Tutar Isra'ila. Asalin hoton: Facebook.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi zargi cewa mambobin majalisar dokokin Isra’ila 70 daga cikin 120 sun nuna goyon bayansu ga kafa kasar Biafra sun kuma nuna bukatar ganin an saki Nnamdi Kanu.

Hukunci: Karya ce. Babu wata sheda da ta nuna cewa ‘yanmajalisar na Isra’ila sun nuna goyon bayansu ga kafa kasar Biafra ko kuma sun nemi a saki Nnamdi Kanu.
A bincike kan rahotanni daga kafafan yada labarai na Isra’ila da Najeriya dama bayanan da aka tattaro daga majalisar ta Knesset babu inda aka ga wannan muhawara ko daukar matakin.
Cikakken Sako
Shafukan sada zumunta sun kasance dandali na kungiyoyi da masu fafutuka wadanda suke amfani da su don yada manufofinsu da ajandarsu, don sauya tunanin al’umma.
Sau tari irin wannan suna yaduwa ba tare da tantancewa ba, da yada labaran da ba haka suke ba.
Kungiyar da ke fafutukar ganin ta kafa kasar Biafra tana nan a shafukan sada zumunta, suna yada labarai mabanbanta don cimma muradunsu.
Sai dai DUBAWA a lokuta da dama ta bankado da’awa da dama masu alaka da wannan kamar a wadannan wurare nan da nan da nan.
Mai amfani da shafin na Facebook ya bayyana a wani bidiyon (kamar yadda aka ajiye a nan) cewa mambobi 70 daga cikin 120 na majalisar dokokin Isra’ila sun bayyana goyon bayansu ga fafutukar kafa kasar Biafra da neman sakin Nnamdi Kanu.
Mai da’awar a bidiyon mai tsawon dakika 30, yace “Ya ku mutanena a farkon makon da ya gabata na fada maku cewa majalisar dokokin Isra’ila za ta yi zama kan batun kasar Biafra. An samu rahoto cewa sama da mambobin majalisa 70 daga cikin 120 sun goyi bayan kafa kasar Biafra, nan ba da dadewa ba za su fitar da labari da zai iya bayuwa ga samun kasar Biafra mai cin gashin kanta.”
Ya zuwa ranar 12 ga watan Maris, 2026, wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu 507 da masu tsokaci 36 da wadanda suka yada 91 da mutane sama da 2,000 da suka kalla.
Mun duba sashin na tsokaci don ganin me masu tsokacin ke cewa kan wannan da’awa.
@Okechukwu Chima ya rubuta cewa “Tabbas, sai kasar Biafra. Najeriya ki saki Mazi Nnamdi Kanu da Biafra yanzu.
@Ifeco Ezegbu yayi martani da cewa, “Muna taya murna, kasar Biafra har abada babu sauran wani abu. Muna godiya.”
Dukkanin wadanda suke tsokaci sun nuna cewa sun aminta da wannan da’awa sai dai @Akile Bende, wanda yace, “Karya da Karya da Karya.”
Irin wannan da’awa an yada ta a wasu shafukan na Facebook kamar a wadannan wurare nan da nan da nan.
Wannan da’awa akwai alamun tambaya a kanta duba da cewa abu ne mai wahala a ce wata kasar waje ta shiga al’amuran cikin gida na siyasar Najeriya. Don haka DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan da’awar.
Tantancewa
Ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi daga cikin da’awar, mun duba ko akwai wasu rahotanni daga wasu kafafan yada labarai irinsu The Times of Israel da The Jerusalem Post, wurin da duk wani abu da ya shafi majalisar dokokin Isra’ila ake maganarsa amma babu wani labari daga majalisar inda ta yi wani rahoto akan hakan.
DUBAWA ta tabbatar da cewa majalisar ta Knesset tana da ma mambobi 120 adadin da yayi daidai da na mai da’awar, duk da haka babu inda muka samu labari da ya nuna cewa majalisa ta yi wani zama ta kuma dauki wani mataki kan abin da ya shafi kasar Biafra.
Mun yi yunkuri na nazartar kalanda ta Knesset da ke nuna ajandar majalisar ta kasa ko ta bayyana wani abu mai kama da Biafra sai dai wannan shafi baya aiki.
Haka nan ta hanyar amfani da shafin YouTube na majalisar shima nan babu sakamakon da ya nuna ko wata tattaunawa kan wannan labari da ake zargi.
Wannan tasha na dauke ne kawai da wasu kananan bidiyo kan abin da ya shafin siyasa da tattalin arziki da tsaro da ci gaba da lafiya a Isra’ila.
A karshe mun duba kafofin yada labarai na Najeriya babu wani rahoto. anan ma babu wata kafar yada labarai da ta yi rahoto kan cewa majalisar dokokin Isra’ila ta yi zaman tattaunawa kan batun ‘yantar da kasar Biafra ko kuma ta yi labarin fafutukar kasar ta ganin a saki Nnamdi Kanu.
Karshe
Babu wata sheda da ta tabbatar da ganin cewa Isra’ila ta shiga harkokin siyasar Najeriya ko ta dauki wani mataki da zai karfafi “fafutukar ‘yantar da Biafra.” Duk da cewa Isra’ila na da mambobi 120 babu inda muka samu sheda cewa ‘yanmajalisa 70 sun goyi bayan kafa kasar Biafra ko sun nemi a saki Nnamdi Kanu, don haka wannan da’awa karya ce.
