African LanguagesHausa

Binciken zargin Peter Obi kan talauci da tsabta

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Leba Peter Obi, kwanan nan ya fitar da kudurin shi mai shafuka 72, wanda ya yi wa taken “Zai yiwu: Alkawarinmu da ‘Yan Najeriya”. Wannan kuduri ya gabatar da manufofin da su ka sanya a gaba, da izinin tabbatar da tsaro, hadin kai da ma mayar da Najeriya kasa mai bunkasa.

Yayin da ya ke yin matashiya ga wasu daga cikin matsalolin da ake fama da su a Najeriya da abubuwan da  su ka dace a yi, Mr Obi ya ce kashi 63 cikin 100 na ‘yan Najeriya  na zaman mutane miliyan 133 ke nan kuma wadannan mutane na fama da talauci kuma ba su da ababen more rayuwar da za su taimaka mu su wajen tsabtace muhalli da ma tsabtataccen ruwan sha misali.

Bukatar sany ido kan masu rike da mukaman gwamnati ne ya sa DUBAWA daukar nauyin tantance gaskiyae wannan zargin.

Zargi na 1: Kashi 63 cikin 100 na ‘yan Najeriya na cikin talauci

Binciken zargin Peter Obi kan talauci da tsabta

Da gaske ne!

Binciken mahimman kalmomin da suka danganci wadannan alakaluman sun kai mu ga wani rahoton jaridar Vanguard wanda ya yi amfani da wadannan alkaluman. Jaridar ta sami wannan adadi ne daga rahoton binciken 2022 na wanda dke duba yanayin talauci a fuskokn rayuwai da yawa a Kasa wato Multidimensional Poverty Index (MPI)

Rahoton na MPI wanda ya yi la’akari da fuskokin rayuwa guda hudu, wadanda su ka hada da lafiya, Illimi, matsayi ko yanayin rayuwa, da aikin yi, ya bayyana cewa kashi 63 cikin 100 na al’ummar Najeriya (miliyan 133) na fama da talauci  a dukka wadannan fuskokin da aka bayyana.

Zargi na 2: Kashi 63 cikin 100 na ‘yan Najeriya ba su da ababen more rayuwar da za su tabbatar mu su da tsabtataccen muhalli

Binciken zargin Peter Obi kan talauci da tsabta

Batun bai cika gaskiya ba

Hukumar Yaki da Cututtuka CDC na kwatanta tsabtace muhalli a matsayin samun ababen more rayuwa irin wadanda suka hada da wuraren bahaya masu tsabta da amince, da kuma samin damar tsabtace kai da muhalli yayin da ake cin moriyar ayyukan gwamnati kamar tura manyan motocin kwashe shara, kwashe kayayyakin da aka gama aiki da su a masana’antu musamman masu hadari, da kuma alkinta ruwan sha ta samar da hanyoyin fitar da wanda ba’a so da tsabtace wanda za’a yi amfani da shi.

Binciken MPI ya nuna cewa kashi 46.5 cikin 100 ne ke da matsala a wannan fannin.

“Fiye da rabin al’ummar wadanda ke fama da talauci a fuskokin rayuwa daban-daban, kan yi girki ne da takin gargajiya (wato kashin dabbobi), itace, ko gawayi a maimakon makamashi mai tsabta. Akwai kuma masu fama da matsanancin rashi wajen tsabtace kai da muhalli, lokacin zuwa asibiti, rashin abinci da rashin gida,” a cewar wani bangaren rahoton.

A Karshe

Zargin farko mai cewaa kashi 63 na ‘yan Najeriya na jin radadin talauci a fuskokin rayuwa da dama gaskiya ne. Sai dai zargi na biyu mai cewa kashi 63 cikin 100 ba su da damar samun abubuwan more rayuwar da za su taimaka da tsabtace muhalli ba daidai ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button