African LanguagesHausa

Bidiyon Olumide Oworu a lokacin da yake nadar fim ne ake amfani da shi da zargin wai an kai masa Hari

Zargi: Hoton dan takarar majalisar jihar Legas a karkashin inuwar jam’iyyar LP Olumide Owuro inda aka nuno jina-jina an dauka lokacin da aka kai ma sa harin ne a ofishin yakin neman zaben shi

Sakamakon binciken: Babu cikakken gaskiya. Binciken mu ya nuna mana cewa hoton inda aka ga Mr Owuro jina-jina daga wani fim ne da aka yi. Ba sakamakon wani harin da aka kai kan tawagar yakin neman zaben sa ba ne.

Cikakken Bayani

Kasa da sa’o’i 48 kafin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a Legas, wani hoto ya bulla na Olumide Oworu, da fuska jina-jina, wato dan takarar majalisar jiha a Legas daga mazabar Surulere 1 a karkashin jam’iyyar LP.

Bayanai sun ce ‘yan daba ne suka kai hari kan Mr Oworu da magoya bayan sa ranar Alhamis 16 ga watan Maris 2023, kamar yadda gidan talibijin na Channels ya rawaito.

Hoton da ke yawo a duniyar gizo-gizo bayan da aka yi zargin harin ya nuna Mr Owuro da da jina ko’ina a fuskarsa da rigar da ya ke sanye da ita, tare da zargin cewa ‘yan daban da jam’iyyar APC suka yi haya ne suka yi mi shi dan banzan duka lokacin harin kwanton baunar da suka yi masa.

Wani mai amfani da shafin twitter, @omolerinjare, ya wallafa hoton tare da zargin cewa Desmond Elliot ne ya shirya harin. Bayan shi, wani kumamai suna @ayemojuba shi ma ya wallafa labarin tare da taken cewa, “‘Yan daban APC sin kai gari kan.”

Ganin yadda wannan batun ke da sarkakiya ne ya sa muka dauki nauyin tantance gaskiyar wannan batun gabannin zaben.

Tantancewa

Binciken da kungiyar bincike da tantance gaskiyar bayanai ta FactCheckHub ta gudanar ya nuna cewa hoton Mr Oworu ya dade a shafukan sada zumunta ya kai wajen watanni biyar. Mr Oworu wanda dan wasan kwaikwayo wanda ya fito a fina-finan Nollywood da dama wanda kuma ya sami lambobin yabo da yawa saboda wasu daga cikin fitowar da ya yi, ya sanya hoton a shafinsa na instagram tare da taken da ya bayyana cewa fim ne ake dauka.

Ya wallafa hoton ranar 3 ga watan Oktoban 2022,  da taken “ALagbado John Wick. #OntheEdge a shafinsa na Instagram.

Haka nan kuma, ba mu iya tantance sahihanci labarin cewa ‘yan daban APC ne suka kai mi shi harin ba yayin da muke rubuta wannan rahoton.

A karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa hoton da aka yada na Mr Oworu jina-jina daga daya daga cikin fina-finan da ya yi ne.

FactCheckHub ta rubuta wannan labarin yayin da DUBAWA ta sake wallafawa a matsayin wani yunkurin hadin gwiwa na masu bincike da tantance gaskiyar bayanai. Dan karanta ainihin labarin da suka rubuta latsa nan

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button