|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Samun karuwar rashin daidaiton siyasa a Afurka ta Yamma ya haifar da samun juyin mulki na soja a wasu kasashe na Afurka ta Yamma a shekarun baya-bayan nan. Kasashe irinsu Mali da Guinea da Burkina Faso da Niger da Guinea-Bissau sun fada karkashin mulkin soja haka kuma an samu jita-jita a wasu kasashen irin na Najeriya da Ivory Coast.
Rudanin da aka samu ya sanya labarai masu alaka da juyin mulki suka dauki hankali a 2025. Ga wasu da’awowi da aka hada labarai da su wadanda DUBAWA ta kalle su ana tsaka da wannan dambarwa.
- Bidiyon mai taimaka wa Traore na fallasa masu juyin mulki, an hada shi da kirkirarriyar basira ta AI
Wani bidiyo da ya yadu a watan Yuni,2025 wanda yayi da’awar cewa me taimaka wa shugaban ya fallasa yunkurin masu son juyin mulki inda aka nemi ba shi cin hanci €500,000 don halaka Traoré. Wannan da’awa ta ja hankali sosai inda al’umma suka rika nuna tantamarsu kan makomar masu rike da madafun iko a kasar.
Aikin gano gaskiiyar labari da DUBAWA ya gudanar ya nunar da cewa bidiyon na karya ne, saboda manhajojin gano asalin bidiyo irinsu Deepware Scanner da Attestiv sun fallasa bidiyon da cewa dabaru ne kawai aka hada inda ma cikin manhajojin suka nunar da cewa kaso 98 cikin dari ya nunar da cewa bidiyo ne da aka kirkira. Haka kuma hoto ya nunar da cewa an hada ne da fasahar ta AI, ga kuma batun ba da cin hanci wanda babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta yi wannan labari kamar yadda za a iya karantawa a nan.
- An yi amfani da wani bidiyo da aka yi shekaru 14 da suka gabata don kara bijiro da batun juyin mulki a Ivory Coast.
Wata da’awa a shafin X a ranar 22 ga watan Mayu,2025 ta sake bayyanar da juyin mulki tare da kama Alassane Ouattara a Ivory Coast, Wannan wallafa da ta dauki hankali ta nuna yadda wadanda aka dauka sojoji suka yi aikinsu inda masu amfani da shafin suka yi ta jinjinawa sojoji inda kuma suke sukar kungiyar ECOWAS da ke a yankin tareda zargin sanya bakin kasashen yamma.
Binciken DUBAWA ya gano cewa da’awar karya ce, ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi a gudanar da bincike an gano cewa babu wata kafa sahihiya da ta fitar da rahoto a cikin gida ko a waje, haka kuma babu wani labari daga bangaren gwamnatin Ivory Coast ko ECOWAS ko AU da suka fitar da wani bayani a hukumance wanda za a kafa hujja da shi.
Shima bidiyon da aka bincika an gono cewa an taba wallafa shi a watan Afrilu, 2011 inda aka nuna yadda aka kama abokin adawar Shugaba Ouattara wato Laurent Gbagbo. Sojoji da ke goyon bayan Ouattara ne suka tsare Gbagbo bayan da yaki amincewa da shan kayi a zaben da aka yi a 2010.
Kwana daya bayan jita-jitar ta yadu Ouattara an tabbatar ya ci gaba da gudanar da ayyukansa inda ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na mako-mako. Wannan da’awa an bayyanata da zama da’awa ta kirkira da aka yi daga wata kasa ta waje da ma yada labaran da ba haka suke ba, wanda ake ganin an kikrkira ne daga wata kasa makociyar Ivory Coast da nufin haifar da rudani a kasar.
- Shugaban riko zai jagoranci Guinea-Bissau tsawon shekaru uku bayan juyin mulki
Wani shafin TikTok mai suna “BISSAU ELITE TV” ya shirya karya inda yace dakarun tsaro sun sanya shugaban kasa na riko da zai jagoranci kasar a tsawon shekaru uku, wannan wallafa ta ja hankali sosai ana tsaka da zaman rashin tabbas na makomar siyasa a wannan kasa.
Sai dai bincike ya tabbar cewa bayanin ko labarin karya ne kasancewar kafar yada labaran kasar ta (TGB) ta fitar da bikin rantsar da sabon shugaban kasar Janar Horta Inta-A a ranar 27 ga Nuwamba,2025.
Rahotanni na hukuma sun tabbatar da cewa Janar Inta-A wanda sojojin suka tsara an rantsar da shi a matsayin shugaban riko na tsawon shekara daya abin da ya ci karo da da’awar shekaru uku da bidiyon ya yada.
- An yi amfani da bidiyon Kamaru na 2014 aka bayyana zanga-zanga da ta tashi a Burkina Faso a 2025
Bayan da mahukuntan Burkina Faso suka alakanta shirin juyin mulki da bai nasara ba da Côte d’Ivoire a watan Afrilu,2025 an ga wani bidiyo a shafin Facebook inda aka ga zanga-zangar nuna goyon baya ga Ibrahim Traoré
Wannan wallafa da aka yada ta shafin wani mai yawan mabiya, ya nunar da cewa zanga-zangar ta faru ne a birnin Ouagadougou a ranar 20 ga Afrilu,2025 kwanaki kadan bayan juyin mulkin da ya gaza nasara.
Tantancewa ta tabbatar wannan da’awa karya ce duba da hotunan, da ma abin da aka rubuta akwai kura-kurai , haka bidiyon ma tsoho ne, kuma an dauki hoton ne a birnin Yaoundé na Kamaru inda aka ga motocin haya na tasi da launin dorawa sabanin na Ouagadougou wadanda launinsu kore ne.
Hanyar tantance asalin bidiyo ma ta nunar da cewa an wallafa wannan bidiyo a shekarar 2014 a shafin Facebook a lokacin jana’izar Charles Ateba Eyene wani fitaccen dan siyasa a kasar ta Kamaru, wani dan jarida ma a kasar ta Kamaru ya tabbatar da cewa babu wani gangami da aka yi da ya tattara jama’a a wannan rana ta 20 ga watan Afrilu,2025.
