Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya yi da’awar cewa gwamnati ta hana a fita da masara zuwa kasashen waje kuma an bada damar shigowa da masarar a Nijeriya.

Hukunci: Yawanci Gaskiya ne! Gwamnatin Nijeriya ta haramta fita da masara zuwa kasashen waje, sai dai ta bayar da damar shigowa da masarar ne tsakanin watan Augusta zuwa Disamban 2024.
Cikakken Bayani
Farashin kayan abinci a Najeriya ya tashi sosai a kasar inda alkaluma daga hukumar kididdiga ta kasar suka nuna cewa, a watan Disamba kawai an ma’aunin hauhawar farashi ya kai kashi 34.80% sabanin yadda yake a watan Nuwamba kashi 34.60. Sai dai a kididdigar da aka yi ta watan Janairu an ga yadda tashin farashin ya sauka zuwa kashi 24.48, abinda hukumar ta alakanta da sake sauya tsarin yin lissafin hauhawar farashin kayayyaki.
A gefe daya ‘yan kasar na zargin gwamnati da daukar wasu matakai da suke ganin na kara jefa al’umma cikin wahala.
Wani mai amfani da shafin X Extraordinary Ustaz (@bapphah) ya yi da’awar cewa an bada damar shigo da masara da shinkafa daga kasashen waje yayin da aka hana shigowa da ita a cikin Najeriya.
An wallafa irin wannan a shafin Facebook a wurare da dama kamar yadda muka zakulo a nan da nan.
Dubawa ta bi diddigi domin gano gaskiyar wannan lamarin a kokarin wayar da kan al’umma akan labarai na gaskiya.
Tantancewa
Bincike ya nuna cewa tun a watan Satumban 2020 ne, babban bankin Nijeriya CBN ya dakatar da shigowa da masara kasancewar a wancan lokacin gwamnati na kokarin bai wa manoma damar samar da abinci cikin gida.
Akan batun shigowa da kayan abinci daga waje, Dubawa ta gano cewa a watan Yulin 2024, gwamnatin Najeriya ta amince da bude iyakokin kasar tare da janye harajin kayan abinci na tsawon watanni biyar, ciki har da masara, domin samar wa ‘yan kasar sauki akan hauhawar farashin kayan abinci da ya jefa ‘yan kasar cikin mawuyacin hali, haka kuma gwamnatin ta ce za ta hannu da jihohi domin karfafa noma.
Sai dai a watan Oktoban 2024 kasa da wata uku da majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta aiwatar da dokar haramta fitar da kayan abinci zuwa kasashen waje domin daidaita farashinsa a nan cikin gida Nijeriya.
Bayan haka ne majalisar dattawa ta amince da wani kudirin doka da zai haramta fitar da masara zuwa kasashen waje wanda ta yi duba akai tare da sanya hukuncin shekara daya a gidan yarin ga duk wanda aka kama ya fitar da masara mai yawa da ta kai tan daya daga cikin Najeriya zuwa wasu ƙasashen.
A shafin yanar gizo na hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, Dubawa ta ga an sanya masara a cikin jerin abubuwan da aka haramta fita da su a kasar.
A Karshe
Yawanci gaskiya ne, gwamnatin Nijeriya ta haramta fitar da masarar da ta kai nauyin tan daya domin samar da abinci cikin gida, haka kuma ta bayar da damar shigowa da masara tare da janye harajin da za a biya na watanni biyar kacal domin saukaka farashin abinci.