African LanguagesHausa

Bayani mai mahimmanci : Yadda ‘yan takara ke fama da muggan bayanan da ke musu lahani gabanin babban zaben Najeriya

Zabuka a Najeriya yawancin lokuta kan zo da koma baya iri-iri daga mambobin jam’iyya guda zuwa wadanda ke hamayya da su.

A wace kakar zabe, ba sabon abu ba ne aka ‘yan siyasa da magoya bayansu suna sukar abokan hamayyarsu dan su rage musu kima a idon jama’a.

Yayin da kungiyoyin da ke tantance gaskiyar bayanai irin su DUBAWA ke jagorantar yakin da ake yi da bayanan karya da na bogi, matsalar labaran gaskiyar da ake samu dangane da mutane a juya su tare da mugun nufi ta yadda za su kasance masu hadari na cigaba da kasancewa babban kalubale. 

Mene ne muggan bayanai (wato mal-information da turanci)?

Muggan bayanai, bisa kwatancen  UNESCO, bayanai ne wadanda a zahiri gaskiya ne amma kuma yawanci a kan yi amfani da su wajen janyo lahani ga mutun, kungiya ko kasa. Hukumar ta kuma kara da cewa muggan bayanai batutuwa ne da suka shafi mutun da gaske amma kuma sirrin shi ne wanda babu wanda ke da ‘yancin sani domin bai shafi jama’a ba kuma ba su da hujjar sani.

A wasu lokuta irin wadannan bayanan sun hada da jinsin da mutun ke sha’awa, kiwon lafiyar wani na kusa da shi ko kuma aikin da yake yi wanda ba shi da wata alaka da lafiya ko walwala ko ma  jin dadin al’umma amma kuma sai a yi amfani da shi yayin da ake gangamin zabe dan a bata sunayen abokan hamayya.

Gabanin zabukan Najeriyar da kowa ke jiran gani, DUBAW ta duba wasu daga cikin lokutan da aka yi amfani da muggan bayanai lokacin yakin neman zabe a kasar. 

  1. Funke Akindele

Funke Akindele ita ce ke takarar neman kujerar mataimakiyar gwamnan jihar Legas a inuwar jam’iyyar adawa ta PDP kuma tana daya daga cikin wadanda ke fama da matsalar muggan bayanai. Tun bayan da jam’iyyar ta gabatar da ita a matsayin wadda za ta yi takara da mai neman mukamin gwamna, Olajide Adediran (Jandor) ‘yar siyasar da jarumar fina-finan ke fuskantar kalubale.  Kafin sanarwar jam’iyyar dangane da takarar nata rabuwar da ta yi da mijinta Abdulrasheed Bello wanda aka fi sani da JJC Skillz, ya janyo martanoni masu zafi a kan soshiyal mediya musamman saboda da ma sananniya ce ga jama’a. JJC Skillz ne ya fara sanar da rabuwar ta su a shafinsa na Instagram, inda ya ce abubuwa sun kai inda ba za’a iya gyarawa ba a tsakininsu.

Wadansu ‘yan Najeriyar kuwa suka fara ba’a da burin siyasarta saboda rabuwar da ta yi da mijinta. Wasu ma har cewa suka yi ta mayar da hankalinta wajen gyara aurenta a maimakon shiga siyasa. 

Kwanan nan ma ba dadewa ba, lokacin wani yakin neman zaben jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Legas, mahalarta sun rika yi da ‘yan takaran PDPn inda suka ce da Jandor din da ita Funke Akindelen ba su da aure.

Sun yi ta habaici da su cikin wasu wakokin yarubanci inda su ke cewa “Funke o l’oko, Jandor o l’aya, e ba wa so fún wọn kò sáré ṣe wedding,” abun da ke nufin Jandor ba shi da aure Funke ma ba ta da aure dan haka su biyun su yi kokari su yi aure kawai.

Shin rashin auren nata zai yi tasiri kan yanyin shugabancinta? Ba zai taba yi ba.

  1. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar wanda s´kuma shi ne dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar adawa ta PDP shi ma ya fuskanci ire-iren wannan kalubalen wanda ya danganci yawan matan da ya aura.

Daga Bayanan da za’a iya samu daga shafukan intanet, a yanzu haka Atiku na da mata hudu, bayan ya rabu da biyu daga cikinsu kuma yana da yara 29. Matan na sa sun hada da Titilayo Albert, Ladi Yakubu, Princeww Rukaiyatu Mustafa, Fatima Shettima, Jennifer Douglas da wata ‘yar Morocco.

Yayin da zaben ke kusantowa, wasu ‘yan Najeriya sun shiga shafukan soshiyal mediya sun yi Allah wadai da yawan auren da ya yi inda suka zargin wai zai dauki kudaden Najeriya ne kawai ya biya bukatun ‘ya’yan shi da matan shi. Har sun ma kara da cewa wannan zai kara tsadar mulki ne kawai, wanda zai kara jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin kangin talauci kamar yadda aka gani a nan, nan, nan da nan 

  1. Peter Obi 

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Leba, Peter Obi shi ma yana fama da wannan matsakar.

Yayin da ya ke cigaba da shan suka dan barin PDPn da ya yi ya je ya tsaya takara a jam’iyyar Leba, wani mai amfani da shafukan sada zumuntan,  kwanan nan ya yi amfani da aikin da diyar Peter Obi, Gabriella Nwamaka Frances ke yi yana ba’a yana kuma yi wa dan takarar dariya dan ita malama ce a wata makarantar sakandare da ke jihar Legas.

Mr Obi, lokacin wani Taron Zauren tattaunawa (1:23:10) da daluban jihar Bayelsa, ya ce diyarsa, wadda ta yi makarantarta daga firamare har zuwa jami’a a kasar waje ta fi so ta rika koyarawa a makarantar gwamnati.

Wani mai amfani da shafin Facebook ya yi amfani da bayanin ya na wa Peter Obi dariya. Inda ya ce dan takarar ya gaza sama wa diyarsa aiki mai tsoka duk da irin  karfin fada a jin da ya ke da shi, albarkacin mukamin gwamnan da ya rike a jihar Anambra.

Inda takaddamarsa ita ce babu yadda za’a yi mutumi irin wannan ya sama wa matasa aikin yi a Najeriya idan har aka zabe shi shugaban kasa.

  1. Datti Baba-Ahmed

Datti Baba-Ahmed, shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar Leba, wanda shi ma an yi mi shi dariya saboda ‘yan uwansa. Kwanan nan Baba-Ahmed ya kusan kuka a talbijin yayin da ya ke bayanin yadda ake kunyatar da iyalansa tun bayan da ya shiga takarar mataimakin shugaban kasar a jam’iyyar Leba. 

Bisa  tarihi, mahifin Baba-Ahmed wanda ya riga mu gidan gaskiya yanzu, mai sayar da shanu ne wanda ya zo daga Mauritaniya wanda kuma aka ce kwararre ne kuma farfesa dangane da addinin musulunci.

Sai dai a waje guda, a watan Disemban 2022, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya wallafa wani bidiyo inda ya ke kiran dan takarar mukamin mataimakin shugaban kasar “Dan Mauritaniya masoyin shanz”.

father, now deceased, was an Arab cattle trader from Mauritania who was said to be a professor and expert on Islamic jurisprudence.Meanwhile, in December 2022, Nigeria’s former Aviation Minister, Femi Fani Kayode, posted a video of the vice-presidential candidate describing the latter as a “Mauritanian cow-lover”.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button