African LanguagesHausa

Da gaske ne Shugaba Joe Biden ya yi wata addu’a da harshen Arabiya?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: A wani bidiyon da ya bazu a shafin WhatsApp an yi da’awar cewa Shugaban Amurka Joe Biden  dan shekaru 82 yana karanta wata addu’a da harshen Arabiya inda yake cewa “NASARA NA GA MUSULINCI ALLAHU AKHBAR.”

Da gaske ne Shugaba Joe Biden ya yi wata addu’a da harshen Arabiya?

Hukunci: Yaudara ce! Bincike da DUBAWA ya gudaar ya gano cewa  bidiyon na karya ne an hada shi ta hanyar fasahar kwakwalwa ta AI.

Cikakken Sako

Miliyoyin al’umma suna da addini da suka yi amanna da shi, wanda suke ganin suna tasirantuwa da shi a rayuwarsu. A kwai wani bidiyo da ya rika zagayawa a shafin WhatsApp a baya-bayan nan inda aka ga Shugaban Amurka Joe Biden ana zargin yana karanta wata addu’a da harshen Arabiya a adu’ar yana cewa, “Nasara ta tabbata ga addinin Islam”

Yadda wannan bidiyo ya rika bazuwa ana yada shi a shafin na WhatApp, hakan yasa muka shiga aikin bincike don gano gaskiyar da’awar.

Tantancewa

DUBAWA ya gudanar da bincike  ta hanyar amfani da WeVerify, wata manhaja da ke iya bin kwakkwafi na bidiyo ta yi fillla-filla da bidiyon don tantance shi , inda sakamakon ya nunar da cewa bidiyon kirkirarsa aka yi, bayan gano asalin bidiyon da aka dauko aka yi masa kwaskwarima. 

A bidiyon an ga Biden sanye riga kwat iri daya da wacce yake sanye da ita a bidiyon  haka nan kuma kala daya da madaurin wuyansa, da yadda yake kallon kamera.

Tattaunawa ce da aka yi da shugaban ta bidiyo (video interview) mai taken “Shuagab Joe Biden: Tattaunawa ta tsawon mintuna 60 a 2023,” inda Shugaba Biden ya ba da amsa kan batun kokarin Isra’ila na ganin an kubutar da Amurkawa da aka yi garkuwa da su a Gaza, da halin da ake ciki a dangane da yakin Ukraine da sauransu yayin tattaunawarsa da Scott Pelley. Biden bai furta komai ba a harshen Arabic a tattaunawar da aka yi.

Haka nan DUBAWA ya kuma nazartar bidiyon inda ya kwatanta shi da wasu bidiyon kamar yadda ake gani nan,  here da here da here don tantancewa. An kuma gano banbance-bance a bidiyon lokacin da ake dubawa, misali babu hoton hakori, ba a iya ganin kwayar idanunsa , sannan yadda labbansa ke motsi sun banbanta da abin da ke fita daga bakinsa. An rika samun kiftawar idanu akai-akai, ga wani motsi na ba gaira wanda ya saba wa halayyar dan Adam, da gangan aka sanya bidiyon ya dusashe da rashin motsin jiki da  wani gashi na daban, dama rashin wasu hallayya da aka san Biden da su, kamar motsa hannu lokacin jawabi, duk irin wadannan alamu da suka saba ka’ida alamu ne da ke nuna cewa bidiyon na bogi ne (deep fake.)

A karshe mun kuma yi amfani da wasu muhimman kalmomi muka zakulo wasu kafafan yada labarai na kasa da kasa ciki kuwa har da BBC da CNN da Aljazeera sai muka ga babu wani rahoto da yace ga Biden na wata addu”a a wadannan kafofi.

A Karshe

Binciken DUBAWA ya gano cewa bidiyon tsabar karya ce an kirkire shi ne don a yaudari masu kallo.

Wannan bincike an yi shine a shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024   karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari Fellowship da hadin gwiwar Nigeria Police Radio 99.1 Fm Abuja, a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »