Kim Jong-un, Shugaban Koriya ta Arewa da Bola Tinubu, Shugaban kasar Najeriya.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X na da’awar gwamnatin Najeriya ta karbi fam(£) biliyan 50 a matsayin bashi daga Koriya ta Arewa.

Hukunci: Babu isassashen hujja! Babu wani bayani a hukumance da ke nuna cewa Koriya ta Arewa ta baiwa Najeriya bashin Pam biliyan 50. Bacin haka, Koriya ta Arewa ba ta da hurumi ko ma ikon yin hakan.
Cikakken Bayani
Baya ga cibiyoyin kasa da kasar da ke bin Najeriya bashi, wani mai amfani da shafin X @I_am_Tkgold na da’awar cewa gwamnatin Najeriya ta karbi bashin Fam biliyan 50 daga gwamnatin Koriya ta Arewa.
Da’awar (wanda za’a iya gani a nan) ya fara daukar hankali sosai yanzu domin masu amfani da shafin X na tambayar wanda ya wallafa labarin ya gawo hujjoji masu kwari.
Alal misali , Olalekan Oyedeji tambaya ya yi kamar haka, “wannan dai da walakin goro a miya. Koriya ta Arewa ta baiwa Najeriya bashi har na fam biliyan 50? Muna da majiyoyi masu kwari da za su iya tabbatar da wannan bayanin ko kuma wani bayani a hukumance? Bayanan da ba daidai ba kan yadu cikin gaggawa; mu tantance tukuna.”
Baya ga Olalekan, akwai wasu su ma wadanda suka hada da @favor_million da @Freelancer_Ib, su ma sun kira bayanin “labarin da ba daidai ba.”
Sai dai, @I_am_Tkgold ya hakikance kan cewa ya sami bayaninsa daga maiya mai nagarta, amma kuma ya ki ya bayyana suna.
Hade da tsokacin da aka yi a karkashin labarin, daga ranar 11 ga watan Maris, 2026, mutane 557 sun nuna alamar like yayin da wasu 216 suka sake raba labarin. Haka na kuma ya bayyana a wadannan shafukan na Facebook, wato nan da nan.
DUBAWA ta yanke hukuncin tantance wannan bayanin ne saboda mahimmancin da ya ke da shi kan tattalin arziki da ma yadda ya riga ya fara yaduwa.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da gudanar da bincike inda muka gano wani jaddawalin da ke dauke da sunayen duk wuraren da Najeriya ta taba karbo bashi kuma babu inda aka ce ta karba a wurin Koriya ta Arewa.
Daga nan mun tuntubi Wale Edun, ministan Kudi, da Taiwo Oyedele, sabon karamin ministan kudin da aka sa yanzu, ta wayar tarho da WhatsApp. Sai dai tsakanin ministocin biyu babu wanda ya amsa tambayar mu.
Mun kuma tattauna da Kimiebi Ebienfa, Mai magana da yawun ma’akaitar kula da harkokin wajen Najeriya. Ya ce shi ba shi da wani bayani dangane da wannan batun, ya kuma shawarce mu da mu koma ma’aikatar kudin kasar inda ya ce za mu fi samun karin bayani.
Dan haka bayan nan sai muka gudanar da bincike kan yadda Koriya ta Arewa ke kashe kudadenta musamman wajen tallafawa kasashe ko bayar da bashi. A nan ne muka gano cewa Koriya ta Arewa ba ta taba baiwa kowa kudin da ke da wannan darajar ba. Daga shekarar 2024 ana Kiyasin cewa baki daya jimilar kudin da ta samu shi ne biliyan 32 na dalar Amurka wato pam biliyan 23. Dan haka idan har aka bi na mai da’awar ana iya cewa kudin da ya ke da’awar Najeriya ta karba bashi ya ninka abinda akae kiyasin ta na samu kowace shekara har sau biyu.
Ko da ma ya kasance Koriya ta Arewr ta na da wannan kudin, ba ta da goyon bayan doka ta bai wa Najeriya ko ma kowace kasa bashi bisa tanadin Majalisar Dinkin Duniya. Koriya ta Arewa na rayuwa ne kan akidarta ta dogaro da kai dan haka ita saniyar ware ce a fannin tattalin arziki. To amma mafi mahimmanci, al’ummar kasa da kasa ta sanya ma ta takunkumi na bai daya wadanda wasun su su ne takunkumin da suka fi tsauri a duniya a fannin “doka da tattalin arziki” wadanda kuma suka katse kasar daga harkokin kudi a matakin kasa da kasa da tsare-tsaren kasuwanci.
A yanzu haka, kasar da ita kadai ce ke da irin wannan kusancin da ita ta yadda har bashi zai iya shiga tsakaninsu ita ce China.
Haka nan kuma, an katse Koriya ta Arewa daga tsarin biyan kudade na “SWIFT” wanda ake amfani da shi tsakanin kasashe a matakin kasa da kasa. Wannan na nufin ba ma za ta iya turawa Najeriya kudi ba.
Baya ga wadannan abubuwan. Najeriya ba za ta iya aro kudi daga Koriya ta Arewa ba domin yin hakan zai sabawa tanadin Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya. Idan har haka ya faru Najeriya na iya fiskantar takunkumi daga Majalisar Dinkin DUniya, Amurka, da Turai wanda zai yi tasiri mai muni a kan tattalin arzikin Najeriya.
A Karshe
Babu wata hujjar da ta goyi bayan wannan da’awar ta cewa Najeriya ta sami fam biliyan 50 bashi daga Koriya ta Arewa. Bacin haka kasar ba ta da irin wannan kudin bare har ta baiwa wata kasa. Ko da ma tana da kudin Majalisar Dinkin Duniya ta hana ta baiwa duk wata kasar da ke zaman mamba a majalisar.
