African LanguagesHausa

Da gaske ne! Ana iya samun kayan gwajin kwayoyin halitta na DNA da arha amma samun sakamakon na da dan karen tsada

Zargi: Kayan gwajin kwayoyin halitta na DNA a gida ana iya samun su a kan  £ 4.99 (kudin Burtaniya)

Da gaske ne! Ana iya samun kayan gwajin kwayoyin halitta na DNA da arha amma samun sakamakon na da dan karen tsada

Duk da cewa ana iya samun kayan gwajin a kan farashi mai rahusa, samun sakamakon na da tsada sosai dan haka ba komai ne gaskiya dangane da wannan batun tunda daga karshe dai za’a biya kudi mai yawa

Cikakken bayani

Zamba irin wanda ya danganci rashin bayyana mahaifan yara ko iyayensu na gaskiya har sai lokaci ya kure ya kasance babban abin mahawara a Najeriya, musamman a shafukan soshiyal mediya, inda ake samun labarai da dama na ma’auratan da ke wa juna zamba cikin aminci.

Kwanan nan hoton wani abin da ake gwajin kwayoyin halittar da aka fi sani da DNA a turance, wanda ke tantance dangantakar iyaye da yaransu da ma sauran dangi, ya dauki hankali bayan da aka fara zargin cewa yanzu ma’aurata za su fara samun matsala tunda an sassauta farashin kayan gwajin dan haka gano iyayen yara na gaskiya zai zo da sauki.

Wani mai amfani da shafin tiwita ya raba hoton wanda ya fara bulla a shafin Tiwitar Naija_PR da taken “Za’a yi fama da bakin ciki, da hawaye da zud da jini.”

Hoton kayan gwaji na DNA, wanda ya yi kamar an dauka ne a shago ya nuna farashin shi a kan £ 4.99 (kudin Burtaniya)

Wata mai amfani da shafin Tiwita UGOEZE @AkunneChinyere4 da wallafa hoton da tsokaci kamar haka “Kayan gwajin DNA a gida yanzu £ 4 wanda ke zaman kusan Nera 2000 a kudin Najeriya. Ku yi yadda ku ke so da wannan bayanin.”

Wani mai amfani da shafin Nnaemeka Ekele @nnaemekaekele a na sa ra’ayin cewa ya yu wannan zai halaka aurarraki

“£5 kacal wa kayan gwajin DNA, wannan zai rugurguza aurarraki da yawa, amma dai yana da kyau domin ya kamata mutane su san abubuwan da ke faruwa a kewaye da mu kowace rana,” ya bayyana

Wannan hoton ne ma aka yi amfani da shi a sauran shafuka da dama wadanda suka hada da Facebook a shafin Gistlover, Ibadan info da digitv.live

A ‘yan kwanakin da su ka gabata, masu shafin GistReel.Com su ka wallafa hoton suna tambayar masu ma’amala da shafinsu ko za su saye kayan gwajin.

Mahimmancin wannan zargin ya sa mu ke so mu binciki gaskiyar wannan batun.

Tantancewa

Da muka tantance hoton a shafin google, ya nuna mana cewa kamfanin AlphaBiolabs ne su ke sarrafa wannan kayan gwajin na DNA. Wani rahoton da aka yi a shajin jaridar Mirror.co.uk ya ce wani shago mai suna Home Bargains ne ke sayar da shi.

Kayan Gwajin DNA na AlphaBiolabs

Kayan gwajin na AlphaBiolabs wanda ake samun shi a kan farashin £4.99 na bukatar karin wani £99 na daban da samun sakamakon wanda shi ma za’a biya kamfanin kai tsaye.

Kwalin kayyakin ya kunshi audugan da ake amfani da shi a dauki miyau a kuma goge jikin fatar kumatun da ke cikin baki, da takardun nuna amincewa da gwajin wadanda dole sai an cika an sanya wa hannu kafin a tura gwajin zuwa dakin bincike. Ana iya samun sakamako wuni guda bayan an tura kuma a kan tura sakamakon zuwa adireshin email tare da kalmomin sirri na musamman domin tabbatar da tsaro.

Ana iya amfani da kayan gwajin wajen gane mahaifiya, danuwa wanda cikin ku daya, kaka, ‘yan biyu, goggo, kawu da kuma Y Chromosome wato tantancewa ko gano ainihin jinsin mutum. Yana dauke da yawan audugan da zai iya tantance dangantakar da ke tsakanin mutane biyu.

Nawa ne ake gwajin DNA a Najeriya? 

Bisa bayanan da mu ka samu a shafin smartdna.com akwai ire-iren gwajin da ake gudanarwa kuma farashin su ya danganta.

Misali a gwajin da ake yi kan mace mai juna biyu dan gano mahaifin dan da take dauke da shi tun kafin ta haihu, ba tare da an yi wani aiki ko tiyata ba a Najeriya, farashin na reto tsakanin Nera 800,000 da Nera Milliyan daya da rabi (N 1.5 million), kuma ya danganci asibitin. A waje guda kuma, gwajin DNAn da ake yi bisa dalilai na kaura/tafiya ko komawa kasar waje da zama, da ma tantance ainihin mahaifin yaro bisa tanadin doka ana yin shi ne kan farashin N200,000 zuwa N300,000. Shi ma ya danganci asibitin da aka je.

Dab haka, farashin kanyan yin gwajin na kan £4.99 wanda kwatankwacin N2,694 ke nan yayin da kudin samun sakamakon kuma ke kan £99 shi kuma N53,460 a kudin Najeriya idan aka yi amfani da darajar da Babban Bankin Najeriya ke canjin kudaden kasar waje wanda ke kan N540 kan kowace dalar Amurka.

Duk da cewa wannan ya fi arha idan aka kwatanta da yawan kudin da asibitoci ke karba a Najeriya, ba kowane dan Najeriya ba ne zai iya kashe wannan kudin.

A karshe

Duk da cewa gaskiya ne akwai kayan gwajin kwayoyin halittar dan adam na DNA a gida wanda ke kan farashin £4.99 akwai wani karin kudin da za’a yi daga baya idan har ana san samun sakamako. Wato dole sai an kara £99.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button