Cikakken bayani
Kusan kowace shekara cutar sankarau ke bulla a Najeriya, inda ake samun karuwarta lokacin rani. Cutar na da saurin yaduwa kuma tana iya kai ga hallaka cikin sa’o’i 24 kadai. Daga karshen watan Janairu, gwamnatin Najeriya ta sanar da ‘yan kasar cewa cutar sankarau na karuwa a jihar Jigawa, da rahotannin farko na cutar da ke nuna cewa akwai mutane 117 da ake zargin suna dauke da cutar da wasu 12 wadanda aka tabbatar suna da shi.
Bayan haka, Cibiyar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC ta tura wata tawagar agajin gaggawa warto Rapid Response Team zuwa jihohin Jigawa, Yobe, da Katsina dan su taimaka wajen shawo kan cutar.
Sai dai ranar 17 ga watan Fabrairu aka samu rahoton cewa akalla mutane 38 suka hallaka daga cutar a Jigawa. Barkewar cutar a jihar Jigawa ta jawo hankali kan barazanar da cututtuka masu yaduwa cikin sauri ke da shi a yankin da kuma bukatar da ake da shi na inganta wuraren kiwon lafiya da ma tsarin sanya idon kan cututtuka da yadda suke yaduwa a cikin al’umma
Cutar Sankarau da sanadin ta
Sankarau kumburi ne na wata gabar jikin da ake kira meninges da turanci, wanda wani zirin fata ne da ke hada kwakwalwa da kashin baya. Keneth Ayange, likita a asibitin Anglican da ke Kafanchan, ya ce idan har kwayar cuta ta shiga tsarin kwakwalwa da jijiyoyin jikin mutun, tabbas za’a sami kumburi a fatar da ke hada kwakwalwa da kashin baya wanda ake kira meninges.
Abubuwan da suka fi yin sanadin sankarau kwayoyin cutan bacteria da virus be. Idan dai har kwayar cuta ce ta yi sanadin cutar, kwayoyin cuta da yawa ne za su iya jany kumburin. JIn ciwo da wadansu magunguna kuma na iya janyo kumburin. Kamar yadda Dr. Ayange ya bayyana wadansu daga cikin abubuwan da kan taimaka wa cutar ta yadu sun hada da yanayin zafi ko kuma lokacin bazara.
“Rani ya kan samar da irin yanayin da sankarau ke bukata ta habaka domin bushewar hanci na sanya kan sa shi ya kasance da sauki wa kyawar cuta ta sauka a kan hancin ta yadda za’a iya shakarta. Bushewar da hanci kan yi lokacin zafi ne ke sa kwayoyin cuta shiga hancin cikin sauki, inda daga nan kuma suke samun damar zuwa sauran gabobin jikin su yi mu su lahani,” ya ce.
Wani abun da ke kara yada sankarau kuma shi ne rashin yin allurar rigakafin da ta dace da nau’in kwayar cutar da ta hadasa cutar tun farko. Barkewar cutar sankarau ba sabon abu ba ne a wasu bangarorin duniya, a ciki har da wadanda ke nahiyar Afirka inda ake kira meningitis belt da turanci, ko kuma yankin da sankarau ta fi kamari a Afirka wanda ya hada har da Najeriya. Dr Ayange ya ce wannan yankin ya hada da jihohi 19 a arewacin Najeriya wanda Jigawa ke daya daga cikin wadannan jihohin. “Sankarau na yawaita sosai a wannan yankin. Mussamman sankarau mai nau’in C wanda ake kira Neisseria meningitides, ya na banna sosai a yankin,” ya bayyana.
Alamun Sankarau
Alamun da aka fi sani sun hada da kagewar wuya, zazzabi, rashin son haske, rudani, ciwon kai, amai. A jarirari, alamun sun hada da zazzabi, yawan kuka, sai kumayawan baci, kasala, rashin kuzari da rashin cin abinci. Cutar sankarau din da kwayoyin cutar bakteriya da fungai suka yi sanadi yawanci a kan cigaba da ganin alamun na tsawon ‘yan kwanaki ko bayan an gama shan magunguna. Yana iya daukar makwanni kafin a sami cikakkiyar lafiya kuma a wadansu lahanin da sukan samu ya kan cigaba da kasancewa tare da su har abada.
Ire-iren Sankarau
- Sankarau na kwayar cutar bacteriya
Wannan nau’in yana iya yaduwa da saura kuma wata kwayar cutar bakteriya ce ta musamman ke janyo ta. Irin wannan na da mahimmanci sosaiga lafiyar al’umma saboda yana iya kasancewa sanadin mace-mace da dama. Ya na iya kasancewa annoba duk da cewa wannan ya danganci nau’in kwayar cutar bacteriya da ta yi sanadin zuwan cutar amma kuma ana iya kare kai daga kamuwa da ita kuma ana iya samun waraka.
- Sankarau mi kwayoyin cuta biyu a hade wato Virus da bakteriya
Wannan nau’in wanda aka fi sani da Viral bacteria ita ce wadda aka fi yawan kamuwa da ita. Wannan nau’in yakan tafi ba tare da an sha magunguna ba. Sai dai dole a kula da wadansu daga cikin abubuwan da ke janyo cutar.
- Sankarau na Fungi
Ba safai ake samun wannan nau’in na cutar ba. Wannan kwayar cutar ta Fungi ta kan shiga jinin mutun ne ta yadu har ta kai kwakwalwa. Mutanen da ba su da garkuwar jiki mai inganci ne ke iya samun wannan nau’in.
- Sankarau na Parasite (wato irin kwayoyin cutar da ba su iya rayuwa da kansu dole sai sun sami wani abu mai rai sun manna kansu a jikin shi domin ci da shan su)
Akwai irin wadannan kwayoyin cutar da yawa wadanda ke kasancewa sanadin sankarau. Akwai wadanda ake samu daga bayangida, dauda/bola, da kuma wadansu dabbobin da ake ci irin su dodon kodi, danyen kifi, kaji da kuma kayan gona. Sai dai ba kamar sauran nau’o’in cutar ba, da wuya mai dauke da cutar iya bai wa wani kai tsaye illa dai kwayoyin cutar za su boye cikin abincin da dan adam zai dauka ya ci musamman idan ba’a tsabtace su ba.
- Sankarau din da ba’a samu daga kwayoyin cuta
Irin wannan ba kwayoyin cuta ke janyowa kamar yadda aka bayana. A maimakon haka, sankarau ne da ke zuwa sakamakon wata cuta ta daban da mutun ke dauke da shi ko kuma wadansu magungunan da ya ke sha. Ire-iren cututtukan sun hada da jin ciwo ko kuma rauni a kai, tiyata a kwakwalwa, cutar daji, da kuma Lupus – wadda cuta ce inda garkuwar jikin mutun ke yakar kwayoyin halittar da ke cikin jikin mutun kamar yadda za ta yaki cutar da ke da lahani ga jikin mutun alhali kuma ba cuta ba ne.
- Sankarau mai dadewa
Kwayar cutar fungi, cututtukan da kan shafi gabobin jiki da kasusuwa da kuma citar daji kan janyo irin wannan cutar. Magungunan da ake sha dan wannan cutar kan mayar da hankali wajen yakar cutar da ta janyo su ne.
Yadda ake bazawa da kuma kamuwa da ita
Bisa bayanan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kwayar cutar bakteriyar da ke sanadin sankarau kan yadu ne daga mutun daya zuwa wani ne idan har wanda ke dauke da ita ya tufar da miyau ko ya fyace majina ko kuma dai wani abun da ya fito daga makogwaro ko tare da naumfashi. Dan haka dadewa kusa da mai dauke da cutar da ma yin ma’amala da su ta hanyar sumbace, atishawa, ko tari a kan wani, ko kuma zama a kusa da wanda ke dauke da cutar na taimakwa wajen yaduwar cutar.
Tsawon lokacin da cutar ke dauka ta hayayyafa a jikin mutun shi ne kwanaki hudu amma ya danganta domin wata sa’a ya kan dauki tsakanin kwanaki biyu zuwa 10. Kwayar cutar na iya buya a cikin makogwaro wara sa’a ta yadda za ta karya garkuwar jikin mutun ta shiga cikin jini daga nan har ta taba kwawalwa.
Muhammad Adamu, likita da ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa ya gano wadansu daga cikin abubuwa da ke karar asasa yaduwar cutar ta sankarau a yankin. Cunkosi da talauci a al’ummomin da abun ya shafa, da ambaliyar ruwa a jihar Jigawa duka mahimman abubuwa ne. Musamman cunkoson jama’ar da ke samu sakamakon yadda su ke neman wuraren sa kai na wani gajeren lokaci bayan da ambaliyar ruwa ta dauke musu matsugunnensu,” ya ce.
Kariya daga kamuwa da cutar sankarau
Fadakar da al’umma dangane da yaduwar sankarau na da mahimmanci ga yakar cutar saboda ana iya shakarta a iska, Dr Ayange ya jaddada bukatar ilimantarwa da fadakar da al’umma ya na kwatanta matakai masu nasarar da aka dauka lokacin da annobar COVID-19 ta kai kololuwarta. Likitan ya bukaci da a horas da jami’ai ta yadda za su rika gane cutar a kan kari, inda ya ce al’ummar ta yi yawa sosai kuma adadin likitocin ba zai wadata yadda ake bukata ba
A matakin mutun da al’umma, kula da kai na da mahimmanci sosai. Wannan ya hada da samun hutu sosai, kada a sha taba sigari, a guji cudanya da wadanda ke dauke da cutar, wanke hannuwa a kai-a kai duk suna da mahimmanci wajen dakile yaduwar cutar. Allurar rigakafi tana iya kare mutane daga kamuwa daga cutar.
A jihar Jigawa, Dr MUhammad Adamu ya ce mahukuntan jihar sun riga sun sanar cewa akwai yiwuwar barkewar cutar a jihar bana, kuma sun dauki matakan rage yaduwarta. Alal misali, ma’aikatar lafiya ta jihar ta tanadar da wannan shirin da zai gano wadanda suka kamu da cutar a cikin al’umma a basu magunguna tun kafi ya fara yaduwa zuwa na kusa da su. Gwamnatin na kuma bayar da magunguna kyauta ga duk wadanda suka riga suka kamu da cutar.
Yadda ake maganin cutar sankarau
Maganin sankarau ya danganci irin nau’in da ake dauke da shi. Wanda ke dauke da nau’in bakteriya na bukatar magungunan antibiotics – magungunan da ke hana habaka da kuma kashe kwayoyin cuta. Wadanda kwyar cutar virus ta janyo na iya tafiya cikin mao guda. Wadanda kuma kwayar cutar fungi ta janyo (Wadansu kan kira fungi naman gwari) ana iya amfani da magungunan da ke yaki da kwayar cutar wajen kashe su, wadanda ake kira antifungal.
A karshe
Yayin da aka sami nasarar amfani da alluarar rigakafi wajen yaki da yaduwar cutar sankarau, akwai sauran aiki a gaba musamman wajen tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun sami duk bayanai da sauran abubuwan da suke bukata wajen shawo kan barkewar cututtuka masu lahani. Yaki da cutar sankarau na bukatar matakai da yawa wadanda za su hada da hadin kan masu ruwa da tsaki kama daga gwamnati zuwa al’umma domin dakile cutar tun daga tushe.