Getting your Trinity Audio player ready...
|
Bincike: Wani rahoton BBC Pidgin ya tabbatar da sahihancin bidiyon da aka dauka a adireshi mai lamda 016 ko kuma makarantar Ahmadiyya Grammar School, da ke Owo.
Nazarin bidiyon da aka yi ta yin amfain da manhajar INVID ya nuna cewa ba dadadewa ba aka sanya bidiyon cikin shafukan yanar gizo. An zantawar da aka yi da Fidelis David wani mai sanya ido daga jaridar TheCable ne ya tantance cewa harshen da aka yi amfani da shi wanda ake amfani da shi a Owo ne. Mr David wanda ya kasance a Owo tun da sassafe ya ce duk da cewa shi bai ga musayar kudin da ake zargin an yi da idanunsa ba, ya lura cewa akwai wadanda sukan kada kuri’a sai su je gefe su nuna wa wasu wanda suka zaba kafin su jefa ta a cikin akwatin. Wata kila suna yin hakan ne saboda kudin da aka alkawarta musu.
Haka nan kuma, shi ma Ayodele Oluwafemi, wani mai sanya ido daga TheCable a karamar hukumar Kiribo Ese-Odo, ya fadawa NFC ya ce shi ma bai shaida karbar kudin da ido ba, amma ya ga wasu suna karbar wata ‘yar takarda wadda za su yi amfani da shi anjima su karbi abin da aka alkawarta musu.

Hukunci: Gaskiya ce
Majiyoyi: Masu sanya ido,manhajar INVID, BBC Pidgin
Kwanan wata : 16/11/2024
Mawallafiya: Elizabeth Ogunbamowo
EDITOCI: Ajibola Amzat, Simbiat Bakare, da Opeyemi Kehinde