na wannan adadi tsakanin watan Janairu da Mayu, hakazalika jaridar ta BusinessDay ta ba da rahoton hasashen samun kari na 110.4 cikin dari a 2024 saboda kalubale wajen biyan bashin idan aka kwatanta da abin da ke shigowa. 

Da’awa ta 5: Najeriya ta jawo masu zuba jari da kudinsu ya haure dala miliyan dubu $30 a shekarar bara

Masu zuba jari daga ketare Foreign Direct Investment (FDI) shine yadda mai zuba jari zai taso daga wata kasa ya zama shike da iko da wani nau’in kasuwanci a wata kasa.

DUBAWA ta nazarci kudaden da aka shigo da su daga Reports na hukumar kididdiga ta kasa (NBS). Wadannan rahotanni na ba da bayanai kan yadda masu zuba jari na ketare ke zuba jari kai tsaye, ko zuba jari na daidaiku ko wasu kungiyoyi daga ketare da sauran nau’ikan zuba jari a Najeriya duk bayan watanni uku.

A cewar bayanan na NBS data, a watanni uku na biyu a 2023 biyo bayan fara gwamnatin Shugaba Tinubu Najeriya ta samu masu zuba jari daga ketare kai tsaye FDI da kudi dala miliyan $86.03. A watanni uku na uku (wato bayan watanni tara) kuma a shekarar Najeriya ta samu $59.77 daga masu zuba jarin na FDI. A watanni uku kuma na karshe ta samu dala miliyan $183.97. A watanni uku na farkon 2024 Najeriya ta samu masu zuba jarin na FDI $119.18. Baki daya Najeriya ta samu dala miliyan $448.95 daga watanni uku na biyu a 2023 zuwa watanni ukun farko a 2024, adadin da ke zama nesa ko ke da tazara kasa da abin da Shugaba Tinubu ke ikirari na cewa kasar ta samu masu zuba jari daga ketare da yawan kudinsu ya kai dala miliyan dubu $30.

DUBAWA ta kuma gudanar da bincike inda ta yi amfani da wasu muhimman kalmomi; kudaden zuba jari na ketare a Najeriya a 2024 “Foreign direct investment in Nigeria 2024” nan sai ta ga ministar harkokin masana’antu da kasuwanci da zuba jari Doris Uzoka-Anite, na cewa (stated) Najeriya ta yi nasarar samun masu zuba jari da suka zuba kudin da ya haure dala miliyan dubu $30 a shekarar da ta gabata.

Ministar ta yi karin haske da cewa wannan hulda ana sa rai za ta tabbata a shekaru da ke tafe ganin yadda aka fara ayyukan da cimma yarjeniyoyi na karshe.

Binciken gaskiyar mahimman batutuwan da ke kunshe cikin jawabin shugaba Tinubu na Ranar Bukin Samun ‘Yanci kai

Hukunci: YAUDARA CE 

Sabanin da’awar shugaban, bayanai da hukumar kiddidiga ta kasa NBS ta tattara a watanni uku na biyu a 2023 zuwa watanni uku na farkon 2024 kan kudaden zuba jarin daga ketare FDI, abin da ya shigarwa kasar shine  dala miliyan $448.95. Ko da dai ministar masana’antu da kasuwanci da zuba jari tace Najeriya ta jawo masu zuba jari da kudinsu ya haure dala miliyan dubu $30,  wannan na nufin kulla aniya wanda bai tabbata ba daga masu zuba jarin.

Da’awa ta 6: Majalisar Zartarwa FEC ta amince (approved) a samar da taraktoci 2000 samfurin John Deere tractors, da tarakta komai da ruwanka da na’urar yin kunya-kunya a gona da sauran nau’ikan na’urori da ake amfani da su a gona. 

Najeriya na fuskantar kalubale na wadatar abinci, abubuwan da ke da nasaba da rikici a wasu bangarori na kasar da matsalar tattalin arziki da hauhawar farashi na kayan abinci. Relief Web ya bayyana cewa wannan yanayi na iya ci gaba har zuwa farkon shekarar 2025, musamman a yankin arewacin kasar.

 A cewar shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya United Nations akwai kimanin mutane miliyan 4.4 wadanda ke fama da matsalar abinci a jihohi uku na arewacin kasar akasari a jihar Borno, a fadin kasar kuma kimanin mutane miliyan 100 na fama da matsala ta karancin abinci ya zuwa watanni uku na farkon 2024.

Ya zuwa watan Agusta 2024, hauhawar farashin kayan abinci (food inflation rate) ya kai kaso 37.52%  a shekarar, kaso 8.18% kari idan aka kwatanta da 29.34% a watan Agusta 2023.

A farkon shekarar 2024, wani rahoto (report) da cibiyar kirkira da ci gaba a aikin jarida  wato Center for Journalism Innovation and Development (CJID) ta fitar ya nunar da cewa ana samun hauhawar farashin kayan abinci babu kakkautawa, inda ta danganta matsalar yadda ake yin ayyukan gona a matsayin abin da ya jawo hakan saboda matsalar tsaro inda ta bukaci a zuba hannun jari a fannin.

A cewar wasu rahotanni na kafafan yada labarai news reports, a kokarinta na ganin an shawo kan matsalar rashin wadatar abinci Majalisar Zartarwar Tarayya (FEC)  ta amince a siyo taraktar noma 2000 , da na’urar yin kunya-kunya a gona 4000 da babbar motar tirela 1.200 da sauran wasu kayayyaki karkashin shirin ayyukan gona na zamani.

Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa ya yi karin jawabi cewa  Astride DMCC  za su samar da dukkanin kayayyakin sannan za su samar da kamfani da za a rika harhada manyan motocin, a mataki na biyu na kwantiragin, duk da haka bai yi karin haske ba yaushe ne aikin zai kammala.

A wani labarin kuma, ministan ayyukan gona da wadata kasa da abinci , Abubakar Kyari tun da fari (earlier) yayi jawabi cewa Gwamnatin Tarayya ta cimma yarjejeniyar fahimta da kamfanin da ke samar da motocin na tarakta John Deere inda kamfanin zai samar wa Najeriya taraktoci 2,000 a duk shekara tsawon shekaru biyar.

Wannan mataki nazama na abin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce ya cimma a tattaunawa (meeting) da manyan jami’an kamfanin na John Deere inda suka tsara za a samar da kamfani da zai rika samar da tarakta a Najeriya don bunkasa ayyukan gona na zamani.

Binciken gaskiyar mahimman batutuwan da ke kunshe cikin jawabin shugaba Tinubu na Ranar Bukin Samun ‘Yanci kai

Hukunci: GASKIYA CE

Rahotanni da ke a kasa sun nunar da cewa kalaman na shugaban kasa cewa majalisar zartarwa ta amince za a samar da kamfani a cikin gida don harhada wadannan kayayyakin na’urorin aikin gona manya gaskiya ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »