Zargi: Tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi ya kara yawan kudaden shigar da jihar ke samu daga Nera biliyan 7 zuwa biliyan 8 cikin shekaru 8 din da yayi yana mulki, yayin da shi kuma El-Rufai ya kara yawan na Kaduna daga Nera biliyan 15 zuwa biliyan N 93

Yawancin bayanan gaskiya ne
Cikakken bayani
Yayin da hankula ke cigaba da karkata zuwa sakamakon zaben 2023 ‘yan Najeriya da dama sun koma soshiyal mediya inda kowa ya ke nuna goyon bayansa ga dan takarar da ya fi so.
Wadansu magoya bayan su kan wuce gona da iri wajen bayyana goyon bayansu inda suka hadawa har da zage-zage da suka ga mambobi ko ‘yan takaran da su ke bangaren da ake hammaya da su. Wasu kuma na su shi ne kaga labarai marasa gaskiya ko kuma dai wadanda za su yaudari mutane dangane da ‘yan takaran da ba su so – dan dai kawai su nuna cewa na su ya fi.
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar Leba ya shiga kanun labarai kwanan nan bayan da bayyana wadansu alkaluman da suka shafi lokacin da ya yi gwamna a jihar Anambra.
Shimfida
Mr Obi ya sami damar kasancewa gwamna a jihar Anambra ne a karkashin inuwar jam’iyyar APGA ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2006, sai dai tun kafin a kai ko’ina aka tsige shi ranar 2 ga watan Nuwamban 2006, watanni bakwai bayan ya yi rantsuwar kama aiki.
Da hakan ya faru, Obi bai karaya ba nan da nan ya kai lamarin kotu inda ya sami nasara a shari’ar, kuma kotun daukaka kara da ke zaune a Enugu ta mayar da shi kan kujerar gwamnan ranar 9 ga watan Fabrairun 2007.
Watanni bayan nan an sake yin wani zaben a watan Afrilun 2007 wanda ya kawo Andy Uba a matsayin gwamna sai dai kwanaki 16 kadai Uba ya yi a kan kujerar kafin Kotun Kolin kasar ta umurce shi da ya bar kujerar dan Mr Obi ya cigaba da shugabancin jihar.
Mr Obi ya sake takarar neman kujerar gwamnan dan yin wa’adi na biyu, ya kuma yi nasara ta yadda sai ranar 7 ga watan Maris 2014 wa’adin sa ya kare.
Bayan da ya bar wannan mukamin, ba a sake jin duriyarsa a fagen siyasa ba sai shekarar 2019 lokacin da ya tsaya takarar neman mukamin mataimakin shugaban kasa tare da Turakin Adamawa wato Atiku Abubakara karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
A watan Maris na 2022 Mr Obi ya nuna sha’awarsa na tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar a zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyarsa ta PDP, to sai dai burinsa na yin hakan ta dakushe baya da a watan Mayun tsohon abokin takarar ta sa Atiku Abubakar ya kasance dan takarar mukamin shugaban kasa na jam’iyyar.
Daga nan ne Mr Obi ya sauya sheka ya koma jam’iyyar Leba inda nan da nan ya sami damar kasancewa dan takararta na mukamin shugaban kasa.
Bayan da ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Leba, Mr Obi sai ya sami damar yin hammaya dan manyan ‘yan takarar mukamin a mataki na uku, wato yana biye da Atiku Abubakar na APC da Bola Ahmed Tinubu na APC.
Wannan ne ma ya janyo mahawarori dangane da Mr Obi da irin nasarorin da ya yi lokacin da ya ke gwamna a jihar Anambra na tsawon shekaru 8.
Ba da dadewan nan ba ne wani mai amfani da shafin tiwita ya yi zargin cewa irin kudaden da jihar Anambra ke samu daga tattalin arziki da sana’o’in da ake yi cikin gida a jihar ya karu daga Nera biliyan 7 zuwa 8 a cikin shekaru 8 din da ya yi mulki a jihar (wato karuwar Nera biliyan guda)
Wannan bayani ya janyo cece-kuce sosai dangane da ko zai iya jagoranci da ma ko akwai fannoni da ya dara Tinubu da shi, wanda aka ce shi ma ya inganta tattalin arzikin jihar Legas lokacin ya na gwamna.
Mutane da yawa a cikin masu amfani da tiwita sun yi ta wallafa labarin abin da ya sa batun ya kara daukar hankalin jama’a.
A cewar Leong UKpong, farfesa a fanin kudi da tattalin arziki a makarantar kasuwanci ta jami’ar Amurka da ke Yola, jihar Adamawa, Abin da kasa ko jiha ke samu kowace shekara daga kowani fanni ne ake fara la’akari da shi idan har ana so a gwada bunkasar tattalin arziki ba kudaden da ke shiga ba.
Mr Ukpong daya daga cikin shugabannin makarantar ya fadawa DUBAWA cewa ana samun kudaden shiga yawanci daga haraji ne, kuma idan haraji na da yawa, zai rage wa al’umma karfin sayen kayayyakin masarufi.
“Kudaden shiga na IGR ba wani abu ba ne illa haraji. Za ka iya kara yawan haraji a kan mutun guda, ko a birni ko kuma ma a kasa amma kuma ba ya nufin cewa tattalin arziki na bunkasa. Hasali ma ana kashe kasar ne da yawan haraji. Abin da ya ke nuna bunkasar tattalin arziki shi ne yawan abin da ake samu daga duka fannonin tattalin arzikin kasa kowace shekara wato GDP,” ya ce.
“Alal misali, a ce akwai mutane biyu a jihohi biyu, wadanda kowannensu na samun Nera 1,000 a matsayin albashi ko kuma dai kudin shiga. Mutumin da ke Kaduna na iya biyan kashi 60 cikin 100 na wannan kudin a matsayin haraji yayin da wanda ke dayan jihar ke biyan kashi 20 cikin 100. Idan mu ka yi la’akari da haka, za mu yi tunanin Kaduna ce ke bunkasa sosai saboda yawan kudin alhali kuma ba haka ba ne dan IGR ba ya nufin bunkasar tattalin arziki.
“Wata sa’a ma idan har kudaden shiga suka yi yawa, tattalin arzikin kasa ba ya ma bunkasa. Haraji kan cire kudi ne daga jimilar kudin da mutun ke samu, idan har aka dauki kudi da yawa, da kyar mutun ke samun kudin da zai iya batarwa har a samu abin da zai shiga fannonin da ke bukata domin a samu bunkasar tattalin arziki.
“Har wa yau misali, idan mutun na samun N100,000 kowace wata kuma ana biyan harajin kashi 40 cikin 100 wannan na nufin mutun zai je gida da N60,000 ne kacal. Kudin ba zai ishi mutun ya sai wadansu abubuwa ba. Idan haraji ba shi da yawa, mutane za su iya sayayya sosai abin da ake kira kudin batarwa. Yawancin kasashe wata sa’a rage yawan haraji su ke yi dan mutane su iya kashe kudi kan wadansu abubuwa ta yadda kowani fanni zai dan sami bunkasa, irin wanda zai iya kai ga bunkasar tattalin arziki baki daya.
“Idan mutun na samun kashi 60 ne kadai na albashi dole zai rage kashi kudi ya mayar da hankali kan irin abubuwan da su ka wajaba, saura irin su zuwa hutu, ko sayen kujeru da abubuwa irin su DSTV ba za su yiwu ba, kuma idan mutun ya yi haka wannan tabbas zai rage bunkasar tattalin arziki.”
Zargin Farko: Peter Obi ya kara yawan kudaden shiga na IGR da Nera biliyan guda cikin shekaru 8 din da ya yi shugabanci a jihar Anambra
Kamar yadda Akanta Janar na jihar Anambra ya gabatar a rahoton bayanan kudin jihar na shekarar 2006 wanda akanta janar na wancan lokacin, Mrs. V. A Obinwa ta sanyawa hannu, jimilar kudaden shigar da jihar ta samu a karshen shekarar 2006 shi ne Nera biliyan 4.6, abin da ya nuna raguwa sosai daga abin da ta samu a shekarar 2005 wato Nera biliyan 7.3.
A shekarar 2007, bayanan kudin da akanta janar na jihar a wannan shekarar Barrister R.H.C Ogbogu ya nuna cewa IGR din ya karu domin an sami Nera biliyan 6.02 yayin da a 2008 aka sami Nera biliyan 6.06, a 2009 aka sami Nera biliyan 6.05.
Bayanan da muka samu daga ofishin Hukumar Kididdiga ta Kasa dangane da kudaden shiga a matakin jihohi daga shekarar 2010 zuwa 2012 ya nuna cewa a 2010 Anambra ta sami Nera biliyan 7.7, sa’annan a 2011 kudaden ya ragu zuwa Nera biliyan 6.1.
A waje guda kuma, wani bayani da aka wallafa na hadin gwiwa tsakanin Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS da hadaddiyar Hukumar Haraji ya nuna cewa jihar ta sami Nera biliyan 7.6 a shekarar 2012 a yayin da ta sami Nera biliyan 8.7 a shekarar 2013 shekara guda kafin wa’adin Obi ya cika.
A shekarar 2014 abin da jihar ta ke samu ya kai Nera biliyan 10.4 bisa bayanan da muka samu daga Hukumar Kididdiga NBS.
Sai dai DUBAWA ta lura cewa rahoton akantan janar din da ke bayani kan IGR bai bayyana kudin harajin da ake samu daga kayayyakin da ake saye da sayarwa a cikin gida ba wato VAT. Mr Ukpong masanin tattalin arziki kuma malami a jami’ar Amurka ya fadawa DUBAWA cewa VAT wani bangare ne na IGR kuma ana hadawa har da shi wajen lissafa duk abubuwan da ke karkashin kudaden shiga.
Dan haka, DUBAWA ta ga ya kamata ta hada kudin VAT din da ke rahoton akanta janar da kudin IGR din da ya gabatar tsakanin shekarun 2006 zuwa 2009. A 2006 VAT din da aka samu na zaman Nera biliyan 2.7 abin da ya karu zuwa Nera biliyan 3.5 a 2007. Jihar ta sami Nera biliyan 4.67 a 2008 da kuma Nera biliyan 4.6 a 2009.
A Karshe
Zargin cewa kudaden shiga a jihar Anambra ya tashi daga Nera biliyan 7 zuwa biliyan 8 cikin shekaru 8 gaskiya ne. Bayanan da muka samu sun nuna cewa an sami raguwa a kudaden shigan daga Nera biliyan 7 zuwa Nera biliyan 4 tsakanin 2005 da 2006, shekarar da Obi ya zama gwamna. Amma an samu bunkasa a hankali har zuwa Nera biliyan 8.7 a shekarar 2013, watanni kalilan kafin ya sauka daga kujerar mulkin jihar.
Zargi na biyu: El-rufa’i ya kara yawan IGR a Kaduna daga Nera biliyan 15 zuwa Nera biliyan 93
Nasir El-Rufa’i gwamnan jihar Kaduna wanda aka rantsar da shi a watan Afrilun shekara 2015 ya yi tazarce a 2019 dan kammala wa’adinsa a shekarar 2023.
Mr. El-Rufai, ya kasance ministan Birnin Tarayyar Abuja daga 2003 zuwa 2007 ya kuma taba kasancewa darekta a Ofishin Kasuwancin Gwamnati (wato Bureau for Public Enterprise BPE)
El-Rufa’i wanda ke zaman daya daga cikin mambobin da su ka kafa jam’iyyar APC ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasarsu Mr Bola Ahmed Tinubu wanda ke hamayya da Peter Obi.
Wadansu masu amfani da shafin tiwita na zargin wai EL-Rufai ya yi amfani da wani tsarin da dan takarar shugaban kasar ya kirkiro ne wajen habaka yawan kudaden shigar jihar Kadunan.
Mr. Tinubu ya kasance gwamnan jihar Legas daga 1999 zuwa 2007. Binciken DUBAWA ya nuna cewa kudaden shigan Legas a 1999 ya kasance Nera biliyan 14.6 amma a lokacin da Tinubu ya sauka daga mukamin gwamna a jihar a shekarar 2007 kudin ya karu matuka zuwa Nera biliyan 83.02. To sai dai akwai lokutan da aka rika samun koma baya tsakanin shekaru 8 din da ya yi yana mulki.
Magoya bayan Tinubu wadanda ake wa inkiya da ‘BATists’ abin da aka samu bayan da aka takaita sunarsa zuwa BAT, ta yin amfani da harrufan farko da ke sunayen shi uku wato Bola Ahmed Tinubu (sai aka kara …ist), a wasu lokuta sun yi ta zargin cewa kudaden shigan da jihar Legas ta samu a shekarar 1999 ya kai Nera miliyan 600 kuma ta sami bunkasa sosai ganin yadda a yanzu haka kudaden shigan sun kai Nera biliyan 753.4 abin da ke nuna tasirin aikin da Tinubu ya yi duk da cewa tun 2007 ya kammala wa’adinsa na gwamna a jihar.
Tantancewa
Da muka yi amfani da bayanan da muka samu daga Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS, kudaden shiga a jihar Kaduna a karshen shekarar 2015 ya kasance Nera biliyan 11.5, abin da ya nuna an sami faduwar kashi 9.75 cikin 100 idan aka kwatanta da abin da aka samu a shekarar da ta gabata inda aka sami Nera biliyan 12.7.
A shekara ta gaba wato 2016 jihar Kaduna ta sami Nera biliyan 23 ko 17.05 wanda kari mai yawa ne idan aka kwatanta da shekarar baya.
Akwai alkaluman da su ke karo da juna dangane da kudaden shigan jihar Kaduna na shekarar 2016. A wani rahoto, Hukumar Kula da Kudaden Shiga na Cikin Gida ta yi zargin cewa Nera biliyon 23.5 aka samu a 2016. A wani rahoton kuma, ita hukumar da kan ta, ta sake cewa Nera biliyan 17.5 aka samu.
A shekarar 2017 kudaden shigan Kaduna ya kasance Nera biliyan 26.5 wanda ya nuna an sami kari da wajen kashi 15.23 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. A shekarar 2018 jihar ta sami Nera biliyan 29.4 daga harajin kan albashin ma’aikata, harajin da ake sanyawa ‘yan kasuwa da ma’aikata masu zaman kansu, harajin tituna da sauran ire-iren harajin da jihar ke samu.
NBS ta rubuta Nera biliyan 44.9 a matsayin kudin da Kaduna ta samu a 2019. A 2020 ana kiyasin abin da jihar ta samu ya kai Nera biliyan 50.7 a yayin da a 2021 aka sami Nera bikiyan N52.8. Har yanzu ba a kai ga wallafa bayanin abin da jihar ta samu a 2022 ba.
A Karshe
Zargin wai El-Rufa’i ya kara yawan kudaden shigan Kaduna daga Nera biliyan 15 zuwa Nera biliyan 93 ba gaskiya ba ne. Bayanan da hukumomin gwamnatin jiha da ma na kasa suka gabatar sun nuna cewa kudaden shiga mafi yawa a jihar tun da EL-Rufa’i ya fara mulki shi ne Nera biliyan 52.8 kuma a shekarar 2019 aka sami wannan adadin.