African LanguagesHausa

Da gaske ne hukumar INEC ta take ‘yancin zaben wasu bayan da ta sauya mu su rumfunan zabe?

Zargi: Wani sakon WhatsApp da ke yawo na zargin wai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta na canza wa wasu wuraren zabe dan ta hana su damar jefa kuri’unsu baki daya.

Da gaske ne hukumar INEC ta take ‘yancin zaben wasu bayan da ta sauya mu su rumfunan zabe?

Karya ce! Duk da cewa INEC ta kara sabbin wuraren zabe sa’annan ta sauya wa wadansu rumfuna, ta yi hakan ne yankunan da wadanda suka cancanci kada kuri’ar suka yi rajista, domin burin shi ne ta rage yawan mutane a rumfunan zaben da kada a sami cunkoso ba wai dan a take ‘yancin zaben jama’a ba.

Cikakken bayani

Yayin da ranar zabe ke kara kusantowa, abin da ya fi damun wadanda suka yi rajistar zuwa su jefa kuri’un su shi ne wuraren zaben ko kuma Polling Unit wato PU, da yadda za su gane su. 

Kwanan nan, wani sako ya rika yawo a  WhatsApp da zargin wai INEC na sauya wa mutane rumfnan da za su je su yi zabe, wadanda yawanci sun banbanta da inda suka je suka yi rajista.

Sakon ya kuma kara da yi wa jama’a gargadin cewa su yi hattara, domin mallakar katin zabe na PVC ba shi ne zai ba su tabbacin samun damar zabe ba.

Sakon wanda bai bayyana sunan marubucin ba, ya ce “Samun katin zabe na PVC ba shi ne zai ba ka damar yin zabe ba yanzu. Idan har an mayar da sunayenku wata rumfar zabe ta daban (ko da kuwa ba ku bukaci wannan sauyin ba) bisa dalilan da muka bayyana tun farko, ba lallai ne a bari ku yi zabe a ranar zaben ba.”

Sa’annan sakon ya bukaci duk wadanda suka yi rajista su fara bin wannan adireshin dan tabbatar da wuraren da za su jefa kuri’ar su, kana kuma su raba sakon da ‘yan uwa da abokan arziki a ko’ina. 

Bisa tanadin Dokar Zabe 2022, INEC ta cigaba da cewa inda mutun ya yi rajista, a nan ne zai yi zabe ba za’a sauya ba, shi ya sa wannan sakon ke daure kai, yana kuma kara asasa rashin yardar da dama mutane ke da shi idan ya zo ga hukumar zaben, kuma zai iya hana mutane zuwa su jefa kuri’unsu.

Dan haka ne DUBAWA ta ga mahimmancin tantance wannan batun.

Tantancewa

A watan Yunin 2021, INEC ta kirkiro wasu karin rumfunan zabe guda 56,872 , abun da ya kara yawan rumfunan zaben Najeriya zuwa 176,974. Hukumar ta yi haka ne domin ta samar da isassun wuraren zabe ganin yadda adadin wadanda suka canci zabe ke cigaba da karuwa, kuma yin hakan zai rage cunkoso a wuraren sadda ake jefa kuri’a

A wata tattaunawa da shugaban sashen kula da illimantar da masu zabe da samar da bayanai ga jama’a na INEC a jihar Kwara, Adamu Musa, ya bayyana cewa mutane kalilan ne suka zabi su je su yi zabe a sabbin rumfunan da aka kirkiro.

Mr. Musa ya ce hukumar, bisa tanadin sashe na 40 (2) na Dokar Zabe 2022, ta yanke shawarar matsar da wasu daga rumfunan zaben da ke da mutane fiye da 750 zuwa runfanan da ba su kai haka yawa ba.

Ya fayyace mana cewa akan yi wa jama’a wannan sauyin ne a cikin mazabar da suka yi rajista ba wani wuri na daban ake kai su ba. Sa’annan Mr.Musa ya kuma kara ca cewa wannan ba zai hana kowa yin zabe ba kuma za’a sanar da su dangane da sauyin, idan har ya shafe su, a kan lokaci a kuma basu cikakken bayani dangane da inda aka kai su.

Haka nan kuma ya cigaba da cewa sunayen wadanda suka yi rajistan da abun ya shafa za’a lika su a kananan gundumominsu inda za su iya tantancewa kafin ranar zabe. Mr. Musan ya ce za’a yi sanarwa a kafafen yada labarai dan tabbatar da cewa sakon ya kai ga wadanda abun ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki.

Bacin haka hukumar ta tabbatar da wannan sauyin a sakon da ta rubuta a tantatcen shafinta na Twitter  inda ta tabbatarwa jama’a cewa ofisoshin jihohi za ta sanar musu da runfunan zaben da aka basu. A cikin wannan sakon ne ma ta sanar cewa akwai rumfunan zabe 240 a wasu yankunan kasar baki daya inda ba za’a yi zabe ba domin ba wanda ya yi rajista a rumfunan ko kuma ma sun bukaci sauyi sakamakon rashin tsaro. . 

DUBAWA ta kuma tantance wannan  adireshin  wanda aka sa a cikin ainihin sakon da INEC ta wallafa, inda ta ce masu yin zaben za su iya amfani da shi wajen gano rumfunan zabensu. 

A Karshe

Binciken da muka yi ya bayyana mana cewa lallai hukumar INEC ta sauya wa wasu rumfunan zabe, amma wannan matakin ba dan hana wasu zabe ba ne illa dan a tabbatar cewa sabbin rumfanan zaben da aka kirkiro ba su kasance wayam ba kowa ba sa’anan kuma a rage yawan jama’a da cunkoso ranar zabe. Matakin ba dan komai bane illa dan wadanda suka cancanci yin zabe su yi haka cikin sauki.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button