Fact CheckHausaPolitics

Da gaske ne Ganduje da Gawuna sun kaiwa Abba Gida Gida ziyara a Gidan Gwamnatin Kano?

Da’awa: Tsohon Gwamnan Kano Ganduje da Tsohon Dan Takarar Gwamnan Kano na APC Gawuna sun kaiwa Gwamnan Kano Abba Gida Gida Ziyara a gidan gwamnatin jahar Kano.

Hukunci: Karya ce! Da aka bincika hoton an gano cewa tsohon hoto ne da aka dauka lokacin taron jiga-jigan jam’iyyar APC.

Cikakken Bayani

Wani bayani da aka wallafa a shafin yanar gizo na HausaTrends kuma aka yada shi a Facebook a nan ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da tsohotn dan takarar gwamnan a karkashin inuwar jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna, sun kaiwa Gwamnan jihar Kano Abba Kabiru Yusuf (Gida-Gida) a gidan gwamnatin jihar.

Bayanin wanda aka wallafa tare da wani hoto, ya nuna Ganduje da Gawuna da kuma Murtala Sule Garo tsohon dan takarar mataimakin gwamnan APC a zaune kan kujera.

Tun bayan da Kotun Koli ta Najeriya ta tabbatar da nasarar zaben Abba Yusuf a matsayin gwamnan Jihar Kanon, ake ta rade-radin cewa za’a sasanta tsakanin NNPP da APC.

A can baya, an jiyo Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje yana roƙon Gwamnan Abba Kabir Yusuf da ya bar jam’iyyar NNPP ya koma ta APC, kamar yadda kafar yada labarai ta TRT Hausa ta wallafa.

Shin ko da gaske ne Ganduje da Gawuna sun kaiwa Gwamnan Kano Abba Gida Gida Ziyara a gidan gwamnatin jahar Kano?

DUBAWA tayi bincike don tantance sahihancin wannan labarin, saboda kaucewa shiga rudani tsakanin magoya bayan manyan jami’iyyun biyu a jihar Kano. 

Tantancewa

Mun yi amfani da manhajar tantance hotuna ta Google domin gano dukkanin wurin da aka taba amfani da hoton da aka wallafa labarin da shi, mun gano cewa wannan hoton daya ne daga cikin hotunan da aka dauka a yayin wani taron da jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Kano suka gudanar kwana daya bayan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar 12 ga watan Janairu na 2024, inda Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Abba Gida-Gida a matsayin zababben gwamnan jihar Kano.

Hoton da aka zakulo a shafin Instagram

Ga matsayar da shugabannin suka fitar a ranar 19 ga watan Janairu (nan), kwana shida bayan wannan taro.

Hakama a binciken da muka yi domin tantance wannan labari mun gano cewa, babu wata kafar yada labarai ta cikin gida Najeriya ko kasar waje da ta wallafa labarin ganawar da shugabannin bangarorin biyu suka yi, wato APC da NNPP a jihar Kano.

Rashin wallafa wannan labari da jaridu suka yi ya nuna cewa ba’a yi wannan taron ba kamar yadda shafin HausaTrend ya wallafa, kasancewar ganawa irin wannan zata kasance babban labari da kafafen yada labarai zasu dauka domin yada shi ga al’umma.

Haka kuma ba wani bayanin da ya fito daga bangaren gwamnatin jihar Kano akan wannan labarin, hasalima a ranar da aka yi da’awar an gudanar da taro wato 21 ga watan Maris, Gwamnan Kano ya shiryawa Shugabannin hukumomin gwamnatin sa taron buda baki na azumin watan Ramadana a gidan gwamnati.

Mun yi kokarin ji daga bakin Kakakin Gwamnatin Jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ta hanyar kira da kuma tura masa sakon kar ta kwana amma har zuwa hada wannan labarin bamu ji daga gare shi ba. Da muka tuntubi Shugaban Jam’iyyar NNPP a jihar Kano Hashim Sulaiman Dungurawa yace ba zai iya magana ba saboda yayi tafiya wani gari wurin aiki. 

A Karshe 

Labarin dake cewa Tsohon Gwamnan Kano Ganduje da Tsohon Dan Takarar Gwamnan Kano na APC Gawuna sun kaiwa Gwamnan Kano Abba Gida Gida Ziyara a gidan gwamnatin jahar Kano Karya CE! 

An yi wannan binciken ne karkashin shirin Binciken Gaskiya na DUBAWA wato Indeginous Language Fact-Checking 2024, tare da hadin gwiwar Vision 92.5FM, Sokoto, domin dabbaka labarun “gaskiya” a cikin aikin jarida da karfafa ilimin yada labarai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button